FATAWAR MANYAN MALAMAN DUNIYA KAN WANTA BAI YI NIYYAR AZUMIN RAMADHAN BA SAI DA
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=502

 
Daga Dr. Isa Ali Pantami

FATAWAR MANYAN MALAMAN DUNIYA KAN WANTA BAI YI NIYYAR AZUMIN RAMADHAN BA SAI DA SAFE

Akwai fatawoyi guda biyu na Malamai ga Wanda ya kwanta babu labarin GANIN wata, kuma sai da gari ya waye ya Samu labarin GANIN Watan.

1) Suna GANIN bai da Azumi, sai ya Rama, saboda Hadith da ke cewa: ''Babu Azumi ga Wanda bai YI Azumi ba gabannin Alfijir''

2) Wanda kuma itace mafi inganci ga Malamai irin Shaykh Nasiruddeen Albaniy, Shaykh Saleem bn Idd Alhilaliy, da Aliyu Hassan Ali AbdulHameed cewa wannan Azumi yayi ko da safe mutum yayi NIYYAR. Sun kafa hujja da cewa A) Hadithin da masu cewa Azumi bai YI ba, yana magana Akan Wanda ya bar NIYYAR da ganganci, ba Wanda ya bari a rashin sani ba.

Wannan shine Maganar Abuddarda, Abu-Dalha, Abu Huraira, Bn Abbas, Huzaifa. Duba Taaliqut-Taaliq.
B) Cewa Hukuncin farilla baya canjawa, kuma a farkon Musulunci lokacin da aka farlanta Azumin Ashura, akwai Sahabbai da sun YI breakfast da sabe. Amma Manzon Allah, sai ya ce suyi Azuminsu, kuma bai ce su Rama ba bayan RAMADHAN. (Duba Bukhari 3/212, Muslim 1125).

C) Masu cewa a ''Kama baki'' sai bayan Ramadhan tukunna mutum ya Rama, to gaskiya babu wata Ibadah Mai suna Kama baki a Musulunci. Kuma babu Nassi Akan Kamun baki.

Don haka abunda yafi karfin hujja, itace Fatwa ta biyu. Idan Baka da labarin GANIN Wata sai da safe.

Sai kaci GABA da Azumi ko da bayan breakfast ne, kuma Azumi yayi in sha Allah. Wallahu A'alam.

Allah ya sa mu daceBatun: Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin