Adalcin Musulunci: Wasu misalai daga rayuwar Umar dan Khaddabi (4)
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=499

 
Daga Salihu Makera

Adalcin Musulunci: Wasu misalai daga rayuwar Umar dan Khaddabi (4)

Ba ma hukunta 'ya'yan ‘manya' idan suka yi laifi ba, na kusa da manyan ma ba a hukunta su. Sannan 'ya'yan manyan kokari ake a nuna musu cewa ajinsu daban da na talakawa, su mutane ne na musamman da bai kamata su rika cudanya da talakawa a asibitoci da makarantu da kasuwanni da wuraren aiki ba! Ba a bari su je su gwada hazaka da basirarsu wajen daukar aiki tare da 'ya'yan talakawa. ‘Special offer' ake ba su in lokacin daukar aiki ya zo. Kai wasu ma suna makaranta ake ajiye musu guraben da za su yi aiki, alhali hakki ne na kowa a tsakanin jama'ar kasa!

A haka muke tunanin mu je Lahira Allah Ya ba mu Aljanna kamar yadda zai ba wadancan shugabanni magabata?

Duk wanda aka ba shi shugabanci sannanen abu ne cewa adalci ne kawai zai kubutar da shi a gobe kiyama, kamar yadda nassoshi da dama suka tabbatar. Shugabanci koda na 'yan dako ko yankan farce ko acaba ko ma na mene ne akwai wajibcin yin adalci a cikinsa, balle na jama'ar unguwa ko kauye ko gunduma ko garuruwa ko karamar hukuma ko mazabar dan majalisa ko ta sanata ko jiha ko kasa.
Kuma Ubangijin nan guda daya ne, Shi ne na zamanin Annabi Adam (AS), Shi ne na zamanin sauran Annabawa (Alaihimus Salam), Shi ne na yau, kuma Shi ne na gobe, Shi ne na na farko da ba ya da mafari kuma na karshe da ba ya da iyaka ko karshe. Kuma ma'auni daya zai yi amfani da shi wajen yi wa kowannenmu hisabi kafin a kai shiga Aljanna ko wuta. Wannan ma'auni shi ne imani da aiki nagari. Duk wanda ya rasa su, kada ya sa ran akwai wata dabara ko dangataka da za su kubutar da shi. Kada ya sa ran cewa domin Allah Ya yiwo shi a Najeriya za a yi masa shari'a daban da na wanda ya fito daga Saudiyya ko Iran ko Afghanistan ko Ingila ko Jamus ko Faransa!
A ci gaba da kawo kissar adalcin Amirul Muminina Umar dan Khaddabi (RA), ba za mu mance da kissar Gwamnan Baharain ba wato Jarud da wani sabon musulunta mai suna Idrias.

An zargi Idrias da leken asiri ga makiya Musulunci sakamakon ganawar da aka ga ya yi da wani makiyi. An tuhumi Idrias amma ya nuna ba haka ba ne, duk da haka Gwamnan Baharaini ya ci gaba da tuhumarsa. ''Mun hadu da shi a kan hanyata ta zuwa gida. Ya rika yin tambayoyi amma na nuna masa ba ni da abin da zan gaya masa,'' inji Idrias.

Amma sai Jarud ya katse shi cewa: ''Kana jin zan amince da wannan bayani naka? Abin da na sani ka ci amanarmu. Don haka babu batun sassauci, kuma ba zan lamunci haka ba. Ku kama wannan mutum ku sare wuyansa!''

A daidai lokacin da aka kama Idrias za azartar masa da hukunci sai ya ce cikin murya mai karfi ''Ya Umar! Ya Umar!'' Muryarsa ta karade sassan garin cikin daren.

Bayan lokaci kadan sai labarin kashe shi ya isa ga Amirul Muminina Umar dan Khaddabi (RA). Ba tare da bata lokaci ba, Umar ya aika cewa Jarud ya je Madina. Lokacin da Jarud ya isa Madina sai aka kai shi gidan Umar (RA), inda ya kai kansa ga Halifa. Da Umar ya gan shi, sai ya rike mashinsa alamar babbar magana, sannan ya ce ''Idrias na ji ka'' ya fadi haka har sau uku kafin ya juyo wajen Jarud.

Ya ce da Jarud: ''Ina jiran bayaninka kan kashe dan uwanka Musulmi, Idrias da ka yi.''

Sai Jarud ya fara da cewa: ''Ya Amirul Muminina! Ka san yadda Baharaini take a halin yanzu. Muna kewaye da makiya da masu yi musu leken asiri 'yan kadan daga cikinmu wadanda suke ba su bayanan sirri a kanmu. Ba sau daya ba, ba sau biyu ba, mutanen da muka amince da su suke cin amanarmu wajen yi wa Musulunci zagon kasa. Suna nuna gazawa kuma sun lalace da son abin duniya inda suke jawo asarar rayukan mutanenmu da dama. Kuma game da batun Idrias an gan shi yana tattaunawa da makiyi. Don haka ba za mu iya ci gaba da zama da munafukai ba.''

Cikin murya mai sanyi Umar ya ce: ''To kana da hujja ko shaidar da za ta tabbatar da laifinsa?''

Sai Jarud ya ce: ''Ba ni da wata karfaffar hujja ya Amirul Muminina!''

''Wato ka furta da kanka cewa ka kashe wannan mutum ne bisa zargi kawai,'' inji Umar (RA).

''Haka ne ya Amirul Muminina!'' Jarud ya mayar da amsa.

Nan take Umar (RA) ya ce: ''Mutumin nan bai aikata laifin da ake zarginsa ba. Idan ba ka kawo min hujja ko shaidar ya aikata wannan laifi ba, ya tabbata marar laifi. Don haka ba a hukunta wani mutum har sai an tabbatar da ya aikata laifin da ake tuhumarsa. Saboda haka yanzu ka je ka biya iyalansa diyyar ransa, kuma na sauke ka daga mukamin Gwamnan Baharain,'' inji Umar sannan ya juya wa Jarud baya.

Tirkashi! Marasa laifi na Musulmi da wadanda ba Musulmi ba nawa masu mulki ke halakawa bisa zargi marar tushe? Wani Gwamna ko Sanata ko dan Majalisar Tarayya ko ta jiha ko ciyaman, adawa ta siyasa kawai wadda dimokuradiyya ta halatta, in ta shiga tsakaninsa da wani, sai ya sa a halaka shi ba tare da ma da an gabatar da shi a gaban shari'a ba!

Hakika wannan hukunci na Umar (RA) ya nuna wa dukkan Musulmi a fili cewa ba za a hukunta mutum kan zargi kawai ba, kuma dukkan Musulmi ko jama'ar kasa marasa laifi ne har sai kotu ta tabbatar da laifi a kan dayansu. 

Za mu rufe darasinmu na yau da ayoyi masu zuwa domin tunatar da kawunanmu game da koyarwar wannan addini mai girma:

''Lallai Allah Yana umurni da adalci da kyautatawa da bai wa ma'abucin zumunta, kuma Yana hani ga alfasha da abin da aka ki da rarraba kan jama'a. Yana yi muku gargadi, dammaninku, kuna tunawa. Kuma ku cika alkawarin Allah, idan kun yi alkawari, kuma kada ku warware rantsuwoyinku a bayan karafafa su, alhali kuma hakika kun sanya Allah Mai lamuncewa a kanku. Kuma lallai Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatawa. Kuma kada ku kasance kamar wadda ta warware zarenta a bayan tufka, ya zama warwararku, kuna rikon rantsuwoyinku domin yaudara a tsakaninku, domin kasancewar wata al'umma ta fi wata riba daga wata al'umma! Abin sani kawai Allah Yana jarrabar ku da shi, kuma lallai ne Yana bayyana muku a Ranar kiyama, abin da kuka kasance a cikinsa kuna saba wa juna. Kuma da Allah Ya so hakika da Ya sanya ku al'umma guda, kuma Yana batar da wanda Ya so, kuma Yana shiryar da wanda Ya so. Lallai ne ana tambayarku abin da kuka kasance kuna aikatawa…. Abin da yake a wurinku yana karewa, kuma abin da yake a wurin Allah ne mai wanzuwa. Kuma lallai Muna saka wa wadanda suka yi hakuri da ladarsu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa. Wanda ya aikata aiki na kwarai daga namiji ko kuwa mace alhali yana mumini, to, hakika, Muna rayar da shi, rayuwa mai dadi. Kuma hakika, Muna saka musu ladarsu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa.'' (k:16:90-97).
Batun: Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi