Idan mutum yana cikin yin sahur, sai ya ji kiran sallah yaya zai yi?
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=508

 
Daga Sheikh Abdulwahhab Abdullah AMSA:

Idan mutum yana cikin yin sahur, sai ya ji kiran sallah yaya zai yi?

A irin wannan hali mutum zai qarasa abin da ke hannunsa ne.

Domin hadisi ya tabbata daga Abu Huraira radhiyallahu anhu ya ce:

Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce:

Ma'ana:

Idan dayanku ya ji kiran sallah alhali qwarya tana hannunsa, kada ya ajiye ta, har sai ya biya buqatarsa .

Amma a nan sai a yi hattara, kada a mayar da irin wannan dabi`a ta zama al`ada a kullum domin ba ance mustahabbi bane yin hakan ballantana a ce ana so a rinqa yi, sassauci ne akayi ga wanda ya fara cin abinci sai lokaci ya kure masa.
wa sallallahu wa sallama ala Nabiyyina Muhammadin wa ala aa'lihi wa sahbihi ajma'in.

Yaushe ne ya fi dacewa a yi sahur?

Daga Sheikh Abdulwahhab Abdullah AMSA:

Yaushe ne ya fi dacewa a yi sahur?

Haqiqa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya kwadaitar da a jinkirta yin sahur zuwa kusan ketowar alfijir, kamar yadda ya tabbata a cikin hadisin da aka karbo daga Anas daga Zaid Ibn Thabit radhiyallahu anhu ya ce:

Ma'ana:

Mun yi sahur tare da Annabi sallallahu alaihi wa sallama, sannan sai ya tashi zuwa sallah.

Sai na cewa (Anas) yaya (tsawon lokacin da ke) tsakanin kiran sallah da yin sahur yake? Sai ya ce:

Gwargwadon (karanta) ayoyi hamsin .

Haka kuma an karbo daga Sahal Ibn Sa'ad radhiyallahu anhu ya ce:

Ma'ana:

Na kasance ina yin sahur cikin iyalina, bayan wannan sai in yi gaggawa domin in samu sujada (sallah) tare da Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama.

Wadannan hadisai na nuna cewa ana yin sahur ne dab da ketowar alfijir.
Batun: Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin