Muhawara Hausa
 



MUSABAKAR HADDAR ALQUR'ANI KO HADITHI KO WANI NAU'IN ILMI A MAHANGAR M
 
Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc MUSABAKAR HADDAR ALQUR'ANI KO HADITHI KO WANI NAU'IN ILMI A MAHANGAR MUSULUNCI

Da yawa daga cikin wadanda suka zaba wa kansu sabanin shiriyar Manzon Allah cikin gudanar da addininsu suna ganin cewa: In har Idin Maulidi bidi'ah ne, to kuwa lalle Musabaka a kan haddar Alqur'ani Mai girma, ko haddar Hadithan Annabi masu daraja ko haddar wani ilmi na Musulunci su ma yin su bidi'ah ce!!!

A nan muna ganin cewa yawan nisantar wadannan mutane ga littattafan Shari'ah na maluman Musulunci ne ya sa ba su ma san cewa: Dukkan abin da halaccinsa ya tabbata ta yanyar Ijma'in Musulmi cikin wani zamani daga cikin zamuna, to dole ne ya zamanto daya daga cikin abubuwa uku:-

1- ko dai ya zamanto Mubaahi, watau abin da yin sa da rashin yin sa duk daya a idanun Shari'ah.

2- ko kuwa ya zamanto Mustahabbi, watau abin da in har ba a yi shi ba to ba a yi wani laifi ba, in kuma aka yi shi to ana da wani lada na musamman.

3- ko kuwa ya zamanto Waajibi, watau abin da in har ba a yi shi ba za a sami zunubi, in kuma an yi shi to an yi abin da Shari'ah ta tilasta yin shi.

shi kuwa Musabaka domin haddar Alqur'ani Mai girma abu ne da Maluman Sunnah, da su kansu masu bidi'ah na Duniya suka hadu a kan halaccinsa a bisa hujjar kiyasin shi a kan Musaabakokin da Nassi ya zo da halaccinsu.

In kuwa haka lamarin yake, to ta kaka ne za a hada hukuncin Musaabaka domin haddar Alqur'ani da hukuncin Idin Maulidin da babu mai yin shi ko halatta shi in banda wasu daga cikin masu yin bidi'ah??

HUKUNCIN MUSABAKA:

1. Imam Ibnu Qudaamah mai rasuwa a shekara ta 620 watau da mutuwarsa yau shekaru 815 ke nan, ya ce cikin littafinsa mai suna Almugnii 13/404-405 :-

{ ﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﺟﺎﺋﺰﺓ ﺑﺎﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻻﺟﻤﺎﻉ، ﺍﻣﺎ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﺮﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺳﺎﺑﻖ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺨﻴﻞ ﺍﻟﻤﻀﻤﺮﺓ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﻔﻴﺎﺀ ﺍﻟﻰ ﺛﻨﻴﺔ ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ، ﻭﺑﻴﻦ ﺍﻟﺘﻲ ﻟﻢ ﺗﻀﻤﺮ ﻣﻦ ﺛﻨﻴﺔ ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ ﺍﻟﻰ ﻣﺴﺠﺪ ﺑﻨﻲ ﺯﺭﻳﻖ. ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ.... ﻭﺍﺟﻤﻊ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺟﻮﺍﺯ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺠﻤﻠﺔ. ﻭﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺿﺮﺑﻴﻦ: ﻣﺴﺎﺑﻘﺔ ﺑﻐﻴﺮ ﻋﻮﺽ، ﻭﻣﺴﺎﺑﻘﺔ ﺑﻌﻮﺽ. ﻓﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﺑﻐﻴﺮ ﻋﻮﺽ ﻓﺘﺠﻮﺯ ﻣﻄﻠﻘﺎ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺗﻘﻴﻴﺪ ﺑﺸﻲﺀ ﻣﻌﻴﻦ، ﻛﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﻗﺪﺍﻡ، ﻭﺍﻟﺴﻔﻦ، ﻭﺍﻟﻄﻴﻮﺭ، ﻭﺍﻟﺒﻐﺎﻝ، ﻭﺍﻟﺤﻤﺮ، ﻭﺍﻟﻤﺰﺍﺭﻳﻖ، ﻭﺍﻟﻤﺼﺎﺭﻋﺔ، ﻭﺭﻓﻊ ﺍﻟﺤﺠﺮ ﻟﻴﻌﺮﻑ ﺍﻻﺷﺪ، ﻭﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ؛ ﻻﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﺳﻔﺮ ﻣﻊ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻓﺴﺎﺑﻘﺘﻪ ﻋﻠﻰ ﺭﺟﻠﻬﺎ، ﻓﺴﺒﻘﺘﻪ، ﻗﺎﻟﺖ: ﻓﻠﻤﺎ ﺣﻤﻠﺖ ﺍﻟﻠﺤﻢ ﺳﺎﺑﻘﺘﻪ ﻓﺴﺒﻘﻨﻲ، ﻓﻘﺎﻝ: ﻫﺬﻩ ﺑﺘﻠﻚ. ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻮﺩﺍﻭﺩ .

