Muhawara Hausa
 



NURULHUDA KUSAKURAN DA SUKA YADU A BAKUNAN MUTANE
 
Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi FADAKARRAWA GA MUSULMAI

NURULHUDA KUSAKURAN DA SUKA YADU A BAKUNAN MUTANE 1

Cewa: AN HALICCI DUNIYANE DOMIN MANZON ALLAH ‏ Wannan kuskure ne ya sabawa nassin Alqur'ani..

Allah ya halicci duniya tun kafin ya halicci manxon ‏Allah.. kuma ya halicci manzon Allah ﷺ da duniya domin Bautarsa ne kawai.

Allah yace cikin suratul kahfi:

''Kace ni ban kasance ba face mutum kamar ku, ana wahayi gareni cewa lallai Allahnku Allah dayane, duk wanda yake burin haduwa da Ubangijinsa. Toh ya aikata aiki NA gari. Kuma kada ya hada bautar ubangijinsa da kowa ''.

Wannan ayar ta nuna mana..

Annabi mutum ne kamar kowa..

Banbancin mu dashi kawai shine shi Anai masa wahayi.

Abinda yake daidai shine: Allah ya halicci duniya da abinda ke cikinta har da annabi Muhammad (SAW) ba don komi ba sedan su bauta masa.

Dalili shine fadin Sa madaukakin sarki.

''Ban halicci Aljanu da mutane ba FACE dan su bautamin''.

Ayar taxo da siga mai gamewa..

sannan ayar da muka kawo a sama ta nuna mana cewa Manzon Allah dayane daga cikin mutane, dan haka ya shiga cikin wadanda Allah yake cewa bai haliccesu se dan bautansa.

A wani wajen Allah yacewa manxon Allah

Ka bautawa ubangijinka har lokacin da yaqini (mutuwa )zatazo maka.

Allah yace:

Kuma bamu halicci sammai da qassai ba domin wasa.... se yace:

Bamu haliccesu ba sedan gaskiya.sedai dayawa daga cikinsu basu sani ba.

Dan haka Allah ya halicci duniyace domin gaskiya wanda itace ake ganin girman Allah da ikonsa da yadda yake jujjuya Al- amura. Da rahamarsa.. badan komai ba sedan agane cewa shi kadai ya cancanci bauta.

Nassosi akan wannan suna da yawa Muna rokon Allah ya shiryi masu waccar fahimtar. Ya dawo dasu kan gaskiya, mu kuma ya tabbatar damu akanta.

Allah yasa mudace .

©SA'AD ALBANY

 Posted By Aka Sanya A Wednesday, October 04 @ 08:24:56 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi:
Bayyanar mata masu neman mata a kasar Hausa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 5
Kurioi: 1


Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi



"NURULHUDA KUSAKURAN DA SUKA YADU A BAKUNAN MUTANE" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com