Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al'umma (2)
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=504

 
Daga Salihu Is'hak Makera

Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al'umma (2)

Abin da ke nuni kan tsare addini ya zo ne a cikin fadinSa Madaukaki: ''Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kowa face Shi.''

Game da tsare da tsare dukiya Ya ce: Kuma ka bai wa ma'abucin zumunta hakkinsa,'' da kuma fadinSa: ''Kuma kada ka bazzara dukiyarka, bazzarawa.'' 

Kuma game da tsare rai sai Ya ce: ''Kuma kada ku kashe 'ya'yanku,'' da kuma fadinSa: ''Kuma kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta face da hakki.'' (Islam wa Daruraul Hayat, shafi na 18-19).

b. Daga Sunnah:
An karbo daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: ''Ku guji abubuwa bakwai masu halakarwa.'' Suka ce: ''Ya Manzon Allah! Su wanne ne?'' Ya ce: ''Shirki da Allah da sihiri da kashe rai wadda Allah Ya harama face da hakki da cin dukiyar riba da cin dukiyar maraya da juya baya a fagen yaki da kuma yin kazafi ga kamammun mata muminai gafalallu ''daga aikata barna).'' (Buhari a Kitabul Wasaya Babin kaulin Lahi Ta'ala'' Innalazina ya'akuluna amuwalil yatama zulman.'' Hadisi na 2615 da Muslim a cikin Al'Iman, Hadisi na 89).

Abdullahi kadiri ya ce: ''Hakika Annabi Sallallahu Alaihi Wa sallam ya ambaci aikata wadannan abubuwa da masu halakarwa ne, saboda ba abin da ke zama mai halakarwa sai idan ya kasance tsare wannan al'amari lalura ne daga cikin lalurorin rayuwa.'' (Islam wa Daruratul Hayat, shafi na 20).

Kuma an karbo daga Ubbadata bin Sabit (RA) cewa lallai Manzon Allah (SAW) ya ce a lokacin akwai wasu sahabbai kewaye da shi: ''Ku yi min mubaya'a a kan ba za ku yi shirki da Allah ba cikin komai ba, ba za ku yi sata ba, ba za ku yi zina ba, ba za ku kashe 'ya'yanku ba, ba za ku zo da keren karya da kuke kirkira a tsakanin hannuwanku da kafafunku ba, ba za ku saba (min) a cikin aikin alheri ba. To duk wanda ya cika (wadannan hukunce-hukunce) daga cikinku to sakamakon ijararsa yana ga Allah. Wanda kuma ya aikata wani abu daga cikin wadannan za a yi masa ukuba a duniya a matsain kaffara gare shi. Wanda kuma ya aikata wani abu daga cikinsu, sa'an nan Allah Ya rufa masa asiri (Ya boye shi), to al'amarinsa yana ga Allah, idan Ya so Ya yi masa afuwa, idan Ya so Ya yi masa ukuba (horo).'' Sai muka yi masa mubaya'a a kan haka.'' (Buhari a cikin Kitabul Iman, Babu Alamatul Iman Hubbil Ansar, Hadisi na 17 da Muslim a cikin Hudud, Hadisi na 1709).

Abdullahi kadiri ya ce: ''Hakika sahabban Manzon Allah (SAW) sun yi masa mubaya'a a kan kiyaye wadannan lalurori, su ne kiyaye addini cikin fadinsa (SAW) ''Ba za ku yi shirkin komai da Shi (Allah) ba,'' da kiyaye rai cikin fadinsa: ''Ba za ku kashe rai wanda Allah Ya haramta ba, face da hakki,'' da kiyaye nasaba da zuriya da mutunci a cikin fadinsa: ''Ba za ku yi zina ba,'' da kuma fadinsa: ''Ba za ku zo da keren karya da kuke kirkirarsa a tsakanin hannuwanku da kafafunku ba,'' da kuma kiyaye dukiya cikin fadinsa (SAW): ''Ba za ku yi sata ba.'' (Al-Islam wa Daruraul Hayat, shafi na 21).

c. Daddalewa kan dalilan na shari'a:

Imam Shadabi ya ce: ''Hakika al'umma da sauran addinai da akidoji sun hadu a kan cewa, lallai an sanya shari'a ce domin tsare wadannan lalurori biyar su ne: addini da rai da nasaba da dukiya da hankali. Saninsu a wurin al'umma (malamai) kamar lalura ne. Kuma haka bai tabbata gare mu da wani dalili ayyananne ko muka samu shaida ta asali ayyananniya da za a koma a kanta ba, a'a an sani da dimbin dalilai na shari'a makare da dalilai da ba za a takaita su a cikin babi daya ba.'' (Al-Muwafikat, mujalladi na 1 shafi na 31).

2. Jerantuwar laluran:

Ibnu Amir Alhaji ya ce: ''Ana gabatar da tsare addini daga cikin lalurorin a kan sauran yayin bijirowa ne saboda shi ne makasudi mafi girma na halittar dan Adam: ''Kuma ban halitta aljanu da mutane ba sai don su bauta Mini.'' (k:51:56). Waninsa an samar da su ne saboda shi, kuma alherinsa (addini) shi ne mafi kamalar alherai, wato samun sa'ada ta har abada a yayin makwabta da Ubangijin talikai. Sannan sai aka gabatar da tsare rai a kan tsare nasaba da hankali da dukiya, saboda ya kunshi gyaran addini, domin sai da shi za a iya gudanar da ibada. Kuma samuwar ibada yana dogara ne da samun rayuwa. Sannan ya gabatar da tsare nasaba, domin shi tabbatar da rayuwar abin haihuwa bai yiwuwa sai da haramta zina domin kada a gurbata nasaba. Ta haka sai a jingina abin haihuwa da mutum daya wanda zai kula da tarbiyyarsa da tsare rayuwarsa. Idan aka rasa haka, sai a yi watsi da shi, rayuwarsa ta shiga halin da ba zai iya kare tab a. Sannan sai aka gabatar da tsare hankali a kan tsare dukiya, saboda yadda yake kare raid a karfinsa ta yadda idan aka rasa hankali duk karfin dan Adam sai ya hade da dabbobi, kuma takalifanci ya fadi daga kansa, don haka rasa shi tamkar rasa rai ne kacokan ta yadda za a biya cikakkiyar diyya kansa, sannan sai kiyaye dukiya.'' (At-Takrir wat Tahyyir, mujalladi na 3, shafi na 231).

3. Hanyoyin tsare lalurorin:

Imam Asshadabi ya ce: ''Kiyaye su yana kasancewa ne da abubuwa biyu:

Na farko: Abin da yake tsayar da rukunansu ya tabbatar da ka'idojinsu. Wannan manufa ce ta kiyaye su ta fuskar samuwa.

Na biyu: Kawar da duk abin da zai iya yi musu illa tta auko musu ko su auka cikinsa, wannan yana nufin kiyaye su ta fuskar rasa su.

Usulai na ibadoji suna komawa ne zuwa ga kiyaye addini ta fuskar samuwa kamar imani da furta kalmar Shahada da Sallah da Zakka da Azumi da Hajji da makamantansu.

Al'ada kuma tana komawa wajen tsare nasaba da dukiya ta fuskar samuwa, haka ma tsare rai da hankali, amma shi ma ta fuskar al'ada. Sannan jinane, umarni da alheri da hana abin ki na tattara su tare da tsare dukkansu daga rasa su.'' (Al-Muwafikat, mujalladi na 1, shafi na 18-20).Batun: Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc