Muhawara Hausa
 



Illolin zina da luwadi da madigo (1)
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen Illolin zina da luwadi da madigo (1)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin Manzanni, Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam) tare da alayensa da sahabbansa. Bayan haka, wannan tsokaci ne a kan ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncin kowanensu a karkashin shari'ar Musulunci da Dokta Muhammad Rabi'u Umar Rijiyar Lemo ya rubuto kuma muka ga ya dace a sanya a wannan fili don amfanin jama'a. Ina rokon Allah Ya sa abin ya yi tasiri a kan kowane Musulmi. Bismillah!

Ma'anar zina da hukuncinta:

Lafazin zina a shari'ance yana nufin saduwa da mace ba tare da an yi aure, ko an mallake ta a matsayin baiwa ba. Sai dai akan yi amfani da lafazin zina a kan abin da bai kai saduwa ba, kamar yadda ya zo a Hadisin Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ) ya ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "An rubuta wa dan Adam rabonsa na zina, babu makawa sai ya same shi, zinar idanu ita ce gani, zinar kunnuwa ita ce ji, zinar harshe ita ce magana, zinar hannu ita ce damka, zinar kafa ita ce taku, zuciya kuwa tana kwadayi tana fata, farji kuma shi yake gaskata haka ko ya karyata." Muslim.

A cikin wannan Hadisi za mu ga yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya nuna cewa kowane dan Adam an rubuta masa rabonsa na zina, kuma zai samu wannan rabo babu makawa, sai dai ba za a kama shi da laifi ba, har sai idan ya gaskata abin da idonsa ko kunnensa ko hannunsa ko kafarsa suka jiyar da shi, ta hanyar yin amfani da farjinsa don biyan bukatar wadannan gabbai. Wannan shi ne ma'anar fadin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a karshen Hadisin, "farji shi yake gaskata haka ko ya karyata." (Sharhin Sahih Muslim na Imam Nawawi Juz'i na 16, shafi na 216).

Hukuncin zina:

Zina haramun ce a addinin Musulunci. Allah Madaukakin Sarki Ya haramta ta inda Yake cewa : "Kada ku kusanci zina, domin ita alfasha ce kuma tafarki ne mummuna." (Isra'i:32).

Malamai suna cewa, fadin Allah "kada ku kusanci zina," kai matuka ne wajen hana ta, don ya fi a ce "kada ku yi zina."

Sheikh Abdur-Rahman Assa'idiy yana cewa: "Hani ga a kusanci zina ya fi kai matuka a kan hana yin ta, saboda cewa kada a kusance ta ya hada hana dukkan yin abubuwan da suke gabatar ta kuma suke kawo yin ta, domin kuwa duk wanda ya yi kiwo a gefen shinge, to ko yana daf da fadawa cikinsa, musamman ma a kan irin wannan lamari, wanda da yawa daga cikin zukata suna dauke da abin da yake sawa a afka masa. Sannan Allah Ya siffata zina da cewa alfasha ce. Ma'ana zina wata aba ce da shari'a da hankali suke ganin muninta, saboda keta alfarmar Ubangiji ce da shiga hakkin macen da hakkin danginta da mijinta, kuma bata wa miji shimfidarsa ne da cakuda dangantaka da makamancin haka." (Tafsirin Assa'idiy).

A wani wurin a cikin Alkur'ani Mai girma, Allah Madaukakin Sarki Ya siffata bayinSa muminai da cewa su ne wadanda ba sa zina, inda Ya ce, "Wadanda ba sa kira ko bauta wa wani tare da Allah; ba sa kashe rai da Allah Ya haramta sai da hakki; kuma ba sa zina, duk wanda ya aikata haka zai gamu da azaba." (Alfurkan: 78).

Ya tabbata a cikin Hadisi an tambayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) a kan wane zunubi ne ya fi girma, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, "Shirka da Allah alhali Shi ne Ya halicce ka." Sai aka ce, ‘sai wanne?' Sai ya ce, "Sannan kashe danka don kada ya ci tare da kai." Sai aka ce, ‘Sannan sai wanne?' Sai ya ce, "Ka yi zina da matar makwabcinka." (Buhari).

Allah Madaukakin Sarki Ya sanya hukuncin wanda duk ya yi zina kuma ya taba aure, a jefe shi, namiji ko mace; idan kuwa bai taba aure ba, sai a yi masa bulala dari, sannan a bakuntar da shi a wani gari daban tsawon shekara guda (ma'ana a daure shi a kurkuku).

Duk wanda ya kalli hukuncin zina, zai ga Allah Ya kebance shi da wasu abubuwa masu yawa, saboda munin zina. Ga kadan daga cikin abubuwan da hukuncin ya kunsa:

• Kausasawa wajen ukubar mazinaci, ta hanyar jefewa. Ko kuma bulala da bakuntarwa shekara guda.

• Hana jin tausayin mazinaci ko mazinaciya yayin da ake musu ukuba. Allah Ya ce: "Mazinaciya da mazinaci ku yi wa kowane daya daga cikinsu bulala dari. Kada ku ji tausayinsu a cikin addinin Allah, in dai kun yi imani da Allah da Ranar karshe." (Annur:2).

• Yi musu ukuba a gaban mutane. Ba a yarda a yi musu a boye ba. Allah Ya ce: "Wasu bangare na muminai su halarci wajen yi musu ukuba (haddi)." (Annur:2).

Duk wadannan abubuwa suna nuna mana munin zina da rashin kyanta a Musulunci. Imam Buhari ya kawo a cikin ingantaccen littafinsa daga Maimun Al'audiy ya ce, "A lokacin Jahiliyya na taba ganin wani biri da ya yi zina da wata biranya, sai sauran biran suka taru suka jefe su."

Mafi munin zina ita ce wadda mutum zai yi da mahaifiyarsa; sai da muharramarsa; sai wadda zai yi da mata (ko 'yar) makwabcinsa. Allah Ya kare mu.
Illolin zina:

Babu ko shakka duk mai hankali ya san cewa zina tana tattare da illoli masu yawa, wadanda suke shafar mazinacin ko mazinaciyar, ko su shafi al'umma gaba daya. Ga wasu daga cikin illolinta:

1. Zubar da mutunci da jawo wa kai kaskanci: Duk matar da ta yi zina, to ta jawo wa kanta da danginta da mijinta kaskanci, ta kuma zubar musu da mutunci a idon duniya. Idan har ta samu ciki ta haihu, sannan ta kashe dan, to ta hada laifi biyu, laifin zina da laifin kisan kai. In kuma ta bar shi, to kuma ta shigar wa mijinta ko danginta, wanda ba ya cikinsu. Idan kuwa mai zinar namiji ne, to ya lalata mace, ya jawo mata lalacewa da tabewa, wanda hakan lalata duniya ne gaba daya.

2. Zina ta hada dukkan sharri gaba daya: Saboda a cikin zina akwai rashin tsoron Allah; rashin kunya; rashin tsantseni; rashin cika alkawari; karya da butulci da sauransu. Duk kuwa wadannan munanan halaye ne a Musulunci.

3. Zina tana haifar da cututtuka da mutuwar zuciya da sanya zuciya ta zama bakik-kirin da samun kai cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali da nutsuwa a koyaushe. Bincike ya tabbatar da cewa cutar kanjamau ta fi yaduwa ta hanyar zina fiye da kowace hanya da ake iya daukar cutar daga gare ta, sannan ta hanyar cutar akan kamu da miyagun cututtuka masu mugun hadari.

4. Zina tana haifar da talauci da musiba a bayan kasa, saboda da duk namijin da yake mazinaci, to ba ya iya tattali, kullum kudinsa suna wajen matan banza, duk abin da zai samu, ba zai amfanu da shi ba yadda ya dace, a banza zai tafi. Haka nan duk matar da take mazinaciya ce, duk abin da ta samu yana karewa ne wajen yadda za ta janyo hankalin maza zuwa gare ta, Allah kuma Zai zare wa dukiyarta albarka.

Mu kwana nan!

Sheikh Muhammadu Rabi'u Umar Rijiyar Lemo, Kano
Imel: Gatafa75@yahoo.com

 Posted By Aka Sanya A Monday, September 09 @ 01:55:07 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen



"Illolin zina da luwadi da madigo (1)" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com