Muhawara Hausa
 



AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA, TSARABAN RAMADAN
 
Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA, TSARABAN RAMADAN

(1) Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawa 6/505:-

(( ﻭﺍﻟﺨﻴﺮ ﻛﻞ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻓﻲ ﺍﺗﺒﺎﻉ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ ﻭﺍﻻﺳﺘﻜﺜﺎﺭ ﻣﻦ ﻣﻌﺮﻓﺔ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺍﻟﻔﻘﻪ ﻓﻴﻪ ﻭﺍﻻﻋﺘﺼﺎﻡ ﺑﺤﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﻼﺯﻣﺔ ﻣﺎ ﻳﺪﻋﻮ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ﻭﺍﻷﻟﻔﺔ ﻭﻣﺠﺎﻧﺒﺔ ﻣﺎ ﻳﺪﻋﻮ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻼﻑ ﻭﺍﻟﻔﺮﻗﺔ ﺍﻻ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﺃﻣﺮﺍ ﺑﻴﻨﺎ ﻗﺪ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻓﻴﻪ ﺑﺄﻣﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺠﺎﻧﺒﺔ، ﻓﻌﻠﻰ ﺍﻟﺮﺃﺱ ﻭﺍﻟﻌﻴﻦ )).

Ma'ana: ((Sannan alheri kuma dukkan alheri yana cikin bin magabata na gari, da kuma yawaita ilmin hadithin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah, da kyakkyawar fahimta cikinsa, da yin riko da igiyar Allah, da lazimtar abin da ke kira zuwa ga jama'a da hadin kai, da nisantar abin da ke kira zuwa ga sabani da rarraba, sai fa abin da ya kasance al'amari ne bayyananne da tabbas Allah da manzonSa ne suka yi umurni cikinsa da wani umurni na a nisanta, to wannan kam biyayya sau da kafa)).

(2) Alhaafiz Ibnu Rajab ya ce cikin littafinsa Alhikamul Jadiiratu Bil Izaa'ah shafi na 12:-

(( ﻓﺎﻟﻮﺍﺟﺐ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﻦ ﺑﻠﻐﻪ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻋﺮﻓﻪ ﺍﻥ ﻳﺒﻴﻨﻪ ﻟﻼﻣﺔ ﻭﻳﻨﺼﺢ ﻟﻬﻢ ﻭﻳﺄﻣﺮﻫﻢ ﺑﺎﺗﺒﺎﻉ ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺍﻥ ﺧﺎﻟﻒ ﺫﻟﻚ ﺭﺃﻱ ﻋﻈﻴﻢ ﻣﻦ ﺍﻻﻣﺔ، ﻓﺎﻥ ﺍﻣﺮ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺍﺣﻖ ﺍﻥ ﻳﻌﻈﻢ ﻭﻳﻘﺘﺪﻯ ﺑﻪ ﻣﻦ ﺭﺃﻱ ﺍﻱ ﻣﻌﻈﻢ ﻗﺪ ﺧﺎﻟﻒ ﺃﻣﺮﻩ ﻓﻲ ﺑﻌﺾ ﺍﻻﺷﻴﺎﺀ ﺧﻄﺎ، ﻭﻣﻦ ﻫﻨﺎ ﺭﺩ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭﻣﻦ ﺑﻌﺪﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﺨﺎﻟﻒ ﺳﻨﺔ ﺻﺤﻴﺤﺔ، ﻭﺭﺑﻤﺎ ﺍﻏﻠﻈﻮﺍ ﻓﻲ ﺍﻟﺮﺩ ﻻ ﺑﻐﻀﺎ ﻟﻪ، ﺑﻞ ﻫﻮ ﻣﺤﺒﻮﺏ ﻋﻨﺪﻫﻢ ﻣﻌﻈﻢ ﻓﻲ ﻧﻔﻮﺳﻬﻢ، ﻭﻟﻜﻦ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﺣﺐ ﺍﻟﻴﻬﻢ، ﻭﺃﻣﺮﻩ ﻓﻮﻕ ﺍﻣﺮ ﻛﻞ ﻣﺨﻠﻮﻕ، ﻓﺈﺫﺍ ﺗﻌﺎﺭﺽ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻭﺃﻣﺮ ﻏﻴﺮﻩ ﻓﺄﻣﺮ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻭﻟﻰ ﺍﻥ ﻳﻘﺪﻡ ﻭﻳﺘﺒﻊ )).

Ma'ana: ((Abin da ke wajibi a kan dukkan wanda umurnin manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya same shi kuma ya san shi to ya bayyana shi ga Al'umma, ya musu nasiha, ya umurce su da bin umurninsa koda kuwa hakan ya saba wa ra'ayin wani babba cikin Al'umma, domin umurnin Manzon Allah shi ya fi cancanta da a girmama kuma a yi koyi da shi a kan ra'ayin wani wanda ake girmamawa da ya saba wa umurninsa cikin sashin wasu abubuwa a bisa kure, daga ma nan ne Sahabbai da wadanda ke bayansu suke yin raddi a kan dukkan mai saba wa Sunnah Sahihiya, sau da dama ma sukan yi kaushi cikin raddin, ba kuma saboda nuna kiyayya gare shi ba, a'a yana nan abin so a gare su kuma abin girmamawa a cikin rayukansu, to sai dai manzon Allah shi ya fi soyuwa a wurin su, kuma umurninsa yana sama da umurnin ko wace halitta, saboda haka idan umurnin Manzo ya yi karo da umurnin waninsa, umurnin Manzon ne ya fi cancanta da a gabatar kuma a bi)).

(3) Shehu Uthmanu Dan Fodiyo ya ce cikin littafinsa Ihyaa'us Sunnah Wa Ikhmaadul Bid'ah shafi na 8:-

(( ﻗﺪ ﺍﻧﻌﻘﺪ ﺍﻹﺟﻤﺎﻉ ﻋﻠﻰ ﺍﻥ ﺁﺭﺍﺀ ﺍﻟﻤﺠﺘﻬﺪﻳﻦ ﻛﻠﻬﺎ ﻣﺴﺎﻟﻚ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻭﻃﺮﻕ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮﺍﺕ، ﻓﻤﻦ ﺳﻠﻚ ﻣﻨﻬﺎ ﻃﺮﻳﻘﺎ ﻭﺻﻠﻪ ﺍﻟﻰ ﻣﺎ ﻭﺻﻠﻮﺍ ﺍﻟﻴﻪ ﺣﻘﺎً، ﻭﻣﻦ ﻋﺪﻝ ﻋﻨﻪ ﻗﻴﻞ ﻟﻪ ﺳﺤﻘﺎ، ﻭﻳﺠﻮﺯ ﺗﻘﻠﻴﺪﻫﻢ ﻓﻲ ﻛﻞ ﺭﺃﻱ ﺍﻻ ﻣﺎ ﺧﺎﻟﻒ ﻧﺺ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﺍﻭ ﻧﺺ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻭ ﺍﻟﻘﻮﺍﻋﺪ ﺍﻭ ﺍﻹﺟﻤﺎﻉ ﺍﻭ ﺍﻟﻘﻴﺎﺱ ﺍﻟﺠﻠﻲ ﻓﺎﻓﻬﻢ )).


Ma'ana: ((Hakika Ijmaa'i ya kullu a kan cewa lalle ra'ayoyin Mujtahidai dukkansu hanyoyi ne zuwa Aljannah, kuma hanyoyi ne zuwa alkhairai, wanda duk ya bi wata hanya daga cikinsu to tabbas za ta kai shi zuwa inda suka kai, wanda kuma ya karkata ga barin hakan sai a ce da shi tir. Kuma yin koyi da su na halatta cikin dukkan wani ra'ayi, sai dai abin da ya saba wa nassin Alkur'ani, ko nassin Hadithi, ko Ka'idodi, ko Ijmaa'i, ko Bayyanannen Kiyasi, ka fahimta)).

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya cusa mana son sahihiyar Sunnah da kuma son yin aiki da ita cikin dukkan wani abu na Aqiidah, ko Ibaadah, ko Mu'aamalah. Ameen.

 Posted By Aka Sanya A Tuesday, May 09 @ 06:02:52 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc:
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 5
Kurioi: 1


Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc



"AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA, TSARABAN RAMADAN" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com