ﻭﺳﺎﺑﻖ ﺳﻠﻤﺔ ﺑﻦ ﺍﻻﻛﻮﻉ ﺭﺟﻼ ﻣﻦ ﺍﻻﻧﺼﺎﺭ ﺑﻴﻦ ﻳﺪﻱ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﺫﻱ ﻗﺮﺩ. ﻭﺻﺎﺭﻉ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺭﻛﺎﻧﺔ ﻓﺼﺮﻋﻪ. ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ. ﻭﻣﺮ ﺑﻘﻮﻡ ﻳﺮﺑﻌﻮﻥ ﺣﺠﺮﺍ ﻳﻌﻨﻲ ﻳﺮﻓﻌﻮﻧﻪ ﻟﻴﻌﺮﻓﻮﺍ ﺍﻻﺷﺪ ﻣﻨﻬﻢ ﻓﻠﻢ ﻳﻨﻜﺮ ﻋﻠﻴﻬﻢ .

ﻭﺳﺎﺋﺮ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺎﺕ ﻳﻘﺎﺱ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﺍ.{ ﺍﻧﺘﻬﻰ .


Ma'ana: ((Musabaka halal ce cikin sunnar Manzon Allah, da Ijma'in Maluma. A cikin Sunnah dai Ibnu Umar ya ruwaito cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya shirya Musabaka tsakanin dawakin da aka yi musu ''Tadhmiir'' (watau wadanda aka yi musu horon tinkarar yaki ta hanyar karanta abinci gare su da sanya musu tufafinsu da sauransu) a filin da ya taso daga Haifaa har zuwa Thaniyyatul Wadaa, haka nan ya shirya wata Musabakar tsakanin dawakin da ba a yi musu Tadhmiiri ba, a filin da ya taso daga Thaniyyatul Wadaa har zuwa Masjidu Bani Zuraiq. Buhari da Muslim ne suka ruwaito hadithin....Sannan Musulmi sun yi Ijma'i a kan halaccin Musabaka a dunkule.

Sannan ita Musabaka ta kasu ne zuwa kashi biyu:

Musabaka da ake yi tare da sanya wasu kudi cikinta (ga duk wanda ya yi nasara). Akwai kuma Musabaka da ake yi ba tare da an sanya kudi cikinta (ga duk wanda ya yi nasara ba). To ita Musabaka da ake yi ba tare da an sanya wasu kudi cikinta ba wannan ta halatta ba tare da sanya mata wani tarnaki a cikinta ba, kamar dai Musabakar da ake yi na tseren gudu da kafa, ko Musabakar tseren jiragen ruwa, ko Musabakar tsere tsakanin tsutsaye, ko Musabakar tsere tsakanin alfadaru, ko Musabakar tsere tsakanin jakuna, ko Musabakar tsere tsakanin giwaye, ko Musabakar yin harbi da kananan masu, ko Musabakar yin kokowa, ko Musabakar daga dutse mai nauyi sanoda gwada karfi, da dai nau'o'in Musabaka dabam daban.

Saboda Annbi mai tsira da amincin Allah wata rana a hanyar tafiye-tafiyensa ya yi Musabakar tseren gudu da kafa tsakaninsa da matarsa Nana A'isha Allah Ya kara mata yarda, kuma ta yi nasara a kansa. Sai A'isha ta ce: da na yi kiba sai wata rana muka sake yin Musabakar tseren gudu da kafa sai ya yi nasara a kaina. Sai ya ce da ni: ni ma na rama wancan ci da kika yi mini.

Wannan hadithi Abu Dawuda ne ya ruwaito shi.

Kuma Salamah Dan Ak'wa ya yi Musabakar tsere da kafa tsakaninsa da wani mutum a gaban Annabi mai tsira da amincin Allah a ranar Ruwan Zuu Qarad.

Sannan Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi Musabakar kokowa tsakaninsa da wani gwanin kokowa mai suna Rukaanah, kuma ya yi nasara a kansa ya kada shi. Tirmizii ne ya ruwaito hafithin. Sannan wata rana Annabi mai tsira da amincin Allah ya wuce wasu mutane suna Musabakar daga dutse mai nauyi saboda sanin wane ne ya fi karfi, amma bai hana su yin hakan ba.

Sauran Musabakpkin sai a kiyasta su a kan wadannan)) [da nassi ya tabbatar]. Intaha.

2. Imamu Ibnu Qayyimil Jauziyyah wanda ya mutu a shekarar Hijira ta 751 watau yau shekaru 684 ke nan da suka wuce ya ce cikin littafinsa mai suna Alfuruusiyyah 1/318:-

{ ﺍﻟﻤﺴﺎﻟﺔ ﺍﻟﺤﺎﺩﻳﺔ ﻋﺸﺮﺓ:

ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺣﻔﻆ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ، ﻭﺍﻟﺤﺪﻳﺚ، ﻭﺍﻟﻔﻘﻪ، ﻭﻏﻴﺮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﻠﻮﻡ ﺍﻟﻨﺎﻓﻌﺔ، ﻭﺍﻻﺻﺎﺑﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺎﺋﻞ، ﻫﻞ ﺗﺠﻮﺯ ﺑﻌﻮﺽ؟ ﻣﻨﻌﻪ ﺍﺻﺤﺎﺏ ﻣﺎﻟﻚ، ﻭﺍﺣﻤﺪ، ﻭﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ. ﻭﺟﻮﺯﻩ ﺍﺻﺤﺎﺏ ﺍﺑﻲ ﺣﻨﻴﻔﺔ، ﻭﺷﻴﺨﻨﺎ، ﻭﺣﻜﺎﻩ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺒﺮ ﻋﻦ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ. ﻭﻫﻮ ﺍﻭﻟﻰ ﻣﻦ ﺍﻟﺸﺒﺎﻙ، ﻭﺍﻟﺼﺮﺍﻉ، ﻭﺍﻟﺴﺒﺎﺣﺔ، ﻓﻤﻦ ﺟﻮﺯ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺑﻌﻮﺽ، ﻓﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﺎﻟﺠﻮﺍﺯ، ﻭﻫﻲ ﺻﻮﺭﺓ ﻣﺮﺍﻫﻨﺔ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ ﻟﻜﻔﺎﺭ ﻗﺮﻳﺶ ﻋﻠﻰ ﺻﺤﺔ ﻣﺎ ﺍﺧﺒﺮﻫﻢ ﺑﻪ، ﻭﺛﺒﻮﺗﻪ. ﻭﻗﺪ ﺗﻘﺪﻡ ﺍﻧﻪ ﻟﻢ ﻳﻘﻢ ﺩﻟﻴﻞ ﺷﺮﻋﻲ ﻋﻠﻰ ﻧﺴﺨﻪ .

ﻭﺍﻥ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ ﺍﺧﺬ ﺭﻫﻨﻬﻢ ﺑﻌﺪ ﺗﺤﺮﻳﻢ ﺍﻟﻘﻤﺎﺭ. ﻭﺍﻥ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻗﻴﺎﻣﻪ ﺑﺎﻟﺤﺠﺔ، ﻭﺍﻟﺠﻬﺎﺩ، ﻓﺎﺫﺍ ﺟﺎﺯﺕ ﺍﻟﻤﺮﺍﻫﻨﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﺕ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ، ﻓﻬﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﺎﻟﺠﻮﺍﺯ.

ﻭﻫﺬﺍ ﺍﻟﻘﻮﻝ ﻫﻮ ﺍﻟﺮﺍﺟﺢ.{ ﺍﻧﺘﻬﻰ .


Ma'ana: ((Mas'alah ta goma sha daya: Yin Musabakar haddace Alkur'ani, da Hadithi, da Fiqhu, da wasu Ilmummuka masu amfani, ko gane abin da yake daidai cikin wasu mas'alolin, shirya irin wannan Musabaka a bisa wani kudi, shin hakan zai halatta ko kuwa ba zai halatta ba? Mutanen Malik, da Ahmad, da Sha'fi'ii sun hana yin sa. Amma mutanen Abu Hanifah da Malaminmu (Ibnu Taimiyah) da ma hikayar Ibnu Abdil Barr daga Sha'fi'ii sun halatta yinsa.

Shi wannan nau'i na Musabaka ya fi yin Musabaka a kan harkar iya sa tarko, ko kokowa, ko ninkaya, sanoda haka wadanda suka halatta shirya Musabaka a bisa kudi cikin wadannan, lalle shirya Musabaka cikin harkokin habaka ilmi shi zai fi cancantar halatta, kuma wannan ita ce surar Muraahanar da Sbubakar Siddiq ya yi da kafuran Quraishawa a kan gaskiyar labarin da ya ba su (na cewa Ruumaawa za su yi nasara a kan Faatisaawa bayan shekaru kadan).

Dalili ya gabata na cewa babu abin da ya shafe ingancin wannan Muraahanar. Kuma shi Abubakar ya yi Muraahanar da su ne bayan haramta yin caca.

Sannan ita tsayuwar Addini da ma tana samuwa ne ta hanyar kafa hujja, da yin jihadi, saboda wannan idan har Muraahanah za ta halatta a kan abubuwan karfafa jihadi, ke nan ta halatta a kan abubuwan karfafa ilmi da za su karfafa kafa hujja shi ne zai fi cancanta, kuma wannan magana ita ce abin rinjayarwa)).

Intaha.

Lalle da wadannan bayanai ne mahankalta za su fahimci cewa ita Musabakar haddar Alkur'ani mai girma, ko musabakar haddar Hadithan Manzon Allah Masu daraja, ko musabakar haddar wani ilmi mai amfani -tare da sanya wani kudi ga wanda ya yi nasara ko kuwa ba tare da sanya wani kudi ga wanda ya yi nasara ba- abu ne da yake halal ta hanyar hujjoji biyu:-

1. Ijma'i.

2. Qiyaasi.

Wannan kuwa duka sabanin maida ranar haihuwar Annabi mai tsira da amincin Allah wani Idi ne, wanda babu Ijma'i a kansa, babu kuma wani Qiyaasi sahihi a kansa.

Muna rokon Allah Ya taimake mu Ya tabbatar da dugaduganmu a kan Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah. Ameen.

 Posted By Aka Sanya A Wednesday, October 04 @ 08:42:11 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc:
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc



"MUSABAKAR HADDAR ALQUR'ANI KO HADITHI KO WANI NAU'IN ILMI A MAHANGAR M" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com