Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
[ Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen ]

·Illolin zina da luwadi da madigo (1)
·Layya da hukunce-hukuncenta
·Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
·Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
·Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
·Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
·Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
·Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
·Menene Hunkunci Azumtar Watan Rajab??

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
 
 
Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi Kyauta da kyauta – yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni'imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya sanya yin kyauta da kyauta-yi cikin kyawawan dabi'un Musulmi. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma ya koyar da cewa kyauta da kyauta-yi ba ta rage dukiya; Amincin Allah Ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur'ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu, (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al'amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

Bayan haka, mun yi tsokaci mai tsawo dangane da nuni kan kyauta cikin kyauta-yi tare da kawo misalai masu yawa da manuniya kan muhimmancin wannan dabi'a daga Hadisan Ma'aikin Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya isa ga mai hankali da lura ya kama aiki. Allah Ya kara mana taimakonSa. Yau, in Allah Ya so, za mu kammala mukalar daga cewa:

Babu shakka shi Musulunci yana haska sadaka ne da kyauta cikin kyauta-yi a wani yanayi da yake haifar da gwaggwabar ladar da take mafi girma a bangarensa, kamar dai yadda aka fitar a wani Hadisi daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa, "Wani mutum ya zo wajen Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, "Ya Ma'aikin Allah, wace irin sadaka ce ta fi?" Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, "Wadda ka bayar a lokacin da kake lafiyayye, kana kankame da dukiya (wato kana tsumulmularta), kana tsoron talauci, kana sa ran zama attajiri! (ita ta fi). Kada ka yi jinkiri har sai ka kusa mutuwa ka rika cewa, "Wannan a kai wa wane da wane; waccan a kai wa wane da wane." Alhali ta kai lokacin da ta zama dukiyar wane da wane!" Buhari da Muslim ne suka ruwaito Hadisin. Wato -Allah Shi ne Mafi sani-, manufa kada a bari dukiya ta kai matsayin ta magada, domin mai ita ya kai gargarar mutuwa.

Musulmi na gaskiya, mai kyauta, shi ne yake bayar da sadaka (ko kyauta) musamman ga wadanda suke da bukatarta. Yakan duba a cikin matalauta da mabukata wadanda suke wadatuwa wajen su roki wani abu daga wajen kowa, ta yadda mafi yawan mutane sai su yi zaton ba su ma da bukata. Yakan je wajen irin wadannan mutane, ya iske su har gida ya ba su abin da zai ishe su biyan bukatarsu ta yau, ta yadda za su kange mutuncinsu. Irin wadannan mutane kuwa su ne na farko da za a je a ba su taimako. Su ne kuwa wadanda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce game da su, "(Ainihin) mabukaci (matalauci) ba shi ne wanda yake (roko kuma yana) karbar dan wani abu shi ke nan ya juya ya tafi ba, a'a, mabukaci shi ne wanda ba ya da shi, ba ya da abin biyan bukatar kansa, amma ya kame daga tambayar (rokon) mutane, saboda ya tsare mutuncinsa." Buhari da Muslim ne suke fitar da wannan Hadisin.

Musulmi na gaskiya, mai kyauta, shi ne yake bayar da sadaka (ko kyauta) ga maraya. Ya dauki nauyinsa, har zuwa lokacin da ya kai matsayin ya nemi na kansa, kuma ba ya damuwa ko bambancewa tsakanin marayan da yake da dangantaka da shi da wanda ba danginsa ba. Yana yin wannan aikin alherin ne da tunanin samun abin da wanda ya dauki nauyin maraya yake samu, wanda yake matsayi mai girma da daraja da za a iya saida rai ma don a same shi. Wannan kuwa matsayi ne na kasancewa tare da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a Aljannah, kamar yadda Imam Muslim ya ruwaito Hadisi daga Sahlu dan Sa'ad, (Allah Ya yarda da shi), cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, "Ni da wanda ya dauki nauyin maraya, za mu kasance kamar haka a Aljanna," sai ya nuna dan yatsarsa (dan-ali) da na tsakiya, ya wara su."

Musulmi na gaskiya mai kyauta cikin kyauta-yi, shi ne yake bayar da sadaka (ko kyauta), ga wadda ta rasa mijinta (bazawara) da kuma matalauci, saboda yana bin shiryarwar addininsa, yana neman yardar Ubangijinsa, yana kwadayin ladar da Allah Ya tanada wa masu irin wannan aikin alheri.

Shi irin wannan aiki na tallafa wa wadda ta rasa mijinta da matalauta yana da ladar da ta kai ta yin azumin nafila da tsayuwar dare da kuma jihadi saboda daukaka kalmar Allah. Wannan lamari kuwa ya biyo bayan abin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, "Duk wanda ya mayar da hankali wajen daukar nauyin zawarawa da matalauta, to kamar wanda yake jihadi ne wajen daukaka kalmar Allah." Mai ruwaya ya ce, ina da tabbacin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, "Haka nan ya yi kamar wanda ya tsayu cikin dare yana Sallah ba gajiyawa da kuma wanda ya dinga azumi ba kakkautawa." Buhari da Muslim ne suka fitar da Hadisin.

Wadannan fuskoki da aka zayyana tun farkon wannan mukala, su ne wuraren da Musulmi mai kyauta cikin kyauta-yi zai rika bayar da dukiyarsa domin kwadayin samun kwanciyar hankali da natsuwar zuciya da faraga da kuma lada daga Allah.

Wadannan duk halaye ne da za su kusantar da bawa ga Ubangijinsa. Sannan ko kusa kada masu dukiya su yi zaton za su samu komai a cikin abin da suke kashewa wajen sharholiyar bayar da ci da sha ga jama'a da watsa kudi don kawai su nuna su, su ne, ko kuma don samun biyan wata bukata ta zukatansu. Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi tir da duk wata ciyarwar da ake yi ba don Allah ba, inda ya ce, "Tir da walimar da mawadata kadai ake gayyata, alhali ana kore matalauta daga gare ta." Buhari da Muslim suka fitar da Hadisin.

A karshe, ana kara jan hankalin Musulmi ya gane cewa mayar da hankali wajen taimakon matan da suka rasa mazajensu da matalauta da daukar nauyin marayu, ba kawai yana samar da gwaggwabar lada ba ne, a'a, har ma yana wanke zuciya; ya kara kyautata zamantakewa; ya tausasa zukata; ya sa a more gardin kyauta cikin kyauta-yi; ya karsasa yin ayyukan alheri cikin nishadi da annashuwa. Shi ya sa ma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yakan zaburar da masu kuncin rai da zafin zuciya, su rika kyauta da ayyukan kyauta-yi, ta yadda zukatan nasu za su yi taushi su cika da rangwame.

Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ba da labarin cewa wani mutum ya kai kukan tsaurin zuciyarsa ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai ya ce masa, "Ka (rika) shafa kan maraya, kuma ka rika ciyar da matalauta." Imam Ahmad ne ya fitar da Hadisin kuma mazajen Hadisin ingantattu ne.

Da wannan muka zo karshen wannan mukala ta kyauta cikin kyauta-yi, tare da fatan daidai din da ke ciki, Allah Ya ba mu ladarsa, kuskure kuma Allah Ya gafarta mana, amin!

Wassalamu alaikum warahamatullahi wabarakatuh.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Monday, September 09 @ 00:18:20 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi:
Bayyanar mata masu neman mata a kasar Hausa


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

"Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: