Muhawara Hausa
 



Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al'umma 08
 
Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc Daga Salihu Is'hak Makera

Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al'umma 08

Don haka giya ko kwaya ko wiwi ko solisho ko duk wani abu mai sanya maye yana daga cikin manyan abubuwan da ke yin ta'addanci ga lalurori biyar da shari'ar Musulunci ta zo domin kare su. Da yawa abubwan sanya maye kan haifar da zubar da jinin da shari'a ta haramta, su haifar da keta mutuncin da lalata dukiya da bata kwakwalen jama'a da ruguza martabar addini. Kuma abin da ke sabbaba haka shi ne gushewar hankali, wanda shi ne ya kamata ya jagoranci mutum zuwa ga ingantuwarsa. (A duba Makasidus Shari'a wa Alakatiha bi Adillatis Shari'iyya, shafi na 223- 229). 

b. Masu bata hankali na ma'anawi:

Masu bata hankali na ma'anawi ko mu ce na boye, su ne abubuwan da suke shiga hankali na daga tasawware-tasawware da tunane-tunane na fasadi ya alla a ciki addini ne ko rayyuwar jama'a ko siyasa ko waninsu na daga abubuwan jin dadin rayyuwa. Wadannan abubuwa suna bata hankula ne ta hanyar sanya hankalin mutum ya gushe, ya rasa tunani mai kyau da ya dace da shari'a. A irin wannan hali hankalinsa zai kazance, ta yadda zai zama batacce da ba ya iya tunani da shi, ko ma a ce ya rasa shi kacokan a wannan lokaci.

Don haka ne Allah Ya yi misali da kafirai a cikin LittafinSa saboda sun rasa hankalin da za su yi tunani a cikin ayoyin Allah na Alkur'ani da na halitta, sai ya zamo hankalin da suke da shi ya kasa jagorantarsu zuwa ga gaskiya. Allah Madaukaki Ya ce: ''Ko kana zato cewa, mafi yawansu suna ji, ko kuwa suna da hankali? Su ba su zama ba face kamar dabbobin gida suke, a'a su ne mafi bacewa ga hanya.'' (k:25:44).

Ibnu Sa'adiy ya ce: ''Allah Ya nuna balaga kan bacewasu, ta hanyar kore hankali da ji daga gare su, kuma Ya siffanta su a cikin batarsu da dabbobin gida, wadanda ba su jin komai face kira, makafi bebayye ba su hankalta, a'a har ma sun fi dabbobin bacewa.'' (Taisirul Karimir Rahman, shafi na 584).

Kwatanta su da dabbobin gida alama ce ta zama da abin da ko wanda yake cutarwa ba tare da damuwa ba. Domin dabbobin daji suna guje wa mai cutar da su da zarar sun gan shi, amma dabbobin gida suna zaune da mutane wadanda suke kama su daidai da daidai suna yanke su suna ci, amma hakan bai sa su kaurace musu.

''Kuma hankali idan ya zamo bai jagoranci zuwa ga fahimtar maganar Allah da maganar ManzonSa (SAW) da tadabburi a cikin halittun Allah da ababen da Ya halitta masu ban sha'awa da mamaki…To ta haka ya wajaba a ce hankali ya riski gaskiya da tsare kowace mashiga ko kafa da za ta rusa imani ko addini ko wata akida batacciya mai rusa shari'a.'' (Makasidus Shari'atil Islam wa Alakatiha bi Adillatis Shar'iyya, shafi na 243-244).

3. Ukubar shan kayan maye:

Imam Buhari ya ruwaito a sahihinsa: ''Babin bulala ga mashayin giya,'' kuma ya fitar da shi da isnadinsa daga Anas dan Malik (RA) cewa: ''Lallai Annabi (SAW) ya yi duka game da shan giya da takarda ko fata da takalmi. Kuma Abubakar ya yi bulala arba'in.'' (Sahihul Buhari, Kitabul Hudud, Hadisi na 6773 da Muslim a Hudud, Hadisi na 1706).

An karbo daga Sa'ib bin Yazid (RA) ya ce: ''Mun kasance muna zuwa da mashaya a zamanin Manzon Allah (SAW) da zamanin Abubakar haka ya tafi a zamanin Umar, sai mu tashi gare shi, (mu doke shi) da hannuwanmu da takalmanmu.. har zuwa karshen zamanin Umar inda ya ce a yi bulala arba'in, idan suka sake ko suka yi fasikanci sa a yi musu bulala tamanin.'' (Buhari a cikin Hudud, babin duka da takarda ko fata da takalmi, Hadisi na 6779).

Ibnu kudama ya ce: ''Haddi ya wajaba a kan wanda ya sha abin maye kada ko da yawa, kuma ba mu san wani sabani a cikin haka ba ga giyar da aka tace daga inabi wadda ba a dafa ba.'' (Almugni, mujalladi na 12 shafi na 497).

Ibnu Hazam ya ce: ''Sun yi ittifaki a kan cewa wanda ya sha digo daya na giya alhali ya san giya ce na daga inabi, hakika wannan ya isa haddin shan giya idan bai tuba ba kuma lokacin shan bai tsawaita ba aka kama shi lokacin shan ko kuma ba yana zaune a kasar abokan gaba ba, ya wajaba a buge shi, idan ya zamo lokacin da ya sha giyar yana da hankali kuma Musulmi ne ba an tilasta shi ba ne, ba kuma ya suma ba ne, ya alla ya bugu (maye) ko bai bugu ba.'' (Maratibul Ijma'i: shafi na 133).

Kuma Ibnu Hazam ya ce: ''Malamai sun hadu a kan cewa haddin ya kasance gwargwadon duka sau arba'in, amma sun yi sabani wajen cika tamanin, kuma sun lizimtta cewa kada ya wuce tamanin.'' (Maratibul Ijma'i: shafi na 133).

To, idan gwamnati ko hukuma irin ta Najeriya ta ce ba ruwanta da addini kowa ya yi addinin da yake so, kuma ta gaza tsare rayuka kamar yadda ke faruwa a yanzu, to gaza tsare hankulan mutane na dada nuna gazawarta ke nan. Kuma hakan yana nuna ba za ta iya tsare sauran hakkokin da za mu ambata a nan gaba ke nan wato tsare nasaba da dukiya.

Duk kuwa hukumar da ta gaza tsare wadannan abubuwa biyar to kusa da ita da babu daya ne. Domin dama amfanin hukuma komai lalacewarta shi ne ta hana akalla tauye wa mutane wadannan hakkoki ne.

'Yan uwa Musulmi a nan za mu jingine tattaunawa a kan wannan batu kan hakkoki biyar da ke kan gwamnati ko hukuma ta tsare su ga jama'ar da take mulki, saboda karatowar azumin Ramadan inda za mu shiga tabo hukunce-hukuncensa da wasu batutuwa da suka shafe shi cikin yardar Allah.

 Posted By Aka Sanya A Thursday, June 18 @ 05:31:56 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc:
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc



"Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al'umma 08" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com