Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Al'Adun Musulmi Da Darajoji
[ Al'Adun Musulmi Da Darajoji ]

·Falalar Darare Goma na Zul-Hajji
·Dabbobin Layya da kwanakin 10 na farkon Zul-Hajji
·Azumi da abubuwan da yake koyarwa (4)
·Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
·Buhari Da Muslim: Babi Na Hudu 140 - 142 & 148
·Buhari da Muslim: Babi na Talatin da Biyu 114 - 124

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Buhari da Muslim: Babi na Tara, Babi na Goma Sha Uku & Babi na Goma Sha Biya
 
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji Buhari da Muslim: Babi na Tara, Babi na Goma Sha Uku & Babi na Goma Sha Biyar 61 - 63 & 72 - 79

Buhari da Muslim: Babi na Tara, Babi na Goma Sha Uku & Babi na Goma Sha Biyar 61 - 63 & 72 - 79

Tare da Sheikh Yunus Is'hak Almashgool, Bauchi

61. An karbo daga Sa'id dan Muhammad Aljarmiyyu ya ce: "Yakub dan Ibrahim ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba mu labari cewa: Lallai Walid dan Kasir ya ba shi labari daga Muhammad dan Amru dan Halhalatu Addailiyyu ya ba shi labari cewa: Lallai dan Shihab ya ba shi labari cewa: Lallai Aliyu dan Husain ya ba shi labari cewa: Lallai su lokacin da suka iso Madina daga wajen Yazid dan Mu'awiyya inda aka kashe Husain dan Aliyu (Allah Ya yi masa rahama), sai Miswar dan Makhramat ya iske shi ya ce masa: Shin ko kana da wata bukata da za ka umarce ni da ita? Na ce masa, "A'a, sai ya ce: "Shin ko za ka ba ni takwabin Manzon Allah (SAW) ina jin tsoron kada mutane su rinjaye ka a kansa yau? Ina rantsuwa da Allah idan ka ba ni ba za su samu ikon karbarsa face in sun kashe ni." Kuma ya ce: "Lallai Aliyu dan Abu Dalib (RA) ya taba neman 'yar Abu Jahil bisa ga nemansa ga Fadima (AS) (wato suna tare). Sai na ji Manzon Allah (SAW) yana huduba ga mutane a mumbarinsa wannan. Lokacin na balaga sai ya ce: "Lallai Fadima tawa ce, kuma lallai ni ina tsoron a fitine ta cikin addininta (bisa ga 'yar Abu Jahil). Sa'an nan ya ambaci surukuntarsa da kabilar Abdu Shams ya yabe shi bisa ga surukuntarsa da shi. Ya ce: Ya yi mini magana ya yi mini gaskiya, ya yi mini alkawari ya cika. Kuma lallai ni, ban zamo mai haramta halal, ko kuma mai halatta haram ba. Amma wallahi 'yar Manzon Allah (SAW) ba ta haduwa da 'yar makiyin Allah har abada."


62. An karbo daga Kutaiba dan Sa'id ya ce: "Sufiyan ya ba mu labari daga Muhammad dan Surakatu daga Munzir daga Abu Hanifiyyatu ya ce: "Da dai Aliyu (Allah Ya yarda da shi), ya kasance yana son ya zame wa Usman (Allah Ya yarda da shi) tunatarwa bisa munantawa da ya yi masa a ranar da mutane suka zo suna kai kukan tawagar masu karbar Zakkar Usman. Sai (Aliyu) ya ce: "Ka tafi ga Usman ka ba shi labari cewa: Lallai wannan sako takardar karbar sadaka ce ta Manzon Allah (SAW) don haka ka umarci ma'aikatanka su yi aiki da ita, sai na je da ita, ya ce: "Ka wadatar da ni game da wannan." Sai na tafi da ita ga Aliyu na ba shi labari." Abu Hannafiyyatu ya ce: "Babana ya aike ni cewa: Ka karbi wannan takarda ka tafi da shi zuwa ga Usman (RA), abin da ke cikinta umarnin Manzon Allah (SAW) ne game da yadda za a rika karbar sadaka."

Babi na Shida:

Dalilin da ke tabbatar da daya cikin biyar na ganimar yaki. Saboda rage wasu bukatun Manzon Allah (SAW) ne da miskinai. Da bayanin baiwar da Annabi (SAW) ya yi wa mutane Suffah (talakawa) da gwagware kuma da bayanin lokacin da Fadima (RA) ta tambaye shi tana kukan rashin mai yi mata hidima saboda wahalar nika da kwaba alkama. Saboda ya ba ta kuyangi sai ya mayar da ita zuwa ga yarda da al'amarin Allah.

63. An karbo daga Badal dan Muhabbar ya ce: "Shu'abah ya ba mu labari ya ce, Hakam ya ba ni labari ya ce, na ji Dan Abu Wa'il ya ce, Aliyu ya ba mu labari cewa: Lallai Fadima (AS) ta taba kaiwa kukan abin da ke faruwa da ita na wahalar nika da kwaba alkama. Saboda haka da ta ji an zo wa Manzon Allah (SAW) da kuyangi na fursunonin yaki, sai ta tafi ta roke shi (Annabi) ya ba ta mai yi mata hidima, sai ba ta iske shi gida ba. Sai ta fada wa A'isha (RA) da Annabi (SAW) ya komo A'isha ta ambata masa. (Fadima) ta ce: "Sai (Annabi) ya zo muna gida lokacin har mu shiga kwanci, sai muka yi kokarin tashi domin taryarsa sai ya ce: "Ku zauna inda kuke, har ina jin sanyin kafarsa bisa kijina (inji Fadima). Sai ya ce: "Shin in nuna muku abin da ya fi Abin da kuka nema gare ni alheri, idan kuka yi riko da su lokacin barcinku? Ya ce: Ku yi kabbara sau talatin da hudu (34). Ku yi tahmidi talatin daidai (30). Ku yi tasbihi sau talatin (30). Wannan ya fi muku alheri daga abin da kuka roke ni game da shi."

72. An karbo daga Muhammad dan Ala'u ya ce: "Dan Mubarak ya ba mu labari daga Ma'amar daga Hammam dan Munabbih daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: "Annabi (SAW) ya ce, "Wani Annabi ya taba nufin fita yakin daukaka kalmar Allah tare da jama'arsa, sai ya ce: "Duk wanda ya yi sabon aure bai sadu da ita ba kuma yana son saduwa da ita, to kada ya bi ni zuwa wannan yaki. Haka kuma duk wanda ya gina wani gida da bai masa rufi ba, kuma yana son ya yi masa rufi kada ya biyo ni. Haka wanda ya sayi tumaki ko wasu dabbobin da ke dakon haihuwarsu. Daga nan ya fita zuwa yakin da ya kusanci wata alkarya kuma sai ga lokacin Sallar La'asar ya yi. Ko ya ce rana ta yi kusan buya kuma bai yi Sallar La'asar ba kuma ga yaki. Sai ya ce ga rana: "Ke ma wadda ake umarta ce, kuma ni ma an umarce ni. Ya Allah! Ka tsare ta gare mu. Sai aka tsare ta har sai da Allah Ya ba su cin nasarar yaki. Ya tara ganima mai yawa wuta ta zo don ta cinye ta, ta gaza cin ta. Sai (Annabin) ya ce: "Lallai daga cikinku akwai wanda ya boye wani abu (gululu). Saboda haka kowace kabila ta zo ta yi mini mubaya'a dai-daya. Sai hannun mutum biyu ko ya ce, mutum uku suka makale da hannunsa (Annabi). Ya ce: "Cikinku akwai gululu, sai suka zo da wani dunkulen zinari kamar kan saniya suka sanya ta. Sai wuta ta zo ta cinye ganimar. (Annabi) (SAW) ya ce: "Sa'an nan Allah Ya halatta mana ganimomi, kuma Ya ga rauninmu da gazawarmu Ya halatta mana ita."

Babi na Tara: Ganima ana raba ta ce ga wanda ya halarci fagen yaki:

73. An karbo daga Sadakatu ya ce: "Abdurrahman ya ba mu labari daga Malik daga Zaid dan Aslam daga Babansa ya ce: "Umar (Allah Ya yarda da shi) ya ce: "Ba domin Musulmi da suke gaba gare mu ba, da ban taba cin wata kasa da yaki ba. Face na raba ta a tsakanin jama'arta kamar yanda Annabi (SAW) ya raba dukiyar Khaibara."

Babi na Goma: Hukuncin wanda ya fita yakin Musulunci domin samun ganima shin ko ladarsa ya tauye?:

74. An karbo daga Muhammad dan Bashar ya ce: "Ghundar ya ba mu labari ya ce, Shu'abah ya ba mu labari daga Amru ya ce: "Na ji Abu Wa'il ya ce, Abu Musal Ash'ariyuu (Allah Ya yarda da shi), ya ba mu labari ya ce: "Wani Balaraben kauye ya zo ga Annabi (SAW), ya ce: "Daga cikin mutane akwai mai yaki don ganima. Kuma akwai mutumin da ke yakin nan saboda a yabe shi. Kuma domin a ga matsayinsa. To, wane ne domin daukaka kalmar Allah? Sai (Annabi) ya ce: "Wanda ya yi yakin nan domin kalmar Allah ta kasance madaukakiya shi ne domin Allah."

Babi na Goma Sha Daya: Shugaba yana iya rabon ganima ga wadanda suke nan kuma yana iya ajiye wani abu ga wadanda ba su nan halarce:

75. An karbo daga Abdullahi dan Abdulwahab ya ce: "Hammad dan Zaid ya ba mu labari, daga Ayyub daga Abdullahi dan Abu Mulaikatu cewa: "Lallai Annabi (SAW) an taba yi masa kyautar wasu taguwoyin siliki masu maballan zinari. Sai ya raba su ga wadansu daga sahabbansa ya janye daya daga ciki ya ajiye saboda Makhramatu dan Naufal. Sai ya zo tare da shi da Miswar dan Makhramatu ya tsaya a kofa. Ya ce, "Kira mini shi, sai Annabi (SAW) ya ji muryarsa ya riko wata taguwar yana rataye da ita, sai ya fuskance shi da wannan taguwar siliki ya ce: "Ya Abu Miswar na ajiye maka wannan ce, ya fadi haka har sau biyu, saboda cikin halayensa (Makhrama) akwai wani abu."

Babi na Goma Sha Biyu: Yadda Annabi (SAW) ya raba ganimar Bani Kuraizat da Bani Nadir da bayanin abin da ya ajiye saboda wasu bukatunsa.

76. An karbo daga Abdullahi dan Aswad ya ce: "Mu'atamir ya ba mu labari daga babansa ya ce, na ji Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), yana cewa: "Mutum yakan kasance yana sanya gonar dabinai kyauta ga Annabi (SAW) har sai da Allah Ya ba shi budi a kan Bani Kuraiza da Nadir. Daga nan ya kasance bayan haka yana mayar wa jama'a kyautarsu."

Babi na Goma Sha Uku: Albarkar dukiyar yakin daukaka kalmar Allah mai shi (mai yi) yana raye ko yana mace tare da Annabi (SAW) ko da mai shugabantar al'amura:

77. An karbo daga Is'hak dan Ibrahim ya ce: "Na ce da Abu Usamatu shin Hisham dan Urwatu ya ba ku labari daga babansa daga Abdullahi dan Zubair ya ce: "Lokacin da Zubair ya tsaya a ranar Yakin Jamal. Ya kira ni na tsaya a gefensa sai ya ce: "Ya dan dana! Lallai ka sani yau babu wanda za a yaka face azzalumi ne ko wanda aka zalunta. Kuma ban ganin kaina face ina daga cikin wadanda za a kashe bisa zalunci. Kuma lallai mafi girman nufina, shin kana ganin ko idan muka biya bashin da ke kaina dukiyarmu za ta saura kuwa? Sai ya ce: "Ya dan dana! Ka sayar da kayanmu ka biya mini bashi. Kuma ya yi wasiyya da daya cikin uku na dukiyar, daya cikin uku ga dansa Abdullahi dan Zubair, yana cewa: Daya cikin ukun uku. Kuma dukan abin da ya rage dai a ba da daya cikin ukun uku, ga 'ya'yanka. Hisham ya ce: "Kuma wadansu daga cikin 'ya'yan Abdullahi sun gama auna sashen yawan 'ya'yan Zubair kamar Khubaib da Abbad saboda shi a wannan rana yana da yara maza tara da 'ya'ya mata tara. Abdullahi ya ce: "Sai ya rika yin mini wasiyya da biyan bashinsa. Yana cewa: "Ya dan dana! Idan har ka gajiya game da biyan bashin nan ka nemi taimakon waliyyina. Ya ce, "Wallahi ban san wane ne ba har sai da na ce, "Ya Baba! Wane ne waliyyinka? Ya ce: "Allah!" Ya ce: "Wallahi ban taba fadawa cikin bakin ciki irin na wannan bashi ba face na ce, Ya Waliyyin Zubair! Ka biya masa bashinsa. Daga nan sai Allah Ya taimake ni wajen biya. A ran nan dai aka kashe Zubair (Allah Ya yarda da shi), bai bar Zinari daya ko Dirhami ba, face wasu filaye a dawa da gida goma sha daya a Madina. Da gidaje biyu a Basrah da gida daya a Kufah da wani gida a Masar. Ya ce: "Abin da ya sanya bashi ga babana saboda idan mutum ya zo da ajiyar kudinsa sai ya ce: "Ka bar mini bashinsa saboda ina jin tsoron halakarsu." Kuma ya ce: "Shi bai taba shugabantar kowa ba kuma bai taba zama mai karbar haraji ba, abin da ya mallaka face sun kasance ta hanyar ganima ne da ake fita yakin daukaka kalmar Allah tare da Manzon Allah (SAW), ko yakin da yayi tare da Abubakar da Umar da Usman (Allah Ya yarda da su)." Abdullahi ya ce: "Saboda haka da na lasaffa abin da ke kansa na bashi sai na samu kamar miliyan biyu ne da dubu dari biyu." Sai Hakim dan Hizam ya hadu da Abdullahi dan Zubair ya ce: "Ya dan dan uwana! Nawa ne ke kan dan uwana na bashin? Sai ya boye masa, ya ce: "Dubu dari ne." sai Hakim ya ce, "Wallahi ban tsammanin dukiyarku zan ta biya wannan bashi." Sai Abdullahi ya ce: "Yaya za ka yi idan haka aka ce: "Ana bin ka miliyan biyu da dubu dari biyu?" Ya ce: "Ban ganin za ku iya biyan wannan, idan har kun gajiya to, ku nemi taimakawata." (Abdullahi) ya ce: "Zubair ya sayi gonar Gabah ce da kamar dubu dari da saba'in." Sai Abdullahi ya sayar da ita bisa farashin miliyan daya da dubu dari shida. Sa'an nan ya mike ya ce: ‘Wanda ke bin Zubair bashi ya zo ya karba a gonarmu ta Gabah." Sai Abdullahi dan Ja'afar ya zo masa, saboda shi yana bin Zubair dubu dari hudu. Ya ce da Abdullahi idan kuna so sai in bar muku? Abdullahi ya ce: "A'a, in kun so ina yi muku jinkiri zuwa wani lokaci? Abdullahi ya ce: ‘A'a," Abdullahi ya ce, sai ya ce: "Ku yanka mini wani yanki daga gonar nan." Sai Abdullahi ya ce: "An b aka daga nan zuwa can." Da ya sayar sai ga shi ta biya bashinsa. Ya rage rabon mutum hudu da rabi (daga fadin gonar). Sai ya gabata ga Mu'awiyya yana tare da Amru dan Usman da Munzir dan Zubair da Dan Zama'atu. Sai Mu'awiyya ya ce: "Na wane kuka sanya wa Gabah (gonarku) kudin? Ya ce: "Kowane kaso na bisa farashin dubu dari." Ya ce: "Kaso nawa suka saura? Ya ce, "Kaso hudu da rabi." Munzir dan Zubair ya ce: "Na dauki rabo guda bisa dubu dari." Amru dan Usman ya ce: "Na dauki kaso daya bisa dubu dari." Dan Zama'atu ya ce: "Na dauki kaso daya bisa dubu dari." Sai Mu'awiyya ya ce: "Nawa ya saura? Ya ce: "Kaso guda daya da rabi." Ya ce: "Na dauke su bisa dubu dari da hamsin." Ana nan haka sai Abdullahi dan Ja'afar ya sayar da rabonsa ga Mu'awiyya bisa farsashin dubu dari shida." Da Abdullahi ya kare biyan wannan bashi. Sai 'ya'yan Zubair suka ce: "To ka raba sauran a tsakaninmu bisa gadonmu." Ya ce, "A'a, wallahi ba zan raba ba ta a tsakaninku sai na yi shela har lokutan bashinsa ya gabato wato lokacin Hajj da kamar shekara hudu. Ya rika cewa: Duk wanda ke bin Zubair bashi ya zo mu biya shi. Sai ya kasance kowace shekara da ta gabato sai ya rika shela lokacin Hajji da shekara hudu suka shude sai ya raba abin da ya saura a tsakaninsu." Kuma Zubair ya kasance yana da mata hudu, ya dauke daya cikin uku (na wasiyya), daga sai da kowace mace ta samu rabon miliyan daya da dubu dari biyu. Kuma dukiyarsa da ya bari da aka lasaffa aka samu miliyan hamsin da dubu dari biyu." (Wannan ya bayyana mana albarkar dukiyar ganima, koda yake mutane zasu fahimci yadda ya tara wannan bashi mai yawa a kansa don tsoron kada ya ci amanar masu bashi ajiyar dukiyoyinsu Allah Ya sa mu dace).

Babi na Goma Sha Uku: Albarkar dukiyar yakin daukaka kalmar Allah mai shi (mai yi) yana raye ko yana mace tare da Annabi (SAW) ko da mai shugabantar al'amura:

Babi na Goma Sha Hudu: Idan shugaba ya aika da wani dan aike cikin wata bukata ko ya shugabantar da shi da wani matsayi shin za a yi rabo da shi?:

78. An karbo daga Musa ya ce: "Abu Awanatu ya ba mu labari ya ce, Usman dan Mauhib ya ba mu labari daga Dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: "Abin da ya tsare Usman (RA) daga Yakin Badar saboda ya kasance 'yar Manzon Allah (SAW) tana aurensa kuma lokacin ta kasance ba ta da lafiya. Sai Annabi (SAW) ya ce masa: "Lallai kai ma kana da sakamakon wanda ya halarci Yakin Badar da rabonsa (na ganima)."

Babi na Goma Sha Biyar:

Dalilin sanya daya cikin biyar na ganimar yaki bisa bukatun Musulmi. Haka ya nuna bisa ga abin da kabilar Hawazin suka roka daga Annabi (SAW) bisa ga ya mayar musu da ganimar yakinsu gare su. Saboda shi an shayar da da shi da wani daga cikinsu, sai ya nemi izinin Musulmi. Da bayanin abin da Annabi (SAW) ya kasance yana alkawari da shi ga mutane cewa: Zai ba su wani abu daga dukiyar fai'u (ganimar da aka samu ba ta hanyar zubar da jini ba). Da karin da yake yi daga daya cikin biyar na ganimar yaki. Da bayanin abin da ya bayar ga mutanen Madina da kuma magana kan abin da ya bayar ga Jabir dan Abdullahi daga dabinan Khaibara.

79. An karbo daga Sa'id dan Ufair ya ce: "Laisu ya ba mu labari ya ce Ukail ya ba ni labari daga Dan Shihab ya ce: "Urwatu ya ambata cewa, lallai Marwan dan Hakam da Miswar dan Makhramat sun ba shi labari cewa: Lallai Manzon Allah (SAW) ya fada a lokacin da tawagar Hawazin suka zo masa suna masu mika wuya (Musulunta). Sai suka roke shi da ya mayar musu da dukiyarsu da fursunan yakinsu. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce musu, "Mafificiyar magana gare ni ita ce wadda ta fi gaskiya. Wato su zabi daya cikin biyu dukiya ko fursunan yaki. Saboda na yi jinkirin rabon ganimarsu. Kuma hakika Manzon Allah (SAW) ya jira karshensu (al'amarinsu) da kamar kwana goma lokacin da ya tafi Da'ifa. Lokacin da suka fahimci lallai Manzon Allah (SAW) ba zai ba su duka face daya cikin abubuwan nan biyu, sai suka ce: "Lallai mun zabi fursunan yakinmu." Sai Manzon Allah (SAW) ya mike cikin jama'ar Musulmi ya yabi Allah da abin da Ya dace da Shi. Sa'an nan ya ce: Bayan haka lallai hakika na ga ya kamata in ba su fursunan yakinsu, amma duk wanda yake son ya bar mini rabonsa to ya aikata haka. Kuma duk wanda ke son in ba shi rabonsa zan ba shi bisa ga abin da Allah Ya ba ni fai'u shi yana neman hakkinsa. Sai mutane suka ce, "Ya Manzon Allah! Mun halatta maka, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: Bisa ga haka dai ba za mu fahimci wanda ya bar mana ba da wanda bai bar mana ba. Saboda haka ku tafi ku yi shawari abin da kuka yanke shawari da malamanku sai su bayyana mana. Sai suka koma ga manyansu suka yi magana da su. Sa'an nan suka komo ga Manzon Allah (SAW) suka ba shi labari cewa: Lallai su, sun halatta masa kuma sun yi izini." Wannan shi ne labarin da ya iso gare mu game da fursunan yakin da aka kamo daga Hawazin.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 08 @ 22:29:10 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji

"Buhari da Muslim: Babi na Tara, Babi na Goma Sha Uku & Babi na Goma Sha Biya" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: