Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

 

 
Buhari da Muslim: Babi na Talatin da Biyu 114 - 124
 
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji Buhari da Muslim: Babi na Talatin da Biyu 114 - 124

Tare da Sheikh Yunus Is'hak

Almashgool, Bauchi

Babi na Ashirin da Takwas: Yadda shugaba ke aikawa ga wanda ya warware alkawari:

114. An karbo daga Abu Nu'aman ya ce: "Sabit dan Yazid ya ba mu labri ya ce, Asim ya ba mu labari ya ce: "Na tambayi Anas (Allah Ya yarda da shi), game da kunuti yaushe ake yi? Ya ce, "Kafin ruku'u ne." Sai ya ce: "Lallai wane yana riyawa ka ce: "Bayan ruku'u ne." Sai ya ce: "karya ya yi." Sa'an nan ya bayar da labari daga Annabi (SAW) cewa: Lallai shi ya yi kunuti kamar wata daya bayan ruku'u yana addu'a a kan kabilun Bani Sulaim." Ya ce, "Kuma ya taba aikawa da wadansu mutum arba'in ko ya ce, saba'in, makaranta Alkur'ani zuwa ga wadansu mutane daga mushirikai. Daga baya suka juya baya suka kashe su, saboda tsakaninsu da shi (Annabi SAW) akwai sulhu. Kuma ban taba ganin abin da ya bata wa Annabi (AS) rai ba kamar mutuwar wadannan mutane ba."

Babi na Ashirin da Tara:

Karbar amanar da mata suka dauka da karbar makwabtakarsu:

115. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: "Malik ya ba mu labari daga Abu Nadar bawan Umar dan Ubaidullahi cewa: "Lallai Abu Murrat bawan Ummi Hani 'yar Abu Dalib ya ba shi labari cewa: Lallai shi ya ji Ummu Hani 'yar Abu Dalib tana cewa: "Na tafi zuwa ga Manzon Allah (SAW) a ranar cin Makka na same shi yana wanka Fadima 'yarsa tana masa shamaki, sai na yi masa sallama ya ce: "Wace ce? Na ce, "Ummu Hani ce 'yar Abu Dalib." Sai ya ce: "Maraba da Ummu Hani." Lokacin da ya kare daga wankansa sai ya mike ya yi Sallah raka'a takwas yana lullube da wani mayafi." Sai na ce, "Ya Manzon Allah! Dan uwana ya riya cewa zai kashe wani mutumin da na karbi makwabtakarsa (tsare shi). Wane dan Hubair. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: "Hakika mun karba miki makwabtakar wanda kika yi makwabtakarsa ya Ummi Hani. Ta ce: "Wannan lokaci ne da hantsi."

Babi na Talatin:

Amanar Musulmi da makwabtakarsu duk daya ce, waninsu zai iya dauke musu:

116. An karbo daga Muhammad ya ce: "Waki'u ya ba mu labari daga Ama'ashi daga Ibrahim Tamimi daga babansa ya ce: "Aliyu ya taba yin mana huduba sai ya ce: "Ba mu da wani littafi tare da mu wanda muke karanta shi face abin da ke cikin wannan takarda. Sai ya ce: "Abin da ke cikinsa hukuncin raunuka da bayanin haramcin diyyar tozon taguwa. Kuma Madina harami ce tun daga Airu zuwa wuri kaza. Wanda ya farar (kaga bidi'a) abin farawa cikinta, ko ya taimaka wa mai fara (kaga) bidi'a cikinta, to la'anar Allah da mala'iku da mutane gaba daya tana kansa. Ba a karbar (amsar) dukan aiki ko adalci (daga gare shi). Haka wanda ya shugabanci abin da ba a nada shi ba yana da misalin haka. Kuma amanar Musulmi duka daya ce, duk wanda ya saba wa Musulmi shi ma yana da misalin haka."

Babi na Talatin da Daya:

Idan masu karbar Musulunci suka ce, "Mun juyo, saboda ba su iya fadar cewa: Mun musulunta ba." Dan Umar ya ce: "Saboda wannan Khalid ya rika yakar wadansu mutane. Sai Annabi (SAW) ya ce: "Ya Allah! Ba hannuna cikin abin da Khalid ya aikata." Umar ya ce: "Idan ya ce: Matarsu (wato kada ka ji tsoro) to lallai ya nuna amintar da shi. Kuma lallai Allah Ya san harsuna dukansu." Umar ya taba cewa ga (Hurmuzi mutum Farisa): Yi magana da harshenka babu wani laifi." (Saboda tabbatar da tsaro ta hanyar sulhu).

Babi na Talatin da Biyu:

Kulla sulhun zaman lafiya tare da mushirikai bisa wata dukiya da waninta. Da bayanin laifin wanda ya saba wa alkawari. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: "Idan suka karkata zuwa ga zaman lafiya kai ma ka karba musu…"(K:8:61).

117. An karbo daga Nusaddad ya ce: "Bishiru dan Mufaddal ya ba mu labari ya ce, Yahya ya ba ni labari daga Bishiru dan Yassar daga Sahlu dan Abu Hasmat ya ce: "Abdullahi dan Sahlu ya tafi shi da Muhayyasatu dan Mas'ud dan Zaid zuwa Khaibara lokacin suna cikin sulhu, sai suka rarraba bisa hanya, sai Muhayyasatu ya iske Abdullahi dan Sahlu yana magagin mutuwa cikin jini, da ya mutu ya bisne shi. Da ya iso Madina, sai Abdurrahman dan Sahlu da Muhayyisa da Huwaisatu yaran Mas'ud suka tafi zuwa ga Annabi (SAW). Sai Abdurrahman ya mike zai yi magana sai (Annabi SAW) ya ce: "Bari babba ya yi magana! Bari babba ya yi magana! Saboda shi ne yaro a cikin jama'ar. Da ya yi shiru sauran biyu suka yi magana: (Annabi SAW) ya ce: "Za ku rantse ku cancanci hakkin dan uwanku da aka kashe? Suka ce, "Kamar kaka (yaya) za mu rantse ba mu da shaida, kuma ba mu gani da idonmu ba? Ya ce: "To, Yahudawa za su kare kansu da rantsuwa Hamsin." Suka ce: "Kaka za mu yarda da rantsuwar kafirai? Sai Annabi (SAW) ya biya diyyar daga wurinsa."

Babi na Talatin da Uku: Fifikon cika alkawari:

118. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: "Laisu ya ba mu labari daga Yunus daga Dan Shihab daga Ubaidullahi dan Abdullahi dan Utba cewa: "Lallai Abdullahi dan Abbas ya ba shi labari cewa: Lallai Abu Sufiyan dan Harb ya ba shi labari cewa: Lallai Hirakala ya aika zuwa gare shi lokacin da yake cikin ayarin Kuraishawa a lokacin da suke sulhun barin yaki da Annabi (SAW) ya kulla da Kuraishawa."

Babi na Talatin da Hudu:

Idan kafirin amana ya yi sihiri za a yafe masa? Dan Wahab ya ce, Yunus ya ba ni labari daga Dan Shihab cewa: An tambaya cewa: Shin kafirin amana idan ya yi sihiri za a kashe shi? Ya ce: "Labari ya isa gare mu cewa: Manzon Allah (SAW) hakika an yi masa haka (sihiri) amma bai kashe wanda ya yi masa haka ba kuma Ahlul Kitab ne."

119. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: "Yahya ya ba mu labari ya ce, Hisham ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba ni labari daga A'isha (RA) cewa: Lallai Annabi (SAW) an yi masa sihiri har sai da ya kai yana ganin kamar ya aikata wani abu alhali kuwa bai aikata shi ba."

Babi na Talatin da Biyar: Abin da aka hana game da yaudara bisa fadar Allah Madaukaki cewa: "Idan sun yi nufin su yaudare ka lallai Allah Ya isar maka kai da mummunai…."(K:8:62).

120. An karbo daga Humaidiyyu ya ce: "Walidu dan Muslim ya ba mu labari, ya ce, Abdullahi dan Ala'u dan Zaid ya ba mu labari ya ce: Na ji Busra dan Ubaidullahi cewa, lallai shi:Ya ji Abu Idris ya ce: ‘Ya ji Aufu dan Malik ya ce: "Na tafi zuwa ga Annabi (SAW) a lokacin Yakin Tabuka yana cikin wata kubba (lema) ta fata sai ya ce: "Ka lissafa abubuwa shida kafin Sa'ar Kiyama: Na farko dai mutuwata; na biyu cin Baitil Makdisi da yaki; sa'an nan yawan mace-mace wadanda za su same ku, kamar mutuwar garken tumaki; sa'an nan watsuwar dukiya har za a bai wa mutum dinari dari ya doge yana mai fushi (saboda rashin wadatar zuci). Sa'an nan da wata fitina wadda ba za ta rage gidan wani Balarabe ba face ta shige shi. Sa'an nan zaman doya da manja (karamin sulhu) a tsakaninku da Turawa sai su rika yaudara, saboda su zo su yake ku bisa tuta tamanin. karkashin kowace tuta da kamar mayaka dubu goma sha biyu."

121. An karbo daga Abul Yaman ya ce: "Shu'aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Humaid dan Abdurrahman ya ba mu labari cewa: "Lallai Abu Huraira (RA) ya ce: "Abubakar ya sanya cikin wadanda ya aika domin su sanar a Ranar Layya a Mina cewa: Wani mushiriki ba zai sake Hajji ba bayan wannan shekara, kuma babu wanda zai sake Dawafi a tube (tsirara). Kuma Ranar Hajji Babba ita ce Ranar Layya, saboda fadar mutanen cewa: Akwai Karamin Hajji a ran nan Abubakar ya zartar da alkawarin kafiran amana a wannan shekara. Saboda haka babu wani mushiriki wanda ya yi Hajji a Hajjin Ban-Kwana lokacin da Annabi (SAW) ya yi Hajjin Ban-Kwana."

Babi na Talatin da Bakwai: Laifin wanda ya yi alkawari kuma ya yi yaudara. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: "Wadannan da suka yi alkawari, sa'an nan suka warware alkawarinsu cikin kowace shekara alhali su ba su takawa…." (K:8:56).

122. An karbo daga Kutaiba dan Sa'id ya ce: "Jarir ya ba mu labari daga A'amashi daga Abdullahi dan Murratu daga Masruk daga Abdullahi dan Amru (Allah Ya yarda da su), ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: "Abubuwa hudu wanda duk ya kasance cikinsu ya kasance tsantsan munafiki. Wanda idan ya yi magana zai yi karya. Idan ya yi wa'adi zai saba. Idan ya yi alkawari zai yi yaudara. Idan ya yi fada sai ya fajirce (ya rika fadin bakar magana ga abokin fadarsa saboda kada su shirya). Kuma duk wanda ke da daya daga cikin wadannan siffofi to yana da daya daga cikin siffofin munafinci har sai ya bar ta."

123. An karbo daga Muhammad dan Bashar ya ce: "Safiyan ya ba mu labari daga A'amashi daga Ibrahim Taimiyyu daga babansa daga Aliyu (Allah Ya yarda da shi), ya ce: "Ba mu rubuta komai daga Annabi (SAW) face Alkur'an da abin da ke cikin takardar nan. Annabi (SAW) ya ce: Garin Madina harami ce tun daga A'ir zuwa wuri kaza. Wanda duk ya farar da wani abu, ko ya taimaka ga dan bidi'ah to la'anar Allah tana kansa da ta mala'iku da mutane gaba daya. Ba za a karbar masa dukkan wani aiki ba, kuma alkawarin Musulmi daya ne mutum guda na tafiya da shi ga wadanda ba su nan. Wanda ya wulakanta wani Musulmi la'anar Allah tana kansa da ta mala'iku da mutane gaba daya. Ba za a karba masa dukkan wani aiki ba. Haka kuma wanda ya shugabanci wani al'amarin Musulmi ba tare da izinin shugabancinsu ba, to la'anar Allah tana kansa da ta mala'iku da mutane gaba daya. Ba za a karba masa dukkan wani aiki ba."

Kuma an karbo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: "Yaya halinku zai kasance idan ya zamo ba ku samun Dinari da Dirhami daga kafiran amana? Sai aka ce masa: "Yaushe kake tsammanin faruwar wannan ya Abu Huraira? Ya ce: "Eh, ina rantsuwa da wanda ran Abu Huraira ke hannunSa na fahimci haka ne daga fadar mai gaskiya abin gaskatawa (Annabi SAW). Sai suka ce, "Kamar yaya? Ya ce: ‘Za a rika tozarta amanar Allah da amanar Manzon Allah (SAW), sai Allah Ya kuntata bisa ga zukatan kafiran amana sai su hana abin da ke hannayensu (jiziya)."

Babi na Talatin da Takwas: Kamar yanda ya gabata:

124. An karbo daga Abdan ya ce: "Abu Hamza ya ba mu labari ya ce, na ji daga A'mashi ya ce: "Na tambayi Abu Wa'il shin ko ka halarci Yakin Siffin? Ya ce, "Na'am. Sai na ji Sahlu dan Hunaif yana cewa: "Ku zargi bin son ranku, saboda lallai na gan ni a ranar da Abu Jandal (ya zo cikin sarka, amma Annabi (SAW) ya mayar da shi zuwa ga wadanda ya kulla sulhu da su a Ranar Hudaibiyya), saboda haka ran nan da ina da ikon canja umurnin Annabi (SAW) da na musanya shi. Kuma ran nan ba mu aje takubbanmu bisa kafadunmu ba. Saboda abin da ke firgita mu, har sai da (Allah) Ya musanya mana zuwa ga al'amarin da muka fahimci shi ya fi abin da muke kai (na niyyar yakar abokan gaba)."

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai

Littafin bayanin yadda aka fara halittar mutum

Babi na farko:

Abin da ya zo cikin fadar Allah Madaukaki cewa: "Shi ne Wanda Ya fara halitta, sa'an nan Ya mayar da ita kuma haka Shi Ya fi masa sauki…" (K:30:27):

132. An karbo daga Muhammad dan Kasir ya ce: "Sufiyan ya ba mu labari daga Jami'u dan Shaddad daga Safawan dan Muhriz daga Imran dan Husain (Allah Ya yarda da shi), ya ce: "Wasu jama'a daga kabilar Tamin sun zo ga Annabi (SAW), sai ya ce: "Ya Bani Tamim ku yi farin ciki da wannan albishir! Sai suka ce: "Mun yi farin ciki, sai ka ba mu wani abu." Sai fuskarsa (ransa) ya baci, ana nan haka sai mutanen Yamen suka zo ya ce: "Mutanen Yamen ku karba mini wannan bushara, idan Banu Tamim sun ki karba mini." Sai suka ce, "Mun karba maka." sai Annabi (SAW) ya rika bayar da labari game da yadda aka fara halitta da Al'arshi. Sai wani mutum ya zo ya ce: Ya Imrana! Taguwarka ga ta can ta gudu, na ce kaicona! Kamar kada in tashi."

133. An karbo daga Umar dan Hafsu dan Ghiyas ya ce: "A'amashi ya ba mu labari Jami'u dan Shaddad ya ba mu labari daga Safawan dan Muhriz cewa: Lallai shi ya ba shi labari daga Imran dan Husain (Allah Ya yarda da su), ya ce: "Wata rana na shiga ga Annabi (SAW) na daure taguwata. Sai wadansu mutane daga kabilar Tamim suka zo, ya ce: "Ku karba mini wata bushara ya Bani Tamim! Sai suka ce: "Hakika ka riga ka ba mu bushara, yanzu dai ka ba mu wani abu (na dukiya) sau biyu." Sa'an nan wadansu jama'a daga mutanen Yamen suka shigo gare shi, sai ya ce: "Ku karba mini wannan bushara mutanen Yamen, idan Bani Tamim sun ki karba." Suka ce: "Mun karba maka ya Manzon Allah! Suka ce, "Mun zo domin mu tambaye ka game da wannan al'amari." Sai ya ce: "Allah Ya kasance lokacin da babu abin da ya kasance, Al'arshinSa na bisa ruwa. Ya rubuta dukkan komai cikin Littafi. Ya halitta sama da kasa." Ana cikin haka sai ya yi shelar cewa: Taguwarka ta kwance ta gudu ya Imran dan Husain, sai na tafi ban ga taguwar ba saboda kawalweniyar hanya (kyallin haske mai dauke ido). Ina rantsuwa da Allah na yi gurin da in kyale ta (taguwar) saboda labarin da (Annabi SAW yake gabatarwa). Darik dan Shihab ya ce: "Na ji Umar (Allah Ya yarda shi) yana cewa: "Wata rana Annabi (SAW) ya mike cikinmu a wani matsayi ya rika ba mu labari game da farkon halitta har shigar 'yan Aljanna masaukansu da shigar 'yan wuta masaukansu. Wanda ya haddace ya haddace, wanda ya manta kuma ya manta."

134. An karbo daga Abdullahi dan Abu Shaibah ya ce: "Daga Abu Ahmad ya karbo daga Sufiyan daga Abu Zinad daga A'araji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: "Allah Madaukaki Ya ce: "Dan Adam yana zagiNa kuma bai dace ba ya rika zagiNa. Kuma yana karyata Ni kuma bai dace ba ya rika karyata Ni. Amma zaginsa gare Ni, shi ne fadarsa cewa: Ina da da. Amma karyarsa gare Ni shi ne da yake cewa: Allah ba zai komo da ni ba kamar yadda Ya kaga halittata!"

135. An karbo daga Kutaiba dan Sa'id ya ce: "Mughira dan Abdurrahman Alkurashi ya ba mu labari daga Abu Zinad daga A'araji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: "Lokacin da Allah Ya kare halitta, sai Ya rubuta a cikin LittafinSa da ke wurinSa bisa Al'arshinSa cewa: "Lallai rahamaTa ta rinjayi fushiNa."

Babi na Talatin da Shida: Yadda ake zartar da alkawarin kafiran amana. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: "Ko dai ka ji tsoron wani ha'inci daga wadansu jama'a ka zartar musu da alkawari bisa daidai…."(K:8:58).
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 08 @ 22:59:25 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji

"Buhari da Muslim: Babi na Talatin da Biyu 114 - 124" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: