Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

 

 
Hukuncin wanda kabbara daga cikin kabbarorin sallan gawa ko sallar idi suka wuce
 
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen Hukuncin wanda kabbara daga cikin kabbarorin sallan gawa ko sallar idi suka wuceshi

Mutum ne yazo sallan gawa sai ya tarar da liman ya riga yayi kabbara biyu ko fiye da haka meye hukuncinsa? zai yi kabbara ya fara daga karatun fatiha ne ko kuma zai fara daga inda limamin yake ne sannan daga karshe ya rama kabbarorin ko kuma bazai rama su ba?

Amsa:

idan mutum wasu kabbarori suka wuceshi daga cikin kabbarorin sallan gawa toh in yazo zaiyi kabbara ne sannan ya fara karanta fatiha, zaiyi lura da cewa wannan kabbarar itace farkon kabbararsa, sannan in limami ya kammala sallan shikuma zai tsaya ya kammala kabbarorin da suka wuceshi da sauri, in har ba'a dauke gawar ba, amma in aka dauke gawar to kawai zaiyi kabbarorin da suka wuce masa ne ajere ba tare da bata lokaci ba ko yin addu'oi bayansu, dalilin da yasa malamai sukace wanda wasu kabbarori suka wuceshi na sallan gawa zai cikesu shine umumin fadin manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam),

''IDAN AKA TAYAR DA SALLAH KU TAFI ZUWA GARETA KUNA MASU NATSUWA, ABIN DA KUKA SAMU KU SALLATA, ABINDA YA KUBCE MUKU KUMA KU RAMA'' wannan hadisi bai bambance tsakanin salloli ba, kuma shima sallan gawa sallah ne kaman ko wani sallah,

haka ibn Baaz ya bada fatwa. majmu'ul fatawa 13/149.

an tambayi maluman lajnatudda'imah, Meye hukuncin wanda ya riski kabbara daya da liman a sallan gawa, kabbarori uku suka wuceshi?

sai suka amsa da cewa ''Zai cike sallan gawarsa sai yayi kabbarori ukun da ya kubce masa kafin a dauke gawar, sannan zaiyi lura da kabbarar farko da ya samu da liman shine farkon sallan sa.

Wanda kuma kabbarorin sallan idi suka wuceshi wasu malamai suna ga zai ramasu da zarar ya shiga sallah bayan kabbarar harama sai yayi su baki daya, wannan itace mazhabar malikiyyah da shafi'iyyah ta daa.... kuma ita tafi kusa da daidai,

wasu kuma suna ga basai ya rama ba sabida sunnace wanda muhallinta ya riga ya wuce, Allahu A'alam.

TANA YIWUWA DAN ADAM YA YI MAGANA DA ALJANI TA HARSHEN MARA LAFIYA

Ingantattun hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah', kamar hadithin Murrah wanda Ahmad da Haakim suka ruwaito, da hadithin Uthman Bin Abil Ass. Da kuma maganganun Malamai, kamar maganar Imam Ahmad Bin Hanbal, da Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah, da Imam Ibnul Qayyim dukkansu suna nuna yiwuwar maganar mutum da aljani ta harshen mara lafiya.

Babban Malami Sheikh Abdul Aziz Bin Baz shugaban majalisar Malamai ta kasar Saudiyya a lokacin da yake raye ya ce cikin lattafinsa mai suna Iidhaahul Haqqi Fii Dkhuulil Jinniyyi Fil Insiyyi shafi na 6-7 ((Aljani ya cakuda da sashin Mata Musulmai a Riyadh, sai sashin Malamai ya karanta (Alkur'ani) domin fidda shi, ya kuma tunatar da Aljanin (girman) Allah, ya yi masa wa'azi, ya kuma ba shi labarin cewa zalunci haramun ne, kuma zunubi ne babba, ya kuma kira shi zuwa ga Musulunci ya musulunta. Daga nan sai suka zo gurina da matar, na tambaye shi (shi Aljanin) dalilin da ya sa ya shiga cikinta, ya ba ni labarin dalilan, ya yi magana da harshen matar amma maganar maganar na miji ne ba maganar mace ba. (Hakan ya faru ne) alhalin tana cikin wata kujera da ke kusa da ni, dan'uwanta, da 'yar'uwarta, da wasu sashin Malamai suna shaidar hakan, suna jin maganar Aljanin a lokacin da yake tabbatar da musuluncinsa a fili, na yi masa nasiha, na yi masa wasiyyar takawar Allah, da kuma cewa ya fita daga wannan matar, ya nisanci zaluntarta, ya kuma karba mini hakan ya ce: Ni na gamsu da Musulunci. Na yi masa wasiyyar ya kira jama'arsa zuwa ga Musulunci. Ya bar matar da aka ambata, karshen kalmar da ya hurta ita ce: Assalaamu Alaikum, daga nan sai matar ta yi magana da irin harshenta da aka saba (ji), ta kuma ji lafiyar jikinta da samun hutu daga gajiyar da ya sanya mata. Daga nan sai ta sake dawowa gurina bayan wata ta kuma ba ni labarin cewa tana cikin alheri da lafiya)).

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya taimake mu. Ameen.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Wednesday, October 04 @ 09:46:40 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Mataki Na Rating

Average Score: 5
Kurioi: 1


Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

"Hukuncin wanda kabbara daga cikin kabbarorin sallan gawa ko sallar idi suka wuce" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: