Muhawara Hausa
 



ME YA FARU A KARBALA? 2 Wane ne YAZIDU?
 
Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi ME YA FARU A KARBALA? 2 Wane ne YAZIDU?

Sunansa YAZIDU Dan Mu'awiyah Dan Sakhr (Abu Sufyan) Dan Harb Dan Umayyah Al Umawy Al Qurashie.

Ana yi masa alkunya da Baban Khalid.

Mahaifiyarsa ita ce Maisun 'yar Bahdal daga kabilar Kalbu, daya daga cikin kabilun Kuraishawa masu karfi a wancan lokaci. Ta rabu da mahaifinsa tana dauke da cikinsa, sai ta yi mafarkin wata ya fito daga jikinta. Masu Fassara suka ce mata in har mafarkinki ya tabbata za ki haifi sarki.

Hakan kuwa aka yi.

An haifi YAZIDU a shekara ta 26H a zamanin halifancin sayyidina Usmanu Dan Affan. YAZIDU ya tashi a gidan sarauta, domin ko da aka haife shi mahaifinsa yana gwamnan Sham. Ya samu tarbiyyar jihadi domin tun yana matashi dan shekaru 24 ya jagoranci runduna mafi girma da ta fatattaki Rumawa kuma ta kwace hedikwatarsu ''Qustantiniyah''. Daga nan ne kuma sunan YAZIDU ya fara fitowa har ya yi tashe a tsakanin matasa. A nan ne kuma ya samu tasa daraja daga Hadisin Ummu Haram bint Malhan Matar sayyidina Ubada bin As Samit wacce ta ce ta ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam na cewa ''Rundunar farko da zasu yi yaki a teku daga cikin al'ummata Allah ya gafarta masu''. Ta ce, Manzon Allah ina cikin su? Ya ce, eh. Kina cikinsu. Sannan ya ce ''Rundunar farko da zasu ci birnin Qaisar daga cikin al'ummata su ma Allah ya gafarta masu''. Ta ce, Manzon Allah ina cikin su? Ya ce, a'a. (Sahihul Bukhari, Hadisi na 2924).

Wannan Hadisi ya hada falalar YAZIDU da babansa gaba daya.

Domin kuwa babansa Mu'awiyah ne ya fara jagorantar Rundunar farko da ta yi jihadi da Rumawa a teku, zamanin sarki Usmanu a shekara ta 27H. A cikin rundunarsa kuwa har da irin su Miqdadu Dan Amru da Shaddadu Dan Ausu da Abu Dharril Gifari da Ubada Dan Samit tare da wannan matar da ta gamu da ajalinta kai tsaye bayan gama yakin.

Shi kuma YAZIDU shi ne ya ci babban birnin Qustantiniyah a shekara ta 52H. Qustantiniyah kuwa ita ce birnin Qaisar a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam. A cikin sojojin wannan runduna tasa kuwa har da wasu fitattun sahabbai irin su Ibnu Umar da Ibnuz Zubair da Ibnu Abbas da Abu Ayyub al Al Ansari, mai masaukin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam, Wanda kuma ya cika kafin kammala yakin.

(Duba Fathul Bari na Al Hafizh Ibnu Hajar 6/120 da kuma Al Bidayah Wan Nihaya na Ibnu Kathir 6/249).

Kafin haka YAZIDU ya yi Amirul Hajji na musulmi baki daya a shekara ta 50H.

Ba zamu yi mamaki ba idan muka ga mahaifinsa ya zabe shi a matsayin Yarima. To, amma ko mene ne ya sa aka zabe shi alhalin akwai wadanda suka fi shi irin su HUSAINI jikan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam?

Wannan ita ce tambayar da zamu amsa a nan gaba Sa'annan mu dawo ma rikicin mawallafa da takin sakar su a kan wannan dan taliki YAZIDU kafin mu fantasia cikin maganar rikicin da ya hada shi da YAZIDU Wanda a sanadiyyarsa Allah ya ba shi shahada.

Allah ya kai mu gobe

 Posted By Aka Sanya A Tuesday, May 09 @ 05:14:49 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi:
Son Maso Wani Koshin Yunwa!: Gidan Annabi Mohammad (SAW)


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi



"ME YA FARU A KARBALA? 2 Wane ne YAZIDU?" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com