Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin
[ Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin ]

·It's Haram To Aid, Promote Or Participate In The Oodua Nation Agitation
·Tauhidi ginshikin Musulunci (5)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (4)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (2) - (3)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (1)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (4)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (3)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (1)
·Darussa daga Hadisin Matafiya Uku

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Adabin Gargajiya
 
 
Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai Adabin Gargajiya

By Faruk Tahir Maigari

Tun asali a ƙasar Hausa, akwai hanyoyi da Hausawa ke bi wajen gudanar da rayuwarsu da kuma isar da saƙonni ta kowace fuska kama daga karantarwa da zaburarwa, da nishaɗantarwa da gargaɗi da sauransu. Dukkan waɗannan abubuwa akan yi su ne a gargajiyance da baki. Misali, a kan bi hanyar waƙa wajen zaburar da mutum kamar mafarauta, 'yan dambe da sauransu. Haka akan bi hanyar tatsuniya wajen koya wa yara kyawawan ɗabi'u ta hanyar labaran tatsuniyar.

Saboda haka wannan tsohuwar hanya, ta karantarwa da sauransu da baki ake yin ta, ba a rubuce ba. Don haka ne masana suka kira ta Adabin Gargajiya.

Aminiya ta yi waiwaye a kan adabin gargajiya domin kalato wadansu bayanai daga masana domin amfanar mai karatu da kuma daliban ilimi. A kan kira wannan rubutu dake tafe Adabin Gargajiya kuma a kan kira shi da Adabin Baka.

Aminiya ta yi wannan waiwaye ne domin dora masu karatu a kan yadda duk lokacin da za su yi karatu su fahimci fagen da suke karantawa.

Ma'anar Adabin Gargajiya

Farfesa Ɗangambo (1984), ya ce, "Adabin Gargajiya, shi ne Adabin da Hausawa suka gada daga kaka da kakanni". Amma Yahaya, Zariya, Gusau, da 'Yar'aduwa (1992), sun kalle shi a matsayin nau'in Adabi da ke ɗauke da zantuttuka gajeru ko dogaye na hikima waɗanda ke koyar da wasu darrusa.

Ke nan, Adabin Baka ko Adabin Gargajiya, Adabi ne da yake wanzuwa ta hanyar magana; da baki ake isar da shi haka nan a taskace shi. Babbar hanyar isar da shi ita ce kunne ya girmi kaka. Idan ana son nazartar rawuyar Bahaushe ta wannan sigar sai a duba abubuwan da ke ƙunshe cikin wannan buhu na Adabin Baka. Yana da rassa ko rabe-rabe.

Rassan Adabin Gargajiya

Adabin Baka yana da ajujuwa ko rassa da dama, Farfesa Ɗangambo (1984), ya karkasa shi a dunƙule kamar haka:

Tatsuniyoyi da Labarai.

Almara da Wasa Kwaƙwalwa.

Ƙissa da Hikaya.

Waƙoƙi da Kaɗe-Kaɗe.

Su kuwa Yahaya, Zariya, Gusau, da 'Yar'aduwa (1992), sai suka karkasa shi kamar haka:

Zube: Ya ƙunshi Tastuniya, Almara, Hikaya, Kissa, Tarihi, Tarihihi, Labari, Barkwanci da sauransu.

Waƙa: Ta ƙunshi waƙoƙin baka, kaɗe-kaɗe, bushe-bushe, tumasanci, roƙon baka da sauransu.

Azancin magana: Ya ƙunshi Karin Magana, Salon Magana, Kacici-Kacici, Zaurance, Karya Harshe/Karangiya, Waskiya, Baƙar Magana, Ba'a, Zambo, Sara, Kirari da sauransu.

Bayan waɗannan rabe-rabe da muka gani daga waɗannan fuskoki guda biyu, haka kuma abubuwan da suka shafi sana'o'i, al'adu, bukukuwa da sauransu, su ma suna cikin wannan aji na Adabin Gargajiya ko Adabin Baka.

Amfanin Adabin Gargajiya

Koyar da tarbiyya: Adabin Baka hanya ce da kaka da kakanni ke amfani da ita wajen koya wa yara tarbiyya cikin hikima ta hanyar magana ko dai kai-tsaye ko kuma cikin labari.

Taskace al'adu: Ta hanyar Adabin Baka Bahaushe yake taskace al'adun gargajiya.

Fito da yanayin zamantakewa: Ta hanyar Adabin Gargajiya Bahaushe yake sanar da jama'a yadda yanayin zamantakewarsa yake.

Koyar da Fasaha da kuma Taskace ta: Ta hanyar Adabin Gargajiya na gaba suke koyar da na baya irin fasahar da Allah Ya hore musu, kamar idan muka duba yanayin zamantakewar Bahaushe za mu ga a cike take da darrusa a kowane lokaci kuma a ko'ina za ka ga yara suna ɗamfare da manya suna koyon abubuwa.

Taskace tarihi da yaɗa shi: Ta hanyar Adabin Gargajiya ne al'ummar Hausa take isar da tarihinta, musamman ta hanyar nan da aka fi sani da kunne ya girmi kaka.

Nishaɗantarwa: Ta hanyar Adabin Gargajiya Bahaushe yake nishadantar da kansa. Waƙoƙi, tatsuniya, kaɗa-kaɗe, barkwanci, wasanni da bukubuwa da sauransu, dukkan waɗannan suna daga cikin hanyoyin da Bahaushe yake bi yana nishaɗantar da kansa ko dai a lokutan bukukuwa ko kuma a lokacin zama haka kawai.

An ciro wani sashi na rubutun nan daga shafin Intanet na searchworks.stanford.edu
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 08 @ 23:18:34 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· EsinIslam Turanci Kusa
· Fiye Da Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai:
MARTANI: Yadda rikicin Izala da darika ya kasance a Sabo Ibadan: Kwan-gaba kwan-


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

"Adabin Gargajiya" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: