Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
[ Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi ]

·Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani
·Wani abu kan Sallar Idi
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)
·Sallar Idi da ladubbanta
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
·Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
·Babu Masu Kashe Masu Jefa Kuri'a A Ranar Zabe Sai Azzalumai

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
 
 
Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu

Hoton Bakan-Gizo

Allah cikin ikonSa Ya yi halittu iri daban-daban, wasu ana ganinsu wasu kuma, sun fi karfin mutum ya gansu. Daga cikin wadanda ba a iya gani da ido akwai iskokai/aljanu da mala'iku da abubuwan da dan Adam ke amfani da su irin iskar da ake shaka da yunwar da ke damunsa da sauransu. Malam Maharazu Barmu Kwasare ya taskace tarihin wani bakan-gizo da ya yi sanadiyyar mutuwar wadansu mutum shida da suka tarar da shi a cikin rijiya ba tare da sun san yana ciki ba. Al'amarin ya faru a 1396 Bayan Hijira wadda ta yi daidai da 1975 Miladiyya, kuma lokacin Malam Maharazu na da shekara 59 a duniya. Ya sanya wa wakar suna "Wakar Jinni Sago". Malam Maharazu ya kira sagon da jinni domin ba a ganinsa. Halittar da ba a gani kuwa, ga Bahaushe ko dai mala'ika ko kuma aljani. Idan aka samu wadanda ba su ba kuma ba a ganinsu, to mai yuwuwa ne suna tare da aljanu.

Sago na da sunaye daban-daban da ake kiransa da su. Wannan bambancin sunayen ya jibinci wurare da al'ummar da ke zaune a can. Wadansu mutane na kiransa sago wadansu kuma, bakan-gizo suke kiransa. Akwai masu kiransa zunni wadansu kuma, masha-ruwa suka fi saninsa da shi.

A wancan shekara ce jama'ar Unguwar Rungumi da ke cikin garin Sakkwato suka himmatu domin gyara wata tsohuwar rijiya don magance karancin ruwan sha. Duk kokarin da suke yi na hada aikin gayya a gyara rijiyar babu wanda ya san akwai bakan-gizon a cikinta. Da sun sani da ba su shiga ciki ba amma da yake Allah Ya kaddaro musu wannan lamari, babu mahani ga faruwarsa. Domin tabbatar da wurin da abin ya faru, ga abin da Malam Maharazu ya ce:

Shiyya ta Rungumi can marina wajen kwalta,

Jabbaru Ya kaddaro musu waki'a har da sago.

A lokacin da za a gyara rijiyar mutane sun taru sosai domin gudanar da aikin. Ga al'ada aikin gayya ba a barin mutum daya da aiki ko shi kadai ne gwani sai dai a hada shi da masu taimaka masa domin aiki ya gudana da sauri yadda ake bukata. Ana haka sai wadansu mutum biyar suka shiga rijiyar daya bayan daya. Saukarsu cikin rijiyar ke da wuya sai sagon (aljanin) ya fara cutar da su ta hanyar sake musu zafin da aka ce yana da shi. Domin tabbatar da haka, ga abin da Malam Maharazu Kwasare ya ce:

Sago maciji na kuma aljani dai na,

Sago wuta na zama zafi ga jinni sago.

Baitin da aka kawo ya tabbatar da cewa, bakan-gizo aljani ne domin ba a ganinsa balle a san yana wuri. Abin da ke sanya a gane yana wuri kawai shi ne idan aka ga barna irin wadda ya saba yi ta faru da kuma sauran alamomin da ke nuna shi ne kamar tarar da matsanancin zafi a wurin da yake zaune. Akan gane haka domin jama'a sun san kowane abin halitta da aikin da yake yi musamman shi da aka san wurin zamansa ba su zarce rami da kogo da bigar rijiya ba. A kan haka ga abin da Malam Maharazu ya ce:

Kogo da rame da biga har kurunguruma,

Ga Rabbana suke har bisa rijiya da sago.

Wata alama da ke nuna alamun akwai sago a cikin rijiya ita ce, a ga duk gyaran da ake yi wa rijiyar domin a samu ruwa sai ruwan ya gagara samuwa kuma, ko an samu ba ya wadatarwa har a gaji a fita batunta a yi wata. Duk rijiyar da ke da wannan siffa, ana kyautata zaton akwai masha-ruwa a ciki. Masu aikin gina da gyaran rijiya sun san da haka kuma, mafi yawa daga gare su ake jin wadannan asirrai na rijiyoyin da ba su aminta da su ba saboda wani abu da suka ji ko suka gani ciki lokacin da suka shiga.

Dangane da al'amarin da ya faru cikin wannan rijiya Malam Maharazu ya ce mutane na fadar maganganu iri-iri dangane da barnar da masha-ruwan ya yi. Daga cikin maganganun da ake fadi ga abin da Maharazu ya ce:

Kila wa kala akwai su kwarai ga annasu,

Komi suka yi bisa kaddara ga sago.

Batutuwa ba mu bin su irin na ashararu,

Mu dai tsrin Allah muka so ga jinni sago.

Bisa kaddarowar Allah da babu mahani gare ta, sai mutanen biyar da suka shiga rijiyar. Nan take zunnin ya bayyana gare su ya sake musu zafi wanda ba ya da iyaka da ya fi karfin su iya fitowa kai-tsaye. Nan take mutanen suka mutu baki dayansu. A kan haka, ga abin da Malam Maharazu Kwasare ya fada:

Mutum biyar Jalla Yay yi kira cikin sa'a,

Guda hukuncin Ilahi Rabban ga sago.

Da aka tabbatar da mutuwar mutanen, sai aka shiga shawarar yadda za a fito da su domin yi musu sutura. A cikin kowane lamari akwai wadanda Allah Ya hore wa tambaya ko lakani ko magani ko gwargwado na wasu matsaloli. A nan aka samu wani mutum daya da ya shiga domin ya fito da su. Da tambayarsa da komai da yake shi ma lokacinsa ya yi, ya ci nasarar fitowa da mutane, amma kwana daya ne tskaninsa da su ga kai makabarta kamar yadda Malam Maharazu ya tabbatar da labarin inda ya ce:

Na shidda wannan da yaz zo don shi tsamo su,

Wanshekare yab bi su bayan gamo da sago.

Bisa bayanin Maharazu ana iya fahimtar cewa, mutum na shida ya ci nasarar fitar da muum biyar daga cikin rijiyar sai dai, shi ma bai tsira ba. Wato bayan ya fitar da su wannan rana aka yi musu jana'iza, shi kuma washegari ya rasu aka yi masa jana'iza kamar yadda aka yi ta wadancan da suka gabace shi da kwana daya. Malam Maharazu ya yi ta'aziyyar mutanen tare da roka musu gafarar Allah kamar haka:

Allah Shi gafarta musu don uban Bello,

Shi saukake musu barzahu kan sago.

Su san jawabin Nakiri da Munkaran zak kyau,

Fa ba tsawattai balle a ce su buga.

Malam ya bayyana cewa, jinni sago ba kamar sauran namun daji yake ba da mutane ke iya korewa daga wurin da yake. Hasali ma, ba a sanin yana wuri sai ya yi aika-aika. A nan, Malam Maharazu na nufin cewa, sago ba irin barewa da damisa ko zaki ko zomo ko kura da sauransu ba ne da ko kuwwa aka yi musu suna iya tashi (gudu) daga wurin da aka gan su su koma wani wuri na daban. Ga abin da Malam Maharazu Kwasare ya fada dangane da haka:

Namu na daji ana kuwwa a tashe su,

Ko an yi taro da kuwwa ba a ta da sago.

An san cewa ba a ganin aljani ido-da-ido face idan sun rikida zuwa wata siffa ta daban. Ai ko Hausawa cewa suka yi:

"Kowa ya ga aljani bai kwana."

Sanadiyyar rasuwar wadannan mutum shida, Malam ya yi addu'o'i daban-daban tare da rokon Allah Ya tayar da sagon ya bar wannan rijiya. Ya roki Allah da surorin Alkur'ani Mai girma da wasu ayoyi da ke cikinsa a wurare da yawa a cikin wakar. Ga misali kamar haka:

Albarkacin wa'alamu har duk da ya ayyu,

Albarkacin innamallahu Ka ta da sago.

Albarkacin wa'ila Madyana da waman,

Ubarri'u Jalla mun roka Ka ta da sago.

Wannan al'amari ne mai girman gaske da tashin hankali da ya faru da ke tabbatar da tarihi a cikin wakokin Malam Maharazu Barmu Kwasare, da fatan Allah Ya sanyaya wa wadannan mutane tare da mu baki daya, amin.

Mun samu sharhin wakar Bakan-gizo daga mai lamba

0703 5141 980.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 08 @ 23:30:11 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· EsinIslam Turanci Kusa
· Fiye Da Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai:
MARTANI: Yadda rikicin Izala da darika ya kasance a Sabo Ibadan: Kwan-gaba kwan-


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

"Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: