Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin
[ Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin ]

·It's Haram To Aid, Promote Or Participate In The Oodua Nation Agitation
·Tauhidi ginshikin Musulunci (5)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (4)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (2) - (3)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (1)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (4)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (3)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (1)
·Darussa daga Hadisin Matafiya Uku

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Buhari da Muslim: Babi na Biyu, Babi na Hudu 43 - 52
 
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji Buhari da Muslim: Babi na Biyu, Babi na Hudu 43 - 52

Tare da Sheikh Yunus Is'hak Almashgool, Bauchi

Babi na Biyu: Bayar da daya cikin biyar na ganimar yakin Musulunci yana daga cikin addini:

Littafin bayanin hukuncin farillan daya cikin biyar na ganimar yaki. Bisa fadar Allah Madaukaki:

43. An karbo daga Abdan ya ce: "Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Yunus ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Aliyu dan Husaini ya ba ni labari cewa: Lallai Husain dan Aliyu (AS) ya ba shi labari cewa, lallai Aliyu ya ce: "Ya kasance ina da wani rakumi da na samu daga rabon ganimar Badar. Kuma Annabi (SAW) ya ba ni wani rakumi daga daya cikin biyar na ganima. Lokacin da na yi nufin aure da Fadima 'yar Manzon Allah (SAW) sai na yi wa'adi da wani makerin zinari daga kabilar Kainuka'u yakan tafi tare da ni sai mu yiwo kayan tsaure. Ina nufin in rika sayarwa ga makera. Saboda in yi amfani da kudin wajen walimar aurena. Ina cikin wannan halin tanadi da sai na debi wasu kaya da sirdin taguwa na gurfana da su kusa da gidan wani mutumin Madina. Sai na komo lokacin da tara abin da nake son tarawa. Sai kawai taguwoyin nan nawa biyu na iske an yanke musu tozo an soke kwibinsu biyu an debe hantarsu. Sai na kasa (gaza) tsare idona daga kuka, saboda abin da na gani. Na ce, "Wa ya aikata mini wannan? Sai suka ce mini, "Hamza dan Abdul Mudallib ne ya aikata, yana cikin wannan gida na mutanen Madina inda ake shan giya. Sai na tafi har sai da na shiga Annabi (SAW) yana tare da Zaid dan Harisa, Annabi (SAW) ya fahimci abin da ke cikin fuskata na bacin rai. Sai Annabi (SAW) ya ce, me ya faru da kai? Na ce, "Ya Manzon Allah! Ban taba ganin bakin ciki irin wannan yini ba, Hamza ya fada wa taguwoyina biyu ya katse musu tozo, ya huda cikinsu. Ga shi can a wani gida na shan giya. Annabi (SAW) ya kira aka kawo masa alkyabbarsa ya yafa ta. Sa'an nan ya tafi da kafa na bi shi ni da Zaid dan Harisa har sai da ya isa ga gidan da Hamza ke cikinsa, ya nemi izini suka yi masa izini sai ga su cikin maye. Sai Manzon Allah (SAW) ya rika zargin Hamza bisa abin da ya aikata, sai ga Hamza idanuwansa sun yi ja, Hamza ya yi dubi ga Manzon Allah (SAW) sa'an nan ya daga idonsa, ya yi dubi zuwa ga gwiwarsa. Sa'an nan ya dubi zuwa cibiyarsa sa'an nan ya daga ganinsa zuwa fuskarsa. Sa'an nan Hamza ya ce: "Shin ku ba komai ba ne face bayin babana." Sai Manzon Allah (SAW) ya fahimci cewa lallai shi ya bugu: Sai Manzon Allah (SAW) ya juya bisa duga-duginsa da sauri zuwa baya, muka fita tare da shi."


44. An karbo daga Abdul'aziz dan Abdullahi ya ce: "Ibrahim dan Sa'ad ya ba mu labari daga Salih daga Dan Shihab ya ce: "Urwatu dan Zubair ya ba ni labari cewa: Lallai Uwar Mumminai A'isha (Allah Ya yarda da ita) ta ba shi labari cewa: Lallai Fadima (AS) ta nemi Ababakar Siddik ya ba ta rabonta na gadon dukiyar fai'u (ganimar da aka same ta ba ta hanyar zubar da jini ba) bayan rasuwar Manzon Allah (SAW), tana neman a ba ta gadon abin da Manzon Allah (SAW) ya bari. Sai Abubakar ya ce: "Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ba a gadon mu (Manzanni), abin da muka rasu muka bari sadaka ce." Sai Fadima 'yar Manzon Allah (SAW) ta yi fushi har ta kaurace wa Abubakar ba ta gushe ba tana kaura ce masa har ta rasu. Kuma ta rayu ne a bayan rasuwar Manzon Allah (SAW) da kamar wata shida. (A'isha) ta ce, "Fadima ta kasance tana neman rabonta daga abin da Manzon Allah (SAW) ya rasu ya bari daga dukiyar Khaibara da Fadak da sadakarsa na Madina. Abubakar ya ki karba mata bisa ga haka ya ce: "Ban barin komai daga abin da Manzon Allah (SAW) ya kasance yana aiki da shi face na yi aiki da kamarsa. Kuma lallai ni ina jin tsoron in har na bar wani al'amarinsa da ke aikatawa, zan karkace." Amma sadakarsa da ke Madina sai Umar ya mika ta ga Abbas, amma Khaibar da Fadak, Umar ya rike su ya ce: "Sukan sadakar Manzon Allah (SAW) ne, hakkokinsu sun kasance abin da ke batarwa a shekara, da wasu bukatunsa da suke faruwa. Al'amarinsu na ga hannun wanda yake rike da shugabancin wannan al'umma." Zuhuri ya ce: Suna bisa haka har zuwa Ranar Kiyama."

45. An karbo daga Is'hak dan Muhammad Alfarawiyyu ya ce: "Malik dan Anas ya ba mu labari daga Dan Shihab daga Malik dan Ausu dan Hadasan cewa: "Muhammad dan Jubair ya kasance ya ambata mini wani labari daga hadisinsa. Sai na tafi har na shiga ga Malik dan Awsu na tambaye shi game da wannan Hadisi sai Malik ya ce: "Wata rana ina zaune a cikin iyalina a lokacin da rana ta raba. Sai ga dan aikar Umar dan Khaddab (RA) ya zo mini ya ce mini ka je Sarkin Muminai na kira. Sai tafi tare da shi har na shiga ga Umar sai ga shi a zaune a gado marar shimfida babu shimfida a kusa da shi, ya jingina bisa ga wani matashi na fata (wanda aka cika audugar rimi). Na yi masa sallama, sa'an nan na zauna. Sai ya ce: "Ya Malik, lallai wadansu jama'a daga mutanenka masu yawan iyali sun zo mini da bukata. Kuma na umarta da wannan kyauta, karba ka raba ta a tsakaninsu. Sai na ce, "Ya Sarkin Muminai da dai ka umarci wanina? Sai ya ce: "Kai wannan mutum ka karba! Lokacin ina zaune a gare shi sai ga mai tsaron kofarsa mai suna Yarfa'u ya zo masa ya ce: "Ga Usman da Abdurrahman dan Aufu da Zubair da Sa'ad dan Abu Wakkas sun zo ko za ka yi musu izini? Ya ce: "Na'am, ya yi musu izini, suka shigo suka yi sallama, suka zauna. Sai Yarfa'u ya zauna na dan lokaci, sai ya zo ya ce: "Ga Aliyu da Abbas ko za ka yi musu izini? Ya ce, "Na'am, ya yi musu izini suka shigo suka yi sallama suka zauna. Sai Abbas ya ce: "Ya Sarkin Muminai! Ka yi hukunci a tsakanina da wannan, saboda su suna husuma bisa ga abin da Allah Ya ba ManzonSa na ganimar (fai'u) daga dukiyar kabilar Bani Nadir. Sai jama'ar da ke wurin su Usman da abokansa suka ce, "Ya Sarkin Muminai! Ka yi hukunci a tsakaninsu, don ka hutar da sashensu a kan sashe. Sai Umar ya ce: "Ku yi hakuri! Zan hada ku da Allah, wanda da izininSa sama da kasa ke tsayuwa. Shin ko kun san lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: "Mu (Annabawa) ba a gadonmu, duk abin da muka bari sadaka ne," yana nufin Manzon Allah (SAW) da kansa? Sai wadansu jama'a suka ce: "Lallai ya fadi haka." Sai Umar ya fuskanci Aliyu da Abbas, ya ce: ‘Ina hada ku da Allah, shin ko kun san cewa: Lallai Manzon Allah (SAW) ya fadi haka? Sai suka ce, "Lallai ya fadi haka." Sai Umar ya ce, "Lallai ni zan ba ku labari game da wannan al'amari. Lallai Allah ne Ya kebance ManzonSa da wani abu daga wannan dukiyar fai'u. Bai halatta ta ga kowa ba face shi." Sa'an nan ya karanto fadar Allah Madaukaki cewa: "Bisa ga abin da Allah Ya bai wa ManzonSa na fai'u daga gare su….(K:59:6). Saboda haka wannan ta kasance kebantacciya gare shi, kuma (Annabi) bai karbe ta duka ba, kuma bai fifita kansa ya bar ku ba. Lallai ya mika ta gare ku ya watsa ta cikinku, har ya rage wannan dukiyar ce tasa. Don haka Manzon Allah (SAW) yake ciyar da iyalansa a shekara daga wannan dukiya. Sa'an nan yakan dauki abin da ya saura ya sanya shi a wurin da ake ajiye dukiyar Allah. Haka Manzon Allah (SAW) ya rika aikatawa cikin rayuwarsa. Ina hada ku da Allah shin kun san haka yake aikatawa? Suka ce, "Na'am.' Sai ya fada wa Aliyu da Abbas: Ina hada ku da Allah shin kun san haka? Umar ya ce: "Sa'an nan Manzon Allah (SAW) ya rasu, Abubakar ya ce: "Shi ne waliyin Manzon Allah (SAW) ya karbe ta, ya yi aiki cikinta da abin da Manzon Allah (SAW) ya yi aiki da shi. Kuma Allah Shi ne Masani lallai shi mai gaskiya ne mai da'a, mai shiryarwa kuma mai bin gaskiya. Sa'an nan Abubakar ya rasu. Ni na kasance waliyyin (mai bi wa) Abubakar na karbe ta shekara biyu, a cikin shugabancina zan yi aiki da irin yadda Manzon Allah (SAW) da kuma irin yadda Abubakar ya yi aiki cikinta. Allah Shi ne Mafi sani lallai ni mai gaskiya ne a cikinta. Kuma ni mai da'a ne, mai shiryarwa, kuma mai bin gaskiya. Sa'an nan ku (Aliyu da Abbas) kun zo kuna yi mini magana, kuma maganarku daya ce, kuma al'amrinku daya ne, kai Abbas ka zo mini kana neman rabonka daga dan dan uwanka. Wannan kuma ya zo yana nufin Aliyu, yana neman rabon matarsa daga mahaifinta (AS) na ce, muku: Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ba a gadonmu, abin da muka bari sadaka ce." Lokacin da ya bayyana mini in mika ta gare ku, bisa alkawarin Allah da amanarsa tana kanku lallai za ku yi aiki cikinta da irin abin da Manzon Allah (SAW) yake aiki cikinta, da kuma irin yadda Abubakar ya yi aiki cikinta, kuma da irin abin da nake aiki cikinta tunda na fara shugabanci, kuka ce in ba ku, to ga ta nan na ba ku. Ina hada ku da Allah shin yanzu na mika ta gare ku. Jama'a suka ce, "Na'am," sai ya fuskanci Aliyu da Abbas ya ce: "Ina hada ku da Allah shin na mika ta gare ku? Suka ce, ‘Na'am," sai ya ce: "Sai dai ku nemi hakkin waninku gare ni, ba wannan ba? Ina rantsuwa da Wanda da izininSa sama da kasa ke tsayuwa ba zan yi hukunci da wanin haka ba. Idan kun gajiya game da ita to ku miko mini ita, lallai ni zan isar muku."

46. An karbo daga Abu Nu'aman ya ce: "Hammadu ya ba mu labari daga Abu Jamrat Duba'iyyu ya ce, na ji Dan Abbas (Allah Ya yarda da su), yana cewa: "Ayarin Abdu Kaisu ya taba zuwa suka ce: "Ya Manzon Allah! Lallai mu kabilar Rabi'atu a tsakaninmu da kai akwai kafiran Mudar ba mu da ikon zuwa gare ka face a cikin watan Almuharram. Ka umarce mu da wasu abubuwar da za mu yi riko da su, mu kira wadanda suke bayanmu da shi." Sai ya ce: "Ina umartarku da abubuwa hudu, kuma zan hane ku game da abubuwa hudu. Na farko imani da Allah, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Ya kulla yatsarsa da nunin cewa daya. Da tsayar da Sallah bayar da Zakka da azumin Ramadan. Kuma lallai za ku bayar da daya cikin biyar na ganimar yaki. Kuma zan hane ku game da giyar masaki da na akushi da na tukunya da na gora."

Babi na Uku: Bayani game da ciyar da matan Annabi (SAW) bayan rasuwarsa:

47. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: "Malik ya ba mu labari daga Abu Zinad daga A'araji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: "Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ba a rabon gadona dinari-dinari. Babu abin da zan bari face ga ciyarwar iyalaina da masu yi mini aiki, bayan haka dukan abin da na bari sadaka ne."

48. An karbo daga Abdullahi Abu Shaiba ya ce: "Abu Usamatu ya ba mu labari ya ce, Hisham ya ba mu labari daga babansa daga A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya rasu babu komai cikin dakina wanda rai mai hanta zai ci face rabin mudun sha'ir wanda ke cikin kwanso. Na rika ci tsawon lokaci har ya kare."

49. An karbo daga Musaddad ya ce: "Yahya ya ba mu labari daga Sufiyan ya ce: Abu Is'hak ya ba ni labari ya ce, na ji Amru dan Haris ya ce: "Annabi (SAW) bai bar komai ba face takwabinsa da farar alfadararsa da wata kasa da ya bar ta sadaka."

Babi na Hudu:

Abin da ya zo cikin bayanin gidajen matan Annabi (SAW) da abin da aka jingina zuwa ga dakunansu. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: "Ku tabbata cikin dakunanku, kuma kada ku rika fitar banza ta Jahiliyya…." (K:33:33)." Da fadar Allah Madaukaki cewa: "Kada ku shiga gidan Annabi (SAW) face in an yi (ya yi) muku izini…"(K:33:53)."

50. An karbo daga Habban dan Musa da Muhammad sun ce: "Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Ma'amar da Yunus sun ba mu labari daga Zuhuri ya ce: "Ubaidullahi dan Abdullahi dan Utbatu dan Mas'ud cewa: Lallai A'isha matar Annabi (SAW) ta ce: "Lokacin da ciwon Annabi (SAW) ya tsananta sai ya nemi izinin matansa bisa ga ya yi jinya a dakina, sai suka yi masa izini."

51. An karbo daga Dan Abu Maryam ya ce: "Nafi'u ya ba mu labari ya ce, na ji Dan Abu Mulaikatu ya ce: "A'isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: "Annabi (SAW) ya rasu a cikin dakina a tsakanin kirjina kusa ga kuncina (haba), kuma Allah Ya hada yawuna (miyau) da yawunsa." Ta ce, "Abdurrahman ya shigo da Asiwaki lokacin Annabi (SAW) jinyarsa kuma ya yi raunin tauna (asiwaki, sai ya nuna yana son ci) sai na karba na tauna masa, na goge masa baki da shi."(Wannan shi ne fassarar haduwar yawunta da yawunsa).

52. An karbo daga Sa'id dan Ufair ya ce: "Laisu ya ba ni labari ya ce, Abdurrahman dan Khalid ya ba ni labari daga Dan Shihab daga Aliyu dan Husain cewa: Lallai Safiyyatu matar Annabi (SAW) ta ba shi labari cewa: Lallai ita ta tafi ga Manzon Allah (SAW) domin ta ziyarce shi lokacin da yake I'itikafi a masallaci a goman karshe na Ramadan. Sai ta mike domin ta koma gida, Manzon Allah (SAW) ya mike domin ya yi mata rakiya har sai da suka kai ga kofar masallaci kusa da kofar Umma Salma matar Annabi (AS) sai wadansu mutum biyu daga mutanen Madina suka zo, su za su shude (wuce). Da suka ga Manzon Allah (SAW) sai su ka tafi da sauri. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, musu: Ku komo ku ga ko wace ce tare da ni. Sai suka ce: "Subhanallah ya Manzon Allah! Haka ya yi musu girma, sai Manzon Allah (SAW) ya ce musu: "Lallai shaidan yana isar wa mutum mummunan tunani har ga magudanar jini. Lallai ni na ji tsoron kada ya jefa muku wani abu (tunani) a cikin zukatanku ne."
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 08 @ 22:26:13 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji

"Buhari da Muslim: Babi na Biyu, Babi na Hudu 43 - 52" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: