Shin Allah Yana sonmu? (4)
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=482

 
Daga Salihu Is'hak Makera

Shin Allah Yana sonmu? (4)

Kuma daga cikin mutanen da Allah Subhanahu Wa Ta'ala Yake so, akwai Nana Khadija (Radiyallahu Anha). Ya zo a cikin Sahihul-Bukhari cewa Annabi (SAW), yana zaune tare da Mala'ika Jibril suna karantun Alkur'ani, sai Nana Khadija (RA) ta zo. Sai Jibril (AS) ya juya ga Annabi (SAW) ya ce: ''Wannan Khadija ce ta kawo maka abinci. Ka isar mata da sallamata!''

A nan Mala'ika Jibril (AS) ne yake mika gaisuwa ga Nana Khadija (RA), sannan sai Jibril ya ce: ''Ka yi mata bushara tana da gida a Aljanna!''

Me zai faru idan Allah Yana sonmu?:

Da farko dai Allah Madaukaki zai ambaci sunan mutum Ya ce, wane dan wane, sannan Allah Ya kira Mala'ika Jibril (AS) Ya shaida masa cewa shi Allah Yana son wancan mutum. Kuma ba so kawai Allah zai nuna wa mutumin ba, zai umarci Jibrila (AS) ya so wannan mutum. Baya ga Jibril, mala'ikun da suke cikin sama da na kasa za su so wannan mutum. Sannan Allah Ya sanya kauna da soyayyar wannan mutum a zukatan mutane.
To, idan irin wannan mutum ya roki Allah komai, Allah zai ba shi, idan kuma ya nemi tsarin Allah daga kowane abu, Allah zai tsare shi. Kuma duk mutumin da ya samu irin wannan matsayi yanke dan Aljanna ne. 

Mu sake tambayar kanmu, ''Shin Allah Yana sonmu?'' Idan har muna ji a jikinmu cewa Allah ba Ya sonmu saboda ba mu aikata abin da ya dace, to 'yan uwa mu yi wa kanmu kiyamul laili, mu tuna da karashen wannan Hadisi da muka fara kawowa, mu guje wa abin da zai fusata Allah. Mu guji mutanen da suke aikata ayyukan da ke fusata Allah. Domin Manzon Allah (SAW) ya fadi a karshen Hadisin cewa: ''Idan kuma Allah Ya ki mutum (saboda saba maSa), zai kira Mala'ika Jibril (AS) Ya ce masa: ''Ya Jibrilu! BawaNa wane dan wane yana ci gaba da fusata Ni, don haka fushiNa ya tabbata a gare shi.'' 

Ke nan samun so daga Allah yana ta'allaka ne da bin abin da Allah Yake so kuma Ya yarda da shi na daga ayyukan da'a. Kuma Allah Yana daukar duk wanda ya yi maSa biyayya a matsayin masoyinSa. Shi ya sa za mu ga Alkur'ani da Sunnah cike suke da darussan da suke nuni kan yadda za mu samu soyayya daga Allah Subhanahu Wa Ta'ala.

Babban ginshikin samun soyayya a tsakanin bawa da Ubangijinsa, shi ne yin imani da kuma yin aiki nagari. ''Lallai wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai (nagari), wadannan su ne mafifita alherin halitta. Sakamakonsu a wurin Ubangijinsu shi ne gidajen Aljanna, koramu na gudana a karkashinsu, suna madauwama a cikinsu har abada. Allah Ya yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa. (k:98:8).

Ibnu Al-kayyim (Rahimahullah) ya rubuta hanyoyi da dama da za mu bi, mu samu son Allah Subhanahu Wa Ta'ala kamar haka: 

Na daya: Mu rika amfani da sulusin karshe na dare wajen yin nafilfili da karatun Alkur'ani da zikiri da hailala da sauran ibadoji na gabbai. Domin Annabi (SAW) ya ce a irin wannan lokaci: ''Allah Madaukaki Yana sauka zuwa saman duniya, Ya rika kiran mutane: ''Ko akwai masu addu'a, in amsa musu! Ko akwai mai neman gafara in gafarta musu!'' Don haka mu ci moriyar wannan lokaci ta wajen nafilar kiyamul laili.

Na biyu: Mu rika ambato (zikiri) Allah a kowane lokaci. Ko a wurin aiki ko sana'a ko muna tsaye ko a zaune, mu rika amfani da wannan lokaci mu rika ambaton Allah. Mu rika tuna Allah a duk abin da za mu aikata, ko za mu ci, ko za mu sha. Domin Allah Ya ce: ''Saboda haka ku tuna Ni, In tuna ku.'' (k:2:152). Wane ne ba ya son Allah Ya rika tuna shi?

Na uku: Wajibi ne mu rika karanta Alkur'ani tare da fahimtar ma'anarsa. Mu karanta abin da Allah Ya saukar mana domin rayuwarmu da mutuwarmu. Allah Madaukaki Ya ce: ''Shin ba za su yi tadabburi (nazari ko kula) da Alkur'ani ba.'' (k:4:82).

Kuma Allah (SWT) Ya sake cewa: ''(Wannan) Littafi ne Mun saukar da shi zuwa gare ka yana mai albarka, domin su lura da ayoyinsa, don masu hankali su rika yin tunani.'' (k:38:29). 

Na hudu: Mu zauna tare da mutanen da suke son Allah (SWT) so na gaskiya, mu tafiyar da lokacinmu a wurinsu. Domin a cikin Surar Khafi, Allah (SWT) Ya ce: ''Za su ce, ''Uku ne da na hudunsu karensu. Kuma suna cewa, ''Biyar ne da na shidansu karensu,'' a kan jifa cikin duhu. Kuma suna cewa, ''Bakwai ne da na takwas dinsu karensu.'' Ka ce, ''Ubangijina ne Mafi sani ga kidayarsu, babu wanda ya san su face kadan.'' (k:18:22).

A wannan aya Allah Madaukaki Ya ambaci karen Mutanen Kogo sau da dama. Don me? Saboda abokan tafiya da karen yake da su na mutanen kirki ne, shi ya sa aka ambace shi sau da dama. To idan za a ambaci kare a Alkur'ani sau da dama saboda wadanda yake tare da su mutanen kirki ne, to ka ji mamakin yadda Allah zai so mutumin da ya zabi ya tafiyar da lokacinsa ta zama tare da mutanen da Allah Madaukaki Yake so. Annabi (SAW) ya koya mana cewa misalin abokin zama nagari kamar mai sayar da turare ne. Koda bai ba ka turaren ba, za ka sha kanshinsa.

Na biyar: Wajibi ne mu so haduwa da Allah (SWT) Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Duk wanda yake son haduwa da Allah, (lami lafiya) to, Allah ma Yana son haduwa da shi.''

Ko shakka babu idan mutum yana son haduwa da Allah Madaukaki lami lafiya, zai rika yin ayyuka nagari don haduwa da Shi, zai yi tattalin wannan haduwa. Wanda kuma ba ya son haduwa da Allah zai tafiyar da rayuwarsa ce cikin sabon Allah. Ba zai so haduwa da Allah (SWT) ba, kuma Allah ba zai so haduwa da wannan bawa ba.

Na shida: Mu kawar da duk wani abu da zai shiga tsakaninmu da Allah Madaukaki. Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya umarce mu cewa mu yi dubi da idon basira kan kowane al'amari da muke yi, mu guji duk abin da ya saba wa Allah. 

Allah Ya sa mu dace, amin.Batun: Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin