Nazari kan ayoyin da suka yi magana kan azumin Ramadan
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=520

 
Daga Salihu Ishak Makera