Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar
[ Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar ]

·Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
·Asalin Hausa (3)
·Asalin Hausa (2)
·Asalin Hausa (1)
·Yadda Musulmi Zaiyi Ta'amuli A Bukin Kiresriti
·08 SHIN KASANCEWA SAYYIDUNA MU'AWUYA DAN ALJANNA NE ????
·002 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 2
·001 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 1
·GASKIYA KENAN! YAU 'YAN IZALA NE AKE RIGIMA DASU WAJE KARE MARTABAR MANZON

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


002 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 2
 
 
Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar 002 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 2

*Yadda Ake Yin Bikin Aure*

Bikin aure wanda ya ƙunshi yayata shi da bayyana shi abin so ne, in ji malamai saboda dalilai masu yawa kamar haka:

Maganar Annabi (Sallal Laahu 'Alaihi wa Aalihi wa Sallam) cewa: Bambancin da ke tsakanin halal da haram shi ne, buga dundufa da jin muryar (waƙa a wurin aure). ²

Kuma a lokacin da su A'ishah r.a suka kai wata amarya gidan mijinta sai Annabi (Sallal Laahu 'Alaihi wa Aalihi wa Sallam) ya ce: A'ishah! Ba ku da wadda za ta yi ɗan waƙa ne, domin su Lansarawa mutane ne da suke sha'awar wasa. ³

Wannan ya nuna abubuwa kamar haka:
° Ya halatta waɗansu mata masu mutunci su raka amarya zuwa gidan mijinta a ranar tarewarta. ⁴

° Kuma in aka samu wata mai rera waƙar aure irin na al'ada a cikinsu duk ya yi daidai.

° Daidai ne kuma matan da suka kai amaryar su zauna a gidan amaryar kuma su saurari irin wannan waƙar.

Sannan kuma ga Aamir Bn Sa'ad ya shiga wurin Ƙarazah Bn Ka'ab da Abu Mas'uud Al-Ansaariy a lokacin wani angwanci, sai kuma ya ga waɗansu kuyangi suna waƙa. Don haka sai ya ce: Haba! Ga ku fa sahabban Manzon Allaah (Sallal Laahu 'Alaihi wa Aalihi wa Sallam) kuma mutanen Badar ne, amma kuka bari ana yin wannan a gabanku?! Sai suka ce: Ka zauna ka ji tare da mu in kana buƙata, domin an yi mana sassauci ga sauraron waƙe irin wannan a lokacin bikin angwanci. 5

• Kuma a lokacin da aka yi wa Ar-Rubayyi'u bint Mu'awwiz aure kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu 'Alaihi wa Aallihi wa Sallam) ya tafi domin gaishe ta, sai waɗansu kuyangi suka fara buga dundufa suna waƙen yabon iyayenta da suka yi shahada a yaƙin Badar. Ana cikin haka ne sai wata daga cikinsu ta ce: Kuma a cikinmu akwai Annabi yana sanin gobe!


A nan ne sai Manzon Allaah (Sallal Laahu 'Alaihi wa Aalihi wa Sallam) ya ce: Rabu da wannan, ke dai ki cigaba da faɗin abin da kike faɗi a da!6

Wannan ya nuna har manya ma sun tafi gidan amarya kuma sun zauna sun taya ta murna, har kuma ma sun saurari kiɗa da waƙar aure a lokacin.
Amma yaya ake yin wannan kiɗan da waƙar?
Malamai sun ce ana yin wannan abin ne kamar yadda Hadisan suka nuna:

• Ayi amfani da gangar da ake kira dundufa kawai ban da wadda ba ita ba.

• Kuma ayi waƙar da irin kalmomin da suka halatta a shari'a, ba da kalmomin da aka hana a shari'ar ba.

• Mata ne kaɗai suke yin kiɗa da waƙar amma ba maza, ko maza da mata a cakuɗe ba!

Amma bukukuwa da wasannin auren da ake yi a yau sun saɓa wa waɗannan ƙa'idojin, saboda dalilai kamar haka:

• Ana amfani ne da kayan kiɗa irin na zamani kamar goge da molo da kalangu da algaita da makamantansu.

• A cikin waƙoƙin ana amfani da mugayen kalmomin batsa masu siffata mata da giya da sauran ayyukan fasiƙanci.

• Kalmomin suna zuga matasa ga aikata ayyukan alfasha na zina da shaye-shaye da sauran ayyukan saɓon Allaah.

• Uwa uba kuma shi ne inda ake samun cakuɗa a tsakanin maza da mata a wurin, wanda yake haifar da aukuwar munanan ayyukan assha na zubar da mutunci da sauransu.7

Shi ya sa tun tuni malamai suka yi kakkausar suka a kan irin wannan bikin:

• Ibn Rajab ya ce: Dundufarsu kamar irin manyan gangunan nan ne, kuma waƙoƙinsu irin waƙoƙin zamanin jahiliyya ne, irin waɗanda suka saba yi a lokutan yaƙi da makamantan haka.
To, duk wanda ya yi ƙoƙarin kamanta wannan da sauraron irin waƙoƙin batsa da ake haɗa su da kayan kiɗa ko busa ko garaya, to babu shakka ya yi babban kuskure. Domin ya yi ƙiyasi ne tare da samuwar bambanci a tsakanin tushe da reshe!

• Al-Izzu Bn Abdis Salaam ya ce: Amma busa da sauran kayan wasa masu igiya kamar molo da garaya da goge, to mashahuriyar magana dai a wurin malaman mazhabobin nan guda huɗu ita ce: Amfani da su da kuma sauraronsu haram ne.8

Babban abin lura dai a nan shi ne:

Kayan kiɗan da aka yarda da amfani da su a wurin bikin aure shi ne dundufa kaɗai, ban da sauran waɗanda suka shiga ƙarƙashin abin da aka haramta.
Hadisi ya tabbata daga Manzon Allaah (Sallal Laahu 'Alaihi wa Aalihi wa Sallam) ya ce: Waɗansu mutane za su kasance a cikin al'ummata waɗanda za su halatta zina da alharini da giya da kayan kiɗa. Kuma waɗansu mutane za su sauka a gefen wani tsauni ana yi musu goge ko garaya a cikinsu, sai mabaraci ya zo musu da buƙatarsa, su kuma sai su ce masa, ka bari sai gobe ka dawo. Sai kuwa a wayi gari Allaah ya hallaka su gaba ɗaya, an ruguza tsaunin kuma an shafe waɗansu, an mayar da su birai da aladu!
Wannan yana daga cikin hadisai da malamai suka inganta a kan haramcin kayan kiɗa.
Hadisin ya nuna haramcin amfani da kayan kiɗa da busa irin na zamani ta hanyoyi da yawa kamar haka:

• Cewa da ya yi: 'za su halatta' ya nuna a asali wannan abin ba halal ba ne, wani abu ne daga cikin abubuwan da Allaah ya haramta amma su ne suka mayar da shi halal!

• Haɗa shi da sauran abubuwan da kowa ya san haram ne a wuri ɗaya, watau: zina da giya da sanya alharini, ya nuna hukuncinsu iri ɗaya ne watau haramci.

• Hallaka su da Allaah Ta'aala ya yi wannan ma ya nuna cewa sun aikata haram ne.

• Haka kuma shafe su da aka yi zuwa ga siffofin birai da aladu, wannan ma ya nuna sun aikata haram ne.
____________________­_
2. Sunan At-Tirmiziy: 1088, Sunan An-Nasaa'iy: 3369, Sunan Ibn Maajah: 1896, kuma Sahihi ne yana cikin Sahih Al-Jaami': 4206.
3. Sahih Al-Bukkaariy: 5162.
4. Saɓanin abin da ke aukuwa yanzu inda matasa suke ɗaukan amaren a cikin motoci su yi ta tuƙin ganganci da su, wani lokaci ma har a samu hatsari mai haifar da jikkata ko ma rasa rayuka!
5. Sunan An-Nasaa'iy: 3383, kuma Shaikh Albaaniy ya inganta shi a cikin Al-Mishkaat: 3159.
6. Sahih Al-Bukkhaariy: 5147, Sunan Abii Daawud: 4922, Sunan At-Tirmiziy: 1090, Sahih Ibn MaaJah: 1897.
7. Wani mawaƙin Hausa (Malam Aƙilu Aliyu) a lokacin da yake nuna alhininsa a farko-farkon bayyanar wannan fitsarar cewa ya yi:
Sabon sauyi wanda ka canjo,
Wai kuma 'yan mata ke banjo,
Ran angwanci an caccajo,
Su da samari sai zuba ajo,
Cakuɗe tare da matan aure.

Ɓarna ce wannan da ta ɓullo,
Mummuna da rashin kyan kallo,
Masu cira ta sunai mana gwalo,
Mu ne 'yan ƙauye daga Lolo,
Don mun ce a kiyaye aure.

Kai! Wannan abu ya isa aibu!
Mummuna ya kama tasa babu,
Ga saɓon Rabbul Arbaabu,
Ga kuma cutar bayin Rabbu,
Watau nasu mazajen aure.
8. Fiƙ-hus Sunnah Iin Nisaa'i: 401-402.

Wallafar: *Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy*

Dan uwanku *Muneer Yusuf Assalafy*

''`Zaku iya kasancewa damu ta''`

Www.facebook.com/­majlisinsunnah

WhatsApp 08164363661

www.facebook.com/­Muneer-Yusuf-Assalafy­-502666713417261/?

''`Zaku iya aiko da tambaya ta email''`

Massalafy8@gmail.com
Muneeryusuf@yahoo.co­m
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 01 @ 01:36:58 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar:
Ko Kasan Daga Ina Aka Gano Maukibi?


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar

"002 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 2" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: