Muhawara Hausa
 



**DUNIYAR MUTUWA**(5)
 
Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi **DUNIYAR MUTUWA**(5)

Da muka isa sama ta 2, nanma aka bude mana har muka isa ta 7, sai naga itace mafi girman sammai, sai naga tamkar rafi agabanmu, naga Mala'iku sun sunkuyas da kawunansu, suka ce: ''Allahumma innaka antas-salaam waminkas-salaam tabaarakta ya zhal-jalaali wal ikraam'' sai naji wani firgici, na qasqantar da kaina hawaye na zubomin, sai Allah yacewa Mala'ikun: ''Ku sanya littafin bawana cikin illiyin (shine rukunin da ake sanya littafan yan Aljannah -Allah ka sanya mu cikinsu-), kuma ku maisheshi zuwa qasa, domin daga gareta na haliccesu kuma cikinta zan maishesu kuma daga gareta zan tashesu wani lokaci na daban. Sabida tsananin Firgici, tsoro, da farin ciki da Murna, ban iya cewa komai ba sai: Tsarki ya tabbata gareka, bamu bauta maka ba yanda ya kamata!.

Sai mala'ikun nan suka sauko dani zuwa qasa, duk sanda muka hadu da mala'iku sai muyi masu sallama, sai nacewa Mala'ikun: shin zai yiwu nasan abinda ya faru da gangan jikina da iyalaina?

Sai sukace: jikinka dai zaka ganshi, amma iyalanka ayyukansune kawai da zasu dinga maka kyautarsu zasu dinga riskarka, amma bazaka gansu ba! Suka dawo dani qasa, suka ajeni kusa da jiki na, sukace: ka kasance a jikinka, mu aikinmu ya qare anan, bayan an sanyaka a qabarinka, wasu Mala'ikun 2 zasu zo maka! Sai nace dasu: Allah maku Albarka, ya saka maku da Alkhairi! To amma zan sake ganinku kuma? Sai sukace: A ranar Qiyaamah zamu tsayu gaba daya, wannan shine ranar halatta (domin dukkan mutane, Aljanu da mala'iku zasu halacce ta), sai naga sanda suka ambaci qiyamah sautinsu ya chanza, sannan sukace: Amma in ka kasance cikin yan Aljannah, zamu zamo tare ku zaka gammu.

Nace: to bayan naga Aljannah kuma naji sautin ababen cikinta, shin akwai sauran shakku agareni (na zan shiga ko za'a korani wuta)?

Sai sukace: Lamarin Shiga Aljannah lamarine da Allah kadai ya mallakeshi, kuma kai ka samu karramawa sabida ka mutu musulmi, abinda yayi saura shine a nuna maka ayyukanka (a qabarinka da qiyamah) da kuma mizani!

Sai fuska ta ta chanza har na kusa kuka, domin ina tuna zunubaina tamkar manyan duwatsu! Sai suka ce dani: Ka kyautata zatonka ga Ubangijinka, kuma ka qudurce cewa Ubangijinka bai zaluntar kowa, Sai sukai min sallama, sukai sama da sauri…..

Naga jikina akwance, sannan sai naji sautin kuka, sautine da na sanshi, Mahaifinane me qaunata da kuma dan-uwana, -subhaanallah, ina nakene yanzu?- sai na kalli jikina naga ana zuba masa ruwa, sai na gane cewar yanzu ana wanke gaawa ta ne! Sautin kukan nan na matuqar takuramin, amma duk sanda naji Mahaifina na cewa: ''Allah ya sassauta maka, Allah maka rahmah'' sai naji tamkar ana zubamin ruwan sanyi ne, sai suka rufe jikina da farin likafani.

Sai nace cikin raina: KAICONA ACE MA BAN TABA BARIN MINTI 1 BA A RAYUWATA FACE CIKIN AMBATON ALLAH, KO SALLAH, KO WATA IBADAH! Kaicona ace ina sadaqa dare da rana, kaicona kaicona!

Babban burina shine qabari, da abinda zai biyo bayansa, sai naji mai min wanka na cewa: shin zaku masa sallah ne bayan La'asar? Babana yace: Eh insha Allah -cikin kuka-! Suka dauki gaawata, ina kallonta amma bana iya magana ko motsi, suka shigar dani firij da ake sanya gaawarwaki, chan sai naji ana cewa: ku daukeshi ku kaishi masallaci! Suka daukeni inajin duk maganganunsu, babban abinda ya fi damuna shine kukan Mahaifina, kamar ince masa: kada ka damu yaa Baba, abinda ke wajen Allah yafi Alkhairi! Don Allah kabar kuka, domin ina shan radadi a dalilin kukanku, amma ko na fadi bazasu jini ba! Inajin sautukansu kuma ina gane muryar kowa, yan'uwana, kuma duk ina jin maganganunsu! Suka isa masallaci suka ajeni, sukai sallar la'asar, nai kwadayin dama ace ina taredasu muyi sallar nan nima nasamu lada! Chan bayan idar da sallah sai naji ladan na cewa: Jama'a kuzo muyiwa dan-uwanmu sallah!

Bayan liman ya soma sallah, sai ga Mala'iku 2 sun zo, daya na tambayar dayan adadin masu mani sallah, nawane cikinsu muwahiddai basu hada Allah da wani? Suna rubutawa! Bayan kabbara ta 3, wacce cikinta ake mani Addu'a, sai naga mala'iku na rubuta abubuwa masu yawa, sai nasan suna rubuta Addu'o'in jama'a ne! Nai fatan dama ace liman ya tsawaita wannan kabbara kada yayi ta 4, domin har na soma sararawa ina jin dadi! Sai yayi kabbara ta 4 yayi sallama! Suka daukeni suka kaini Qabarina…………­…..

Mu hadu a na 6 don jin yanda zata kasance a Qabari.

 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 01 @ 01:42:35 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi:
Bayyanar mata masu neman mata a kasar Hausa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi



"**DUNIYAR MUTUWA**(5)" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com