Muhawara Hausa
 



Zababbun tambayoyi kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (4)
 
Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi Daga Na Abdullahi bin Muhammad bin Abdul'Aziz bin Humaid Fassarar Imam Ahmad Adam Kutubi

Zababbun tambayoyi kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (4)

Tambaya: Ni ma'aikaci ne ina aiki a Riyad, sai na zo Jiddah don yin fasfo, bayan na gama abin da nake yi sai na yi niyyar yin Umara, na yi Harama daga Jiddah, bayan kwana uku na sake yin wata haramar don yi wa mahaifiyata Umara, na yi Harama daga Mikatin Nana A'isha, sai kuma na yi niyyar yi wa mahaifina da ma wasu mutanen daban, tare da cewa mahaifina da mahaifiyata sun rasu, shin abin da na yi niyya ya halatta?

Amsa: Babu laifi don ka yi musu matukar cewa ba ka yi niyyar Umara ba sai a Jiddah, ba a Riyad ka yi ba, wata matsala ce ta kawo ka, wadda da ka gama kuma ka yi niyyar Umara wannan babu laifi. Amma maimaita Umara daga Tan'im ko waninsa wannan bai halatta ba, saboda Sahabban Annabi (SAW), ba sa maimaita Umara, idan son zo Umara daya kawai suke yi ta ishe su, kai mai ka yi daya sai ka shagalta da dawafi kamar yadda Sahabbai da Tabi'ai suke yi , irin su dawusu da Adda'u da wasunsu.

Tambaya: Na zo a jirgi daga Riyad, na yi niyyar idan an zo Mikati in yi Harama amma sai barci ya dauke ni, ban farka ba sai da aka zo Jidda yaya zan yi?

Amsa: Idan ka riga ka yi Harama daga baya, to sai ka yi yanka, idan kuma ba ka yi Harama ba sai ka koma inda Mikati yake wato Sailu ko Wadi Mahra, ka yi Harama a can babu komai.

ambaya: Na zo daga Riyad a jirgi amma ban yi Harama ba, sai na yi Harama a Jidda na yi Umara, da na tambaye ka sai ka ce da ni sai na sake yi Harama ko in yi yanka, na tafi ''Saylu'' na yi wata Haramar a can na sake wata Umarar ta biyu, shin wancan yankan na farko da ban yi ba ya saraya daga kaina ko kuwa?

Amsa: Ka ce ka zo daga Riyad da niyyar yin Umara sai ka yi Harama a Jidda, ka yi Umararka, ka ce na ce da kai, ka je ka yiwo Harama daga ''Saylu.'' A'a, dan uwa ni ban ce maka ka yi Harama a ''Saylu'' ba, matukar a Jidda ka yi Harama sai ka yi yanka, kai koda a Saylu ka yi Harama sai ka yi yanka in dai ka shiga Makka ba tare da Harama ba, ina ma laifin, a ce Mikati ka tafi ka yiwo Harama a can da babu komai, amma indai a Jiddah ka yi Harama yanka ya kama ka, koda bayan wannan Umarar ka yi Umara dubu

ana dai bin ka wancan yankan, amma da a ce ka shiga ne babu niyya daga baya sai ka fito ka tafi Mikati ka yi Harama wannan ya yi, babu laifi.

Tambaya: A bara na yi tafiya daga Riyad zuwa Jidda don yin Umara sai na manta Hiramina, yayin da na yi niyyar yin Harama sai na rasa abin da zan daura a matsayin Hirami, sai da na shiga garin Jiddah na sayo wani Hiramin sannan na yi Umarata shin ina da laifi?

WANI KUMA YA CE: Ni kuma na zo ne ba ni da Hirami sai da na sauka a Jidda na yi Harama a cikinta shin sai na yi yanka?

Amsa: Ai! da ka yi Hirami da kayanka, misali ka yi amfani da rawaninka a matsayin riga, kayanka kuma a matsayin mayafi da babu komai, ko kuma da ka yi niyyarka ta Harama in ya so daga baya sai ka je ka sayi

Hiramin, amma matukar ba ka yi niyyar Harama ba sai da ka shiga Jidda to sai ka yi yanka, saboda ka wuce Mikati ba tare da Harama ba. Abu ne da aka sani cewa idan ka zo ba ka da komai za ka iya yin Hirami da rawaninka da tufafinka ya isar maka.

Tambaya: Na yi Hajji amma ban san takamaiman inda Mikati yake ba, sai na yi Harama a tsakanin Makka da Madina, sai bayan na koma Riyad da na tambayi wani dalibi sai ya ba ni fatawar cewa in yanka tunkiya, a Makka, ni kuma na ba shi uzirin cewa zuwa Makka ta yi nisa ga shi kuma ni ba mai iko ba ne, sai ya ce in yi azumin kwana goma a jere, sai na yi azumin shin hakan ya isar?

Amsa: Gaskiya ne, yanka ta kama ka wanda dole sai a Makka za ka yi, amma da ka ce ta yi nisa sai ya ba ka fatawar ka yi azumi, wannan kuskure ne, babu wani azumin kwana goma da za ka yi matukar kana da ikon yin yanka, sai dai idan ba ka da iko, to babu laifi don ka yi azumi, dama wanda ba shi da abin da zai yi yanka shi aka bai wa damar yin azumi, amma idan kana da iko dole ka je ka yi yanka ko kuma ka tura da kudin, wani ya yanka maka ya rabar maka da naman.

Tambaya: Shin mace tana da wasu kebabbun kaya ne da za ta yi Harama da su, kuma mene ne hukuncinta idan ta yi Harama da fararen kaya?

Amsa: Mace da namiji matsayinsu daya wajen Harama, bai Halatta ta yanke farce ba, bai halatta ta fitar da gashin kanta ba, bai halatta ta rufe fuskarta ba idan ta yi Harama, sai dai idan ta ji tsoron kada maza su dame ta da kallo. Amma game da launin kayan da za ta yi Harama da su ba a kebe wasu kaya na musamman ba. Za ta iya Harama da kowane irin kayanta kore ko fari ko baki, koma dai wane launi ne, kawai dai ba a so ta yi Harama da kayan ado wadanda za su dauki hankali, domin wajen Allah ta zo kamata ya yi, ta yi shiga takankan da kai.

Tambaya: Shin ya halatta mace ta yi harama alhali tana sanye da kayan ado?

Amsa: Babu laifi mace ta yi Harama tana sanye da zobe ko a hannunta akwai wani abu na Zinare, Haramarta ta yi sai dai ana so ta rufe shi kada ta bayyana adonta.

Tambaya: Shin ya halatta mace ta yi amfani da magani don kada haila ta zo mata da azumi ko a kwanakin Hajji?

Amsa: Babu laifi, ya halatta amma da sharadin kada ya zama zai cutar da mace don ta yi amfani da shi. Malamai suna fada a karshen fasalin haila cewa babu laifi don mace ta yi amfani da maganin da zai tsayar mata da haila matukar dai yin amfani da maganin ba zai haifar mata da wata cuta ba, ko kuma magungunan hana daukar ciki, ko masu hana maniyyi gudana don kada a dauki ciki na wasu kwanaki sanannu, dukkan wadannan babu laifi insha Allahu.

 Posted By Aka Sanya A Wednesday, December 02 @ 08:10:30 PST Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi:
Bayyanar mata masu neman mata a kasar Hausa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi



"Zababbun tambayoyi kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (4)" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com