RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI 02
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=498

 
Daga Dr. Mansur Sakkwato Wallafar:

RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI 02

Sheikh Faisal Bn Ali Al- Ba'adani Fassarar:

Dr. Mansur Ibrahim Sokoto da Mal. Aliyu Rufa'i Gusau.

BABI NA DAYA 1.0 Rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama Kafin watan Azumin Ramalana:

Wannan babi zai yi tsokaci ne a kan yadda rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke kasancewa kafin watan Azumin Ramalana ya kama, ta hanyar yawaita Azumin nafila da yake yi a cikin watan Sha'abana, da yi wa Sahabbansa bushara da kamawar watan, tare da yi masu bayanin abubuwan da yake dauke da su na falala, da wasu abubuwa masu kama da haka.
1.1 SHIMFIDA:

Kasancewar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama mutum mai matuqar tsoron Allah Subhanahu Wa Ta'ala da gudun duniya, da tsananin kwadayin abin da Allah Ta'ala ya yi tanadi na kyakkyawan sakamako gobe qiyama.

Sai hakan ta sa yake qara murna da farin ciki, a duk lokacin da wani yanayi na saukar alherin Allah da rahamarsa da jinqayinsa ke qara qamari. Yana kuwa yin haka ne Sallallahu Alaihi Wasallama saboda cika umurnin Allah Subhanahu Wa Ta'ala da yake cewa: ''Kace, su yi farin ciki da samun falalar Allah da rahamarsa. Wannan shi ne mafi alheri fiye da abin da suke Tarawa.'' (10:58)

Wannan aya na tabbatar da cewa yin farin ciki da abin da Allah Ta'ala ya saukar a cikin Alqur'ani, ya kuma hori bayinsa da aikatawa, wanda ya hada da abubuwa na wajibi da na mustahabbi, kamar Azumin Ramalana, wanda kusan babu wani wajibi da ya sha gabansa. To, yin farin ciki da samuwar wadannan abubuwa a falsafar Musulunci, shi ne mafi zama alheri, bisa ga duk wani farin ciki da bawa zai yi a kan tarin tulin wani abu na duniya.

Malam Sa'adi na cewa, qarin bayani a kan wannan aya: ''Ko alama, ba a hada ni'imar addini da ta abin duniya; matsayinsu ba daya ba. Ni'imar addini ta hada arzikin duniya ne, da na lahira baki daya. A yayin da shi kuwa abin duniya, ko a duniyar ba ya da wani garanti. Domin kuwa gishirin qoqo ne, ana cikin kadi yake qarewa. Saboda haka ne Allah Ta'ala ya hori musulmi da yin farin ciki a kan samuwar falala da rahamarsa na addini. Domin hakan na lamunce masu kwanciyar hankali da nishadi da godiya ga Allah Ta'ala.

Wanda a sakamakon haka sai su qara samun qwarin guiwa, da tsananin kwadayi da sha'awar ilmi da inganta imaninsu. Wannan shi ne farin ciki na Shari'a. Ita kuwa murna a kan wani abu na sha'awoyin duniya da jin dadinta, ko natsuwa da faruwar wata masha'a, aikin banza ne. Domin kuwa Allah Ta'ala ya yi tir da masu yin annashawa don abin duniya. Kamar yadda yake ba mu labarin irin yadda ta kasance tsakanin Qaruna da mutanensa, inda suka ce masa; ''Kada ka yi fahariya, lalle ne Allah ba ya son masu fahariya (da abin duniya).

Haka kuma Allah Subhanahu Wa Ta'ala ya yi wa wasu mutane kashedi da yin bugun gaba saboda wani abu da suka mallaka na barna, sabanin abin da Manzanni suka zo da shi na shiriya, inda yake cewa: ''Sa'annan a lokacin da Manzanninsu suka je masu da hujjoji bayyanannu, suka yi farin ciki da abin da ke wurinsu na ilmi.'' (40:83) wannan kenan. Sannan kuma tabbataccen abu ne cewa, babu wani abu da ke gaggauta kusanta bawa da Ubangijinsa, da daukaka alqadarinsa tare da lamunce masa yardar Mahalicci, da saka shi gaban sahu, kamar irin watan Azumin Ramalana da ire-irensa. Matuqar bawa ya gudanar da ibadodi a cikin irin wadannan lokutta kamar yadda aka umurce shi, ta hanyar zare damtse da yin da'a ga ubangijinsa, lalle ya rabauta. Saboda haka ne Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba ya sake da irin wadannan lokuta. Da zarar an ce watan Azumin Ramalana ya gabato, to, sai Ma'aiki ya sha damara ya shirya ransa da zuciyarsa da gangar jikinsa, ta yadda zai fuskanci wannan ibada cikin cikakken nishadi. Wanda hakan za ta ba shi damar cin moriyar watan baki daya.

Muhimman hanyoyin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke taron Watan Azumi da su, sun hada da:

A dakace mu a darasi na gaba in Allah ya so.Batun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen