KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) 31
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=474

 
Daga Sheikh Aliyu Said Gamawa KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) 31 BANBANCIN DA KE TSAKANIN SHUGABANNIN MAZHABOBI WAJEN HANYOYIN DA SUKE DOGARA DA SU (4) 3. MAZHABAR IMAMUS-SHAFI'I Qa'idoji da ginshiqan mazhabar Imamus-Shafi'i (R.A.) su ne abin da ya tattara cikin littafinsa na ''Usulul Fiqhi'' mai suna (Ar-risala) wanda ake ganin shi ne farkon littafin Usulul Fiqhi mai gamewa da aka wallafa a Musulinci. Al- Imamus-Shafi'i (R.A.) ya ce: Tushen Shari'ar Musulunci shi ne Qur'ani da Sunnah, idan ba a sami nassi a cikinsu ba, sai a yi qiyasi a kansu. Idan kuma salsalar Hadisin da aka ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W.) ta sadu da shi, kuma ta inganta, to wannan shi ne matuqa. Ijma'i kuma ya fi gauron Hadisi. Haka kuma ana daukar Hadisi ne a kan zahirin lafazinsa, idan kuma yaqunshi ma'anoni fiye da daya, to ma'anar da ta fi kusa da zahirin ita ta fi cancanta a fahimce shi da ita.
Idan kuma Hadisai suka yi kafada da kafada da juna, to Hadisi mai salsalar da ta fi inganci shi ne mafificinsu, Hadisi Munqadi'i kuwa, ba a bakin komai ya ke ba, idan ba daga Ibnul Musayyib ya ke ba. Hadisi ''Munqadi'i'' shi ne wanda maruwaici daya ya saraya daga salsalarsa, amma da sharadin kada mai sarayar ya zama Sahabi ne shi. Kuma ba a qiyasce Shari'a kan wani tushen da ba nata ba, kuma ba a cewa da tushen Shari'a ta qaqa ko saboda me? Sai dai ana iya cewa don me ga reshen Shari'a kawai. Idan kuma qiyasin reshen ya inganta a kan asali, ya zama ingantacce ke nan, kuma za a iya kafa hujja da shi. Saboda haka Imamu Shafi'i yana bayanin cewa Qur'ani da Sunnah duk matsayinsu daya ne, dangane da shar'antarwa. Babu wani sharadi da ake shardanta wa Hadisi banda inganci, da saduwa da tushensa, domin shi ma asali ne na Shari'a, shi kuwa asali ba a ce masa saboda me, ko ta qaqa? Haka kuma ba a shardanta wa Hadisi ya zama mashahuri idan ya zo cikin abin da yake da wahala a kauce masa (kamar yadda Imamu Abu Hanifa ya sharxanta), amma bai shardanta rashin savawar Hadisi da aikin mutanen Madina ba, (kamar yadda Imamu Malik ya shardanta), sai dai bai yarda da wani Hadisi daga Hadisan ''Misalai'' ba, in banda na Sa'idu Ibnul Musayyib, domin nasa suna da hanyoyin da suka dangana su ga tushe a wajensa. A nan Imamu Shafi'i ya saba da Maliku da Sauriy da sauran tsarakunsa (daga malaman Hadisi) wadanda suke kafa hujja da irin wadannan Hadisai. Haka kuma bai amince da kafa hujja da ''Istihsani'' ba, a wanda a nan ma ya saba da Malikawa da da Hanafawa gaba dayansu. Har ma ya rubuta littafinsa game da rashin amincewa da Istihsani mai suna ''Ibdalul istihsan,'' sannan ya fadi maganar nan tasa mashahuriya inda ya ce, ''Wanda duk ya aiwatar da istihsani, to ya shar'anta hukunci. Kamar yadda ya qi karbar Masalihul-mursala, ya qi amincewa da kafa hujja da ita. Haka kuma ya qi amincewa da kafa hujja da qiyasin da bai kafu a kan wani ingantaccen dalili mabayyani ba. Haka kuma ya qi amincewa da kafa hujja da aikin mutanen Madina, kamar yadda ya kasance yana ganin kuskuren Hanafawa game da barin su ga aiki da Hadisai masu yawa saboda rashin cika sharudan da suka gindaya a kansu wajen aikin Hadisan, kamar shuhura, da makamancinta. Haka kuma bai taqaita ba, (kamar yadda Malik ya taqaita) wajen riqo da Hadisan mutanen Hijaz su kadai. Wadannan su ne ginshiqan Mazhabar Imamu Shafi'i mafiya muhimmanci kuma mafiya fice a jimlance wadanda ana iya ganin sabani tsakaninsu da ginshiqan mazhabar Hanafawa da Malikawa a fili.Batun: Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi