Muhawara Hausa
 



Buhari Da Muslim: Babi Na Hudu 140 - 142 & 148
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji Buhari Da Muslim: Babi Na Hudu 140 - 142 & 148

Tare da Sheikh Yunus Is'hak Almashgool, Bauchi

Yanda aka halitta taurari Kattada ya ce: Bisa faDar Allah MaDaukaki cewa: "Hakika Mun kawata saman duniya da taurari…(67:5)." Kuma dalilan halittar taurari ya kasu kashi uku: Na farko saboda kawata sama, na biyu saboda jifar sheDanun Aljnnu, na uku saboda shiryadda mutane da su. Wanda ya yi fassara fiye da haka to lallai ya yi kuskure ya tozarta rabonshi, kuma ya Dora wa kanshi Abin da bai sani ba." Saboda haka harba mutum zuwa taurari vata dukiya ne da karfi.

BABI NA HUDU:-

Siffar Rana da Wata bisa lissafi. Mujahid ya ce: Suna juyawa kamar mulmulin dunkuli. Wasu sun ce: "Suna kewaya bisa lissafi da masaukai wani bai ketaran wani. Kuma ana kiran jama'a da suna Husban: Kamar yadda ake faDar shihab da shuhban….har zuwa karshe duba littafin Tafsiri.

140. An karvo daga Muhammad DanYusuf ya ce: "Sufiyan ya ba mu labari daga A'mash daga Ibrahim Ataimi daga babansa daga Abu Dharri (Allah Ya yarda da shi), ya ce: "Annabi (SAW) ya ce wa Abu Darri lokacin da rana ta vuya: Shin ko kasan inda wan nan rana take zuwa? Na ce, "Allah da ManzonSa suka fi sani ya ce: "Lallai ita tana tafiya ne zuwa karkashin Al'arshi tayi sujuda, sai ta nemi izini sai ayi mata izinin. Kuma ya yi kusa in tayi suujuda ba za'a karvan mata ba. Kuma za ta nemi izinin, ba za'a yi mata izininba. Sai a ce mata: Ki koma in da kika fito, sai ta rika vulla in da take vuya. To wan nan shine fassarar faDar Allah MaDaukaki cewa: "Rana tana gudana ce ga matabbacinta wan nan shine kaddarawa Mabuwayi Masani. (36:38)."

Sa'an nan ya yi sallama alhali rana ta yi haske. Ya yi wa mutane huduba ya ce: "Game da khusufin rana da wata cewa: Lallai su ayoyi ne biyu daga ayoyin Allah, ba su rashin haske saboda mutuwar wani ko don haihuwarshi, amma idan kungansu haka ku gaugawa zuwa ga yin sallah."

141. An karvo daga Musaddad ya ce: "Abdul Aziz DanMukhtar ya ba mu labari ya ce, Abdullahi Danaji ya ba mu labari ya ce, "Abu Salmat DanAbdirrahman ya ba ni labari daga Abuhuraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: "Rana da Wata za'a tara su ranan kiyama."

142. An karvo daga Yahaya DanSulaiman ya ce: "DanWahab ya ba mu labari ya ce, Amru ya ba ni labari cewa: Lallai Abdurrahman DanAlkasim ya ba shi labari daga Abdullahi DanUmar (Allah Ya yarda da su),, cewa: Lallai shi ya kasance yana bayar da labari daga Annabi (SAW) ya ce: "Lallai Rana da Wata basu rashin haske saboda mutuwar wani ko saboda haihuwarshi. Amma su ayoyine (halitta) daga ayar Allah, idan kunga sun yi rashin haske to kuyi sallah."

Buhari da Muslim 148

148. An karbo daga Hudubat DanKhalid ya ce: "Hammam ya ba mu labari daga Kattada ya ce, Khalifa ya faDa mini, ya ce Yazid DanZurai'u ya ba mu labari ya ce, Sa'id da Hisham sun ba mu labari sun ce: Kattada ya ba mu labari ya ce, Anas DanMalik (Allah Ya yarda da shi), daga Malik DanSa'asa'ah (Allah Ya yarda da su), ya ce: "Annabi (SAW) ya ce, "Wata rana ina ga Dakin tsakanin mai barci da wanda ke farke sai ya mabaci wani mutum a tsakanin mutum biyu. Sai aka zo mini da wata tasa na zinari cike da hikima da imani. Sai aka tsaga kirjina zuwa tsakar ciki. Sa'an nan aka wanke da ruwan Zamzam, sa'an nan aka cika da hikima da imani. Aka zo mini da wata dabba fara ba takai alfadari ba kuma tafi jaki. Sai na tafi tare da Jibril, lokacin da na (muka) isa sama ta Daya, sai Jibrilu ya ce wa mai tsaron sama buDe: Sai ya ce, "Wanene? Aka ce, "Jibrilu ne, aka wake tare da kai? Aka ce, "Muhammad ne, aka ce, "Shin har an aika gare shi? Ya ce, "Na'am," sai aka maraba da shi, kuma madalla da Abin zuwan da yazo. Sai na tafi zuwa ga Adam na yi mashi sallama, sai ya ce: "Maraba da kai, Da Annabi," sai muka tafi zuwa sama ta biyu, aka ce, "Wanene? Ya ce, "Jibrilu ne, aka ce: Wake tare da kai? Ya ce, "Muhammad AS ne, aka ce, "Shin an aika gare shi? Ya ce, "Na'am, sai aka ce: Maraba da shi, madalla da Abin zuwa da yazo. Sai na tafi ga Isah da Yahya suka ce: "Maraba da kai, Danuwa Annabi." Sai muka tafi zuwa ga sama ta uku: Aka ce, "Wanene? Aka ce, "Jibrilu ne, aka ce: "Wake tare da kai? Ya ce, "Muhammad ne," ya ce: "Shin an aika gare shi? Ya ce, "Na'am, sai aka ce: "Maraba da shi, kuma madalla da Abin zuwa da yazo. Sai na tafi zuwa ga Yusuf na yi mashi sallama sai ya ce: "Maraba dakai Danuwa Annabi." Sai muka tafi sama ta huDu, aka ce: "Wanene? Ya ce: "Jibrilu ne, aka ce: "Wake tare da kai? Ya ce, "Muhammad AS ne, aka ce: "Shin an aika zuwa gare shi? Ya ce, "Na'am, aka ce: "Maraba da shi, madalla da Abin zuwa da yazo. Sai na tafi ga Idris nayi masa sallama ya ce: "Maraba da Danuwa Annabi." Sai muka tafi sama ta biyar, aka ce: "Wanene? Aka ce, "Jibrilu ne, aka ce: "Wake tare da kai? Aka ce: "Muhammad ne," aka ce: "Shin an aika zuwa gare shi? Ya ce: "Na'am, aka ce: "Maraba da shi, madalla da Abin zuwa da yazo. Sai muka tafi ga Haruma nayi sallama ya ce: "Maraba da Danuwa Annabi," sai muka tafi zuwa sama ta shida. Aka ce: "Wanene? Aka ce: "Jibrilu ne, aka ce: "Wake tare da kai? Aka ce: "Muhammad AS ne, aka ce: "Shin an aika zuwa gare shi? Maraba da shi, madalla da Abin zuwa da yazo, sai na tafi zuwa ga Musa nayi mashi sallama. Sai ya ce: "Maraba da kai, Danuwa Annabi." Lokacin da na shuDe sai ya rika kuka, aka ce, "Me ya sanya ka kuka? Ya ce: "Ya Allah wan nan saurayi wanda aka aiko a bayana, jama'arsa zasu shiga Aljanna fiye da tawa jama'ar." Sai muka tafi zuwa sama ta bakwai, aka ce: "Wanene? Aka ce: Jibrilu ne, aka ce: "Wake tare da kai? Aka ce: "Muhammad ne, aka ce: "Shin har an aika gare shi? Marabada da shi, madalla da Abin zuwa da yazo. Sai na tafi zuwa ga Ibrahim na yi mashi sallama. Ya ce: "Maraba da kai Da Annabi," sai aka Daukaka mini Baitul Ma'amur na tambayi Jibrilu ya ce: "Baitul Ma'amur ke nan, kowa ce rana mala'iku dubu saba'in ke sallah, idan sun fita basu komowa karshen aikinda ke kansu kenan. Sai aka nuna mini Sidratul Muntaha (itacen mgaryar tukewa da ke sama ta bakwai). Sai na iske ‘yan ‘yan ta kamar tulunan Hajar, ganyenta kamar kunnuwar giwaye, akarkashinta akwai koramai huDu: koramai biyu boyayyu, da wasu koramai biyu bayyanannu. Sai na tambayi Jibrilu ya ce: "koramai biyun nan na cikin Aljanna ne. Amma biyu da suke bayyane, Nilu da Furat ne. Sa'an nan aka farlanta salloli hamsin. Na juyo har sai da nazo ga Musa AS ya ce: "Me ka karba? Na ce, "An farlanta mini salloli hamsin." Ya ce, "Ni nafi ka sanin mutane, na zauna da Bani Isra'il na samu wahala mai tsanani saboda su. Kuma lallai al'ummarka ba zasu iya aikata haka ba. Ka koma zuwa ga Babangijinka ka roke shi sauki. Sai na koma na roke shi, ya mayarda ita arba'in. Sa'an nan na koma (ga Musa ya faDa mini kamar haka) na koma aka rage ta zamo talatin. Sa'an nan na koma kamar haka aka rage ta zamo Ashirin. Sa'an nan na koma kamar haka aka rage ta zamo goma. Na koma ga Musa ya faDa mini kamar haka, sai aka sanya ta zamo biyar. Na tafi ga Musa ya ce: "Nawa aka rage? Na ce, "An sanya ta ta zamo biyar," ya sake faDa mini kamar haka, sai na ce: "Na mika wuya ta ga Allah bisa ga wan nan, daga nan sai aka kira Annabi (SAW) da cewa: "Na riga na zartarda Abin da na farlanta shi kuma na saukaka ga bayina. Kuma zan saka ga kowa ce Daya mai kyau da lada goma."

 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 08 @ 23:02:31 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji



"Buhari Da Muslim: Babi Na Hudu 140 - 142 & 148" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com