Muhawara Hausa
 



MARABA DA WATAN RAMADAN [6]
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen BUDA BAKI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA

MARABA DA WATAN RAMADAN [6]

Haqiqa buda baki yana daga cikin Sunnar Annabi (SAW).

•BUDA BAKI: shine mai Azumi ya buda baki (Yaci wani abu) idan rana ta fadi, yini ya bada baya dare kuma ya gabato, daga wannan lokacin buda baki yayi ga mai Azumi.

•GAGGAUTA BUDA BAKI:

Gaggauta buda baki yana kawo wa al'ummar musulmi alkhayri, saboda Hadithin Sahal dan Sa'ad (RA) ya tabbatar cewa:

Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Mutane ba zasu gushe tare da alkhayri ba matuqar suna gaggauta buda baki" (Bukhari 4/173, Muslim 1093)
Idan al'ummar Musulmi suna gaggauta buda baki to haqiqa sun wanzar da Sunnar Annabi (SAW), Yazo a hadithin Sahal dan Sa'ad (RA) cewa:

Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Al'ummata ba zata gushe a kan sunnata ba matuqar bata jiran 6ullowar taurari, a wajen buda bakinta ba" (Ibn Hibban 891 ya ruwaito shi da ingantaccen isnadi)
kuma an ruwaito Hadith daga Abu Hurayrah (RA)
cewa:

Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Addinin Musulunci ba zai gushe ba rinjayayyen addini matuqar musulmi suna gaggauta buda baki lokacin Azumi. Saboda yahudu da nasara suna jinqirta buda baki" (Abu- dawud 891 ya ruwaito shi da ingantaccen isnadi).

•ABUNDA YA KAMATA A BUDA BAKI DASHI:

Haqiqa Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance yana kwadaitar da al'ummarsa akan su buda baki dabino kamar yadda yazo a Hadithin Ans dan Malik (RA)
Yace:

Manzon ALLAH (SAW)
Ya kasance yana buda baki da danyen dabino kafin yayi sallah, idan bai samu ba sai yayi da busashshe, idan bai samu ba sai ya kamfaci ruwa, saboda shi mai tsarki mai tsarkakewa ne" .

(Mutane 5 suka ruwaito shi, Ibn Khuzaimah, Ibn Hibban, Hakeem sun inganta shi)
•ADDU'A A WAJEN BUDA BAKI:

Ya 'Yan uwana haqiqa Addu'armu a wajen buda baki kar6e66iya ce, saboda haka muyi addu'o'i muna masu sakankacewar an kar6a mana. Amma mu sani cewa ALLAH baya kar6ar addu'ar wanda zuciyarsa rabkananniya ce mai wasa daga ambaton ALLAH.

Abu-Hurayrah (RA) ya ruwaito Hadith cewa:

Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Addu'o'i 3 abin kar6awa ne: Addu'ar mai Azumi, Addu'ar wanda aka zalunta, Addu'ar matafiyi, wannan sune addu'ar da ba a mayar wa.

A wani Hadith kuma Abu-Hurayrah (RA)
Yace: Manzon ALLAH (SAW) Yace: " Addu'o'i 3 ba'a mayar dasu ko kuma mutum 3 ba a komar da addu'arsu:

Addu'ar mai Azumi lokacin buda baki, Addu'ar shugaba mai adalci, Addu'ar wanda aka zalunta" .

•MAFIFICIYAR ADDU'A A WAJEN BUDA BAKI:

Haqiqa an samo daga Hadith cewa Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance duk lokacin da zai buda baki yana cewa:

"ZHABAZ ZAMA'U WABTALATIL URUQU WA THABATAL AJRU INSHAA ALLAH" .

Ma'ana "Qishirwa ta tafi, jijiyoyi sun sanyaya, ladar (ALLAH)
ta tabbata in ALLAH yaso" .

(Abu-dawud 2/306, Baihaqi 4/239, Hakeem 1/422)
ALLAH YA AMSA MANA IBADUNMU (Ameen).

-Faridah Bintu Salis.

(Bintus-sunnah)

 Posted By Aka Sanya A Tuesday, May 09 @ 05:40:02 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen



"MARABA DA WATAN RAMADAN [6]" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com