RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI 04
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=509

 
Daga Sheikh Faisal Bn Ali Al- Ba'adani Fassarar:

RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI 04

Dr. Mansur Ibrahim Sokoto da Mal. Aliyu Rufa'i Gusau.

TABBATAR DA KAMAWAR WATAN RAMALANA:

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba yakan soma Azumin Ramalana ba, face ya tabbatar da kamawar watan, ta hanyar samun shedar wani mutum daya da ya ga watan da qwayar idonsa, ko tabbatar da watan Sha'abana ya cika kwana talatin.

Wadannan hanyoyi biyu na tabbatar da kamawar Watan Azumi, na daga cikin martabobin da wannan addini ya kebanta da su, kuma wadanda suka lamunce ma sa dacewa da kowane zamani da kowane wuri, saboda komai nasa a fili yake, ta yadda gaba dayan mutane na iya zama sheda a kai.

Daga cikin Hadissan da ke tabbatar da dogarar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke yi a kan tabbatar tsayuwar watan Azumi, a kan ganin qwayar ido akwai:
Hadisin dan Umar Raliyallahu Anhu wanda ya ce: ''Mutane sun sa ido ga neman ganin jinjirin watan Azumi, sai na gaya wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa tabbas ni na gane shi. Sai kuwa ya kama Azumi, ya kuma umurci mutane da su kama.''

Sai kuma Hadisin dan Abbas Raliyallahu Anhuma wanda ya ce:

''Wani Balaraben qauye ya zo wurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: ''Tabbas ni na ga jinjirin watan Azumi.'' Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masa: ''Ko ka yi imani da babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah? '' Shi kuwa ya karba masa da cewa: ''Eh, na yi.'' Sai kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya sake tambayarsa: ''Ko ka yi imani da cewa, Muhammadu Manzon Allah ne?

Balaraben ya ce: ''Eh, na yi.'' Daga nan sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa Bilalu: ''Tafi ka shelanta wa mutane kowa ya ta shi da Azumi gobe.''

Ka ga a cikin wadannan Hadissai, musamman ma na biyun, akwai babban darasi, da ke tabbatar da girman wannan addini. Wanda kuma ya kamata a ce Malamai da shugabannin wannan al'umma sun kwaikwaya. Wato su fahimci cewa kowane mutum amintacce ne kuma karbabbe a idon Shari'a, a mataki na farko. Ba kuma za a qi karbar maganarsa ba a kan komai, sai idan wani mugun hali ya bayyana gare shi, wanda zai soki lamiri da adalcinsa. Ko kuma a wayi gari tare da fahimtar cewa, yana da qarancin hankali, ko kuma ba ya son kowa da alheri sai kansa.

Wannan ko shakka babu haka yake.

Domin ka ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yarda da maganar Balaraben qauye a kan wani babban al'amari a Musulunci, wato Azumi, ba kuma tare da wani irinsa ya goya masa baya ba, shi Balaraben. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai yi la'akari da kasancewar Azumin Ramalana ginshiqin addini ba, balle ya nemi shedar taron jama'a a kan tsayuwar watansa. Wannan aqida kuwa, ita ce abin da ya kamta masu tsananta wa mutane al'murran addini, su fahimta su kuma kama, tare da komowa a kan tafarki madaidaici.

Haka kuma daga cikin Hadissan da ke tabbatar da dogarar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi a kan cikar watan Sha'abana kwana talatin, kafin ya kama Azumi, idan ganin watan Azumi da qwayar ido ya faskara, akwai cewar da ya yi wa Sahabbai, su dogara a kan ganin qwayar ido ga watan ba hisabi ba.

Kuma su tabbatar da qarewarsa ta wannan hanya. Ya ce: ''Kada ku kama Azumi sai an ga wata da qwayar ido.

Haka kuma kada ku aje shi, sai an ga watan Sallah da qwayar ido. Kuma kada ku yarda da wata hanya da ba wannan ba. Idan Kuma kuka kasa ganinsa saboda wani dalili, to ku bari sai watan Sha'abana ya cika kwana talatin. Da zarar mutum biyu sun bayar da sheda, to ku kama Azumi, ku kuma aje idan irinsu suka bayar da shedar qarewarsa.''

A wani Hadisin kuma da Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: ''Wata kan yi kwana ashirin da tara. Kada ku kama Azumi har sai kun ga wata da qwayar idonku. Idan kuma kuka kasa ganinsa saboda wani dalili, to ku bari sai Sha'abana ya cika kwana talatin.''

Saboda haka babu wani dalili da zai sa mutum ya dauki Azumi kafin a tabbatar da tsayuwar wata, wai don ko aka yi. Domin kuwa Shari'a ta riga ta yi wa al'amarin makama. Saboda haka ne ma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi mana kashedi da ''Ko- aka yi'' ya ce: ''Kada ku kuskura ku kama Azumi tun watan Ramalana bai tsaya ba, ku bari sai an gan shi da qwayar ido, sannan, idan kuma an ga Sha'abana ta wannan hanya, ku aje.

Idan kuma giragizai suka hana ku ganin sa, to, ku jira Sha'abana ya cika qwana talatin.

A wani Hadisi kuma ya ce: ''Kada ku yi Azumin nafila da kwana daya ko biyu kafin watan Ramalana ya tsaya, sai fa wanda ke yin wani Azumi daban, shi kam irin wannan mutum ya samu ya yi Azuminsa.''

Ka ga a shar'ance abin da wadansu mutane ke yi wato Azumin ''Ko-aka yi''

laifi ne. Saboda wadannan Hadissai da suka tabbatar da rashin halaccin fara Azumin Ramalana ba tare da an ga jinjirin watansa da qwayar ido, ko aka tabbatar da cikar Sha'abana kwana talatin ba, Ammaru dan Yasir Raliyallahu Anhu ya ce: ''Duk wanda ya yi Azumin ''Ko-aka yi'' haqiqa ya saba wa Baban Qasimu Sallallahu Alaihi Wasallama.

Amma kuma duk da haka, idan mutum bai san yadda ake kirdadon tabbatar da tsayuwar jinjirin wata ba, kuma ba ya da wanda zai isar masa a kan haka.

Idan ya yi wannan Azumi na ''ko-aka yi'' amma da niyyar idan an yin, to, ya riga ya kimtsa. Idan kuma ba a yin ba, to, ya dauki Azumin nasa a matsayin nafila. To, Azuminsa ya inganta a zance mafi rinjaye. Saboda niyya na tabbata ne a lokacin da masaniya ta tabbata, kuma hukuncinsu daya ne.

Idan har ya tabbata cewa watan na Ramalana ya tsaya, to wajibi ne ya yi wa Azumin nasa matsaya. Da kuma a irin wannan hali zai yanke niyyar yin Azumin nafila ne, ko Azumi kawai, to, da sakal. Domin kuwa umurnin da Allah ya yi masa shi ne na daura niyyar yin Azumin Ramalana, wanda ya wajaba a kansa, wanda kuma idan ba shi ya yi ba, da sauran magana.

Amma idan ba ya da masaniya da cewa watan Azumi ya tsaya, to, ba wajibi ne a kansa ya yanke wa Azumin nasa hukunci ba. Duk kuwa Malamin da ya wajabta yanke hukuncin a irin wannan hali, to kamar ya daura aure ne tsakanin ruwa da wuta. Allah shi ne masani.

Yau da musulmi za su dawo su qanqame wannan Sunnah ta Manzo.

Su tsaya a kan ganin qwayar ido ko cikar watan Sha'abana kwana talatin, don tabbatar da kamawar watan Azumi, da an huta. Wata fitina ba za ta sake tashi ba, balle a yi ta jayayya a kan halaccin yiwuwar amfani da hisabi da ilimin zamani, ko rashin haka.

Domin kuwa a shar'ance ba ya hallata a qetare abin da nassi ya zo da shi.

To, kuma ga shi abin da nassi ya qunsa a wannan al'amari, shi ne dogara a kan gani na qwayar ido, ba hisabi ba. Amma kuma duk da haka, da za a yi amfani da na'aurorin zamani a tabbatar da haihuwar watan, sannan ya bayyana a fili a gan shi da ido, to, wajibi ne a yi aiki da hakan.

Domin kuwa waccan magana ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba ta batse hakan ba, balle. Don cewa ya yi ''Kada ku dauki Azumi ko ku aje shi sai an ga jinjirin watansa da qwayar ido.'' Idan kuma hakan ta faskara, sai batun jiran kwanakin Sha'abana su ciki talatin, kamar yadda nassin ya tabbatar.

Kuma duk da haka, ba laifi ba ne a yi amfani da tabaran hangen nesa kamar kuma yadda yin hakan ba tilas ba ne.

Saboda abin da Sunnah ta nuna qarara, shi ne dogara a kan gani irin na qwayar ido, kuma na al'ada kawai.

Kuma shi ne kawai abin da ke wajaba a kan al'umma don tabbatar da bayyanar jinjirin wata. Allah shi ne mafi sani.

Ita kuwa cewar da Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: ''Azumi da idin qaramar Sallah da layya na karba sunansu ne idan an yi su tare da mutane.'' Wannan magana na nufin ne ba ya halatta ga wasu mutane su yi tunga, su yi Azumi ko Idi ko layya ba tare da sauran jama'a ba. Lalle ne kowane musulmi ya yi wadannan ibadodi tare da Sarki da sauran jama'a.

Ka ga da Allah zai sa masu wa'azi a wannan zamani namu su rungumi wannan aqida, su kuma yayata ta tsakanin musulmi, da kansu ya hadu a cikin gunadar da wannan ibada. Kuma rikitta da rigingimun da ke qamari a tsakanin tsirarun musulmi a qasashen gabasci da yammacin Turai sun fada.

Mafi sauqin hanyar da wannan manufa ke iya tabbata kuwa a hasashena, ita ce kafa wata hukuma ko cibiya mai zaman kanta wadda za ta kula da farawa da qarewar kowane wata kamar yadda Shari'a ta tanada. Ta haka da zarar sun tabbatar da tsayuwar watan Azumi ko qarewarsa, sai su kama Azumi tare su aje tare. Idan kuwa suka neme shi qaura-wambai, amma ganinsa ya faskara, to sai a jira Sha'abana ya cika kwana talatin, sannan a dauki Azumin. Shi kuma Ramalana ya cika talatin din sannan a aje. Idan kuwa har hakan ta faskara, wato suka kasa ganin watan a garin da suke, to sai su yi aiki da ganin da wani gari na musulmi da ke kusa da su, suka yi masa. Su dauki Azumi tare da su. Iyakar abin da za su iya yi kenan, Allah kuwa ba ya dora wa rayuwa abin da ba ta iya dauka.Batun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen