RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI 09
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=516

 
Daga Sheikh Faisal Bn Ali Al- Ba'adani Fassarar:

RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI 09

Dr. Mansur Ibrahim Sokoto da Mal. Aliyu Rufa'i Gusau.

Ci gaban darasinmu na RAYUWAR ANANBI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA TSAKANINSA DA UBANGIJINSA A LOKACIN AZUMIN RAMALANA (5)

Aje Azumi:

Ya tabbata cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba ya aje Azumi sai ya tabbatar an ga wata, ko sun cika kwanaki talatin cur suna Azumin. Dalili kuwa shi ne, an riwaito yana cewa:

''Kada ku dauki Azumi ko aje shi sai an ga wata, ku kiyaye wannan. Idan kuma watan ya shige hazo, to, ku cika talatin. Idan kuwa shedu biyu suka sheda, to ku yi Azumi ku kuma aje.''

Kamar mas'alar farko ta kamawar watan na Azumi, a wannan ma, wato qarewarsa, muna kira ga mutane da cewa, zance mafi rinjaye shi ne dogara a kan ganin wata da qwayar ido kafin a aje Azumi, ba lissafi irin na masana taurari ba. Hadisin da muka kawo a kan wannan magana kuma shi ne dalili. Amma kuma duk da haka ya zama wajibi a kan kowane musulmi, ya yi matuqar qoqarin ganin kan musulmi ya hadu, ta hanyar gudanar da da wannan ibada tare da juna.
Babu kuma yadda za a yi wannan manufa ta tabbata sai kowannen mu ya kasance mai son gaskiya da karbar ta, tare da qoqari a kan haduwar kan al'umma, ta hanyar rashin yin qememe a cikin al'amarin da ke karbar ijtihadi, da qyamar son galaba da rinjaye don wani qabilanci ko son girma. Dole ne sai mun yaqi wadannan halaye da dabi'u duk kuwa da yake Allah Subhanahu Wa Ta'ala ya halicce mu da su. Muna roqon Allah ya shiryar da mu, ya kuma yi mana jagora. Amin.

Bayan wannan kuma yana da kyau musulmi mu sani, tattare da kasancewar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama mai matuqar son aikata nafiloli da mustahabbai, to kwadayinsa a kan tsare abin da yake wajibi da nisantar haramce-haramce ya fi yawa nesa. Ba mamaki a kan haka, domin kuwa ya fada a cikin Hadisi Qudusi cewa Allah Ta'ala ya ce: ''Bawana ba zai kusance ni da wani abu da na fi so ba, kamar abin da na wajabta masa.'' Shi kuma Annabin ya ce a wani Hadisi: ''Allah ba ya da buqata da Azumin duk wanda ke qarya da aikin jalilci.'' Ko shakka babu, kula tare da kiyaye wadannan Hadisai guda biyu ne kawai, za su sa aikin mutum ya inganta, har ya samu kyakkyawan sakamako. Kuma matuqar ba haka ya yi ba, ko ya ce yana koyi da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne, sai dai mu saurare shi.

Abin da, da yawa daga cikin musulmi ke yi a yau, na mayar da hankali ga kiyaye nafiloli, kamar Sallar Tarawihi, da yawaita sadaqa, alhali ba su kula da alfarmar wasu wajibbai ba, kai sun ma tozartar da wasu; kamar haqqin uwaye da yin Sallah cikin lokacinta, ko shakka babu yin haka babbar hasara ce. Domin kuwa dagewa a kan kare alfarmar uwar dukiya, ga mai hankali, ya fi kokawar neman riba, wato saki sa kama tozo. Sai fa idan an tabbatar da kammalar wajibban, to ba komai.

Allah ya sa mu dace, amin.

Tsayuwar Dare:

Tsayuwar dare wata alama ce ta nagartattun bayi wadanda suka karba sunan bayin Allah. Kuma tarihi ya tabbatar da cewa babu lokacin da Malamai magadan Annabawa wadanda ke fafutukar gyara halayen al'umma suka yi sake da tsayuwar dare, a matsayinsu na masu koyi da Annabi Sallahu Alaihi Wasallam.

Ko ba lokacin Azumi ba, babu daren da ke kamawa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai tsayu a cikinsa ba, balle lokacin Azumin. Akwai Hadissai da dama da ke bayani a kan yanayi da sigogin tsayuwar daren Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci na Azumi. Ga kaxan daga ciki:

Nana Aisha Raliyallahu Anha ta ce:

''Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba ya raka'ar da ta wuce goma sha daya a cikin dare, ko cikin watan Azumi ko waninsa.'' A wani Hadisin kuma take cewa: ''Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi raka'a goma sha uku ne a cikin dare. Sannan idan an kira Sallar Subahin ya yi nafila raka'a biyu 'yan gajeru.'' Ka ga kenan wadannan hadissai biyu na nuna mana cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi raka'a goma sha daya ko sha uku ne kawai a dare.

Bayan wannan kuma, akwai bayanai daban-daban da suka inganta a kan yadda yake gudanar da wadannan salloli. Wanda hakan ke nuna duk yadda mutum ya zabi yi daga ciki, ya yi. Duk da yake an fi so, kai ma ka sassaba, amma kamar yadda Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi, wato ka rinjayar da yin raka'a biyu-biyu kana sallamewa, don shi ma haka ya yi. Allah dai shi ne mafi sani. Amma dai tabbataccen abu ne a shar'ance cewa, babu dalilin da zai sa mutum ya mayar da hankali ga yawaita raka'o'i barkatai a dare, duk da yake kuwa akwai lada a cikin yin haka. Amma da zai tsaya ga tsawaita adadin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi, ta hanyar jan dogayen surori da narkewa a cikin tsoron Allah da tadabburi da zikiri da addu'o'i fai da boye, tare da tabbatar cikar ruku'i da sujada da sauran rukunnan Sallah, to, da hakan zai fi. Ba laifi ba ne, kamar yadda muka fada a baya kadan don mutum ya yi fiye da yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi, amma dai kar a manta cewar da ya yi:

''Ana tsayuwar dare ne raka'a biyu- biyu.'' Ka ga bai qayyade adadi ko siga ba.

Abin da ke faruwa a wannan zamani namu, na sassabawar mutane a cikin adadin raka'o'in Tarawihi, babu laifi a ciki. Domin kuwa ba adadin raka'o'i ba, ko lokacin yin Sallar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai qayyade mana ba. Ya dai kwadaitar da mu ne kawai a kan yin ta. Ka ga ke nan al'amarin na da faraga, ta yadda kowane musulmi ke iya dibar gwargwadon qarfinsa, sharadi kawai shi ne ya yi da kyau. Duk da yake yin yadda Annabin ya yi, ya fi dacewa.

Kuma shi ma wanda ya yi hakan lalle ne ya gudanar da Sallar a cikin cikakkar siga. Allah shi ne masani.

Abin da ya sa muke nanata cewa yin yadda Annabi ya yi ya fi, shi ne, abu ne mai matuqar yiwuwa don tsananin son a yi kandam da lada, musamman irin dabi'ar nan ta dalibai, ta rashin sassauci a komai, a je garin neman qiba a samo rama. Domin kuwa ai qoqarin koyi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na buqatar taskai.

Wata sigar kuma ta tsayuwar daren Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ita ce, ba yakan kwashe tsawon daren yana Sallar ba. A'a, yakan hada ne da karatun Alqur'ani da kuma wani abun, kamar yadda Nana Aisha Raliyallahu Anha ke cewa: ''Ban taba sanin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya karance Alqu'ani a dare daya, ko ya kai safe yana Sallah, ko ya share wata cur yana Azumi in ba Ramalana ba.'' Haka kuma dan Abbas Raliyallahu Anhu ya ce: ''Jibrilu kan zo su yi karatun Alqur'ani tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a kowane dare na Ramalana.'' Ka ga ashe ba kwana ya ke Sallah ba, kenan. Ko shakka babu wannan tsari na Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin wannan ibada, tsari ne mai kyau. Domin kuwa hakan za ta ba shi damar ba jiki da iyalinsa haqqinsu, ya kuma gudanar da ibadar cikin marmari, don kwasar karan mahaukacciya bai dada komai ba. Kuma a ci yau, a ci gobe ai shi ne harka.

Wata siga kuma ta tsayuwar daren na sa, Sallallahu Alaihi Wasallama ita ce, yin ta da yake yi shi kadai ransa, ba tare da jama'a ba, don tsoron kada hakan ya wajabta Sallar ta Tarawihi a kan al'ummarsa. Anas Raliyallahu Anhu ya riwaito, yana cewa: ''Wata rana Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na Tarawihi shi kadai, sai na lallabo na bi shi, wani mutum kuma ya zo shi ma ya bi, da haka dai har jama'a suka taru. Da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ji alamar jama'a bayansa, sai ya dan sassauta sallar. Daga nan bai sake Sallar a waje ba, balle mu bi shi. Da safiya ta yi muka ce ma sa: ''Hala jiya ka ji mu ne bayanka, shi ya sa ka koma ciki? Sai ya karba mana da cewa: ''Lalle na ji ku, shi ya sa ma na yi abin da na yi.'' Haka kuma Nana Aisha Raliyallahu Anha ta ce: ''Wata rana da tsakar dare Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tafi masallaci don yin Sallah, sai wasu Sahabbai suka bi shi. Safiya na yi suka cika gari da labari. A rana ta biyu sai jama'a suka taru sosai, kuma Annabi ya fita don Sallar, suka kuma bi shi. Safiya kuma na yi labari ya qara watsuwa. A rana ta uku, ba sai masallaci ya cika ba!

Aka maimaita irin jiya. To, ai fa rana ta hudu da Annabi ya ga irin yadda masallaci ya cika ya batse, sai ya qi fitowa, har wasu daga cikin mutanen suka rinqa cewa: ''Lokaci ya yi Manzon Allah!'' Annabi na ji ya qyale su. Sai da lokacin Sallar Subahin ya yi, ya fito. Bayan an qare Sallah sai ya fuskanci jama'a, ya kadaita Allah, ya ce, ''Bayan haka, ku sani ba wulakanci ya sa na qyale ku jiya ba. Na ji tsoron ne kada a wajabta maku Sallar dare, ku kasa.''

Haka kuma Abu Zarrin Raliyallahu Anhu ya ce: ''Mun yi Azumi tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama amma, sai da watan ya kai ashirin da uku sannan ya fara Sallar Tarawihi tare da mu. A ranar muka yi ta Sallah har sulusin dare na farko ya shude. A rana ta ashirin da hudu kuma sai ya yi Sallarsa shi kadai. Sai a rana ta ashirin da biyar ya fito muka yi tare, har zuwa tsakiyar dare. Ganin haka sai muka ce masa: ''Ya Manzon Allah me zai hana ka ci gaba da ba mu Sallar nan har daren nan ya qare?.

Sai ya karba mana da cewa: ''Ai duk wanda ya yi Sallar dare tare da liman to, Allah zai ba shi ladar sauran daren da bai sallata ba, matuqar limamin ne ya katse daren.'' Mai riwaya ya ci gaba da cewa: ''Daga ranar kuma bai sake Sallar tare da mu ba. Sai ranar ashirin da bakwai ga watan, a inda ya gayyato mata da mutanen gidansa, muka yi ta Sallah, har sai da muka ji tsoron sahur ya kubce mana.''

Ko shakka babu wannan irin doguwar Sallah da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya jagoranci Sahabbai koyarwa ce ga al'umma, da kuma nuna tsananin qaunarsa ga ita al'ummar, kuma da matsanancin tsoron da yake da shi, na gudun a farlanta masu irin ta, wasu daga cikinsu, su kasa yi, Allah ya kama su da laifi. Wani abin ban sha'awa kuma tattare da haka, su kuma Sahabban sun dage a kan sai ya jagorance su Sallar fiye da yadda yake yi. Shi kuwa Sallallahu Alaihi Wasallama yana ta kakkaucewa, saboda tabbacin da yake da shi na rauni da kasawar al'ummarsa Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan hali da Manzon Allah ya nuna a wannan lokaci ya tabbatar da cancantarsa da kirarin da Allah Madaukakin Sarki ya yi masa a cikin Alqur'ani da cewa: ''Lalle ne, haqiqa, Manzo daga cikinku ya je muku. Yana gudun abin da ke wahalar da ku. Mai kula ne da ku, mai tausayi ne, mai jinqai ga muminai.'' (9:128)

Irin wannan hali na yin tsaye, tsayin daka a kan ganin ya dora al'ummarsa a kan tafarki madaidaici, ba kuma tare da ya takura su ya kai su ga bango ba, balle hakan ta kai su ga fadawa tsantsi. Tabbas irin wannan dabi'a ce ya kamata masu wa'azi da qoqarin gyara al'umma su yi koyi da ita, ko suna kai ga gaci.

Sallar Tarawihi, idan muka nazarci wadannan nassosa da suka gabata, za mu fahimci cewa tana da matuqar girma da daukaka. Kuma gudanar da ita a cikin masallatai Sunnah ne, domin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi haka. 'Yar saurarawar da ya yi kuma, ya yi ta ne don gudun kada a farlanta ta a kan al'umma.

Wafatinsa Sallallahu Alaihi Wasallama ya kawar da wannan fargaba, domin an nade tabarmar sabunta doka.

Tabbatar wannan aminci ta sa halifa Umar Raliyallahu Anhu da ya ga musulmi na yin wannan Sallah daban- daban, sai ya ce a zuciyarsa: ''Me zai hana in tattara su wuri daya, in sa wani alaramma ya limance su. Lalle haka za ta fi dacewa!'' Nan take kuwa sai ya dora wa Sahabi Ubayyu Dan Ka'abu Raliyallahu Anhu wannan nauyi.

Wannan kyakkyawan aiki na Halifa Umar Raliyallahu Anhu ya sami karvuwa matuqa ga Sahabbai. Saboda haka ne ma, aka riwaito cewa Sayyidina Ali Dan Abu Dalib Raliyallahu Anhu wata rana ya fita da dare a cikin watan Azumi, ya ga irin yadda masallatai suka cika da haske, ba kuma abin da ke tashi sai amon karatun Alqur'ani. Ganin haka sai ya ce: ''Allah ya haskaka qabarin Umar xan Haddabi kamar yadda ya haskaka masallatan Allah da karatun Alqur'ani.'' Ka ga da wannan ya tabbata cewa, yin Sallar Tarawihi tare da liman abu ne da ke da falala, kuma duk mai son alheri ga kansa ba zai bari ta wuce shi ba, domin Sunnah ce ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da Sahabbansa. Ya kuma tabbata, kamar yadda muka fada a baya kadan cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, Allah na rubuta cikakkar lada ga wanda ya sallaci sashen daren Azumi tare da liman, matuqar limamin ne ya katse daren amsa ga Sahabban da suka so ya jagorance su Sallar har qarshen dare.

Allah shi ne mafi sani.

Wannan duka na nuna cewa, abin da wasu mutane ke yi na qin daurewa su kammala Sallar Tarawihi tare da limamin da su ke bi, wai don ya wuce raka'a goma sha daya, yin haka abu ne da bai dace ba. Duk da yake qoqarin biyar Sunnah qeqe da qeqe, abu ne da ke da lada a wurin Allah, amma da mutum zai hanqure ya gama Sallar tare da liman, ko da ya wuce wancan adadi, hakan zai qara masa lada ne ba rage ta ba.

Haka kuma wani abin da muke ganin bai dace ba, wanda kuma ya zama ruwan dare a yau, shi ne ciratar da wasu mutane ke yi daga wani masallaci zuwa wani kullum, ko bayan wani dan lokaci. Duk da yake a sane muke da cewa wataqila suna yin haka ne don cin ribar sauraren karatun Alqur'ani da wasu limaman ke yi cikin kyakkyawan sauti fiye da wasu, da sa tsoron Allah da tadabburi da tsawaita Sallah da suke yi, wanda hakan ke taimaka wa mutum ga qara qamewa a kan ayyukan da'a da taqawa. Amma duk da haka da za su zavlbi masallaci daya su riqe, ya fi.

Babban abin da ya sa muka qyamaci wannan dabi'a shi ne da yawa ake fara Sallah ba tare da irin wadannan mutane ba. Ko ma wani lokacin Sallar ta kubce masu baki daya. Sai dai su yi ta su kadai, saboda suna can suna neman masallacin da ake karatu mai dadi. Wani lokaci ko sun sami irin wadannan masallatai, sai ka taras hankalinsu na can ga zaqin karatu ba ibadar ba. Zancen yin tadabburi a cikin ayoyi da ma'anonin Alqur'ani, da kyautata ita Sallar kanta, balle yin tasiri da ayyukan da ta qunsa bai taso ba. Amma kuma duk wannan magana da muke yi ta taqaita ne a kan wanda ke zaune cikin jama'a, yake kuma da halin yin Sallar cikin jam'i. Wanda kuwa ke zaune shi kadai a daji, ko yana a birni amma wani uzuri ya hana shi iya halartar jam'in Tarawihi, to, ba laifi don ya sallace ta shi kadai.

Tabbas kuma zai samu cikakkiyar lada daga wurin Allah. Domin kuwa Allah ba ya tilasta wa rayuwa abin da ba ta iyawa.Batun: Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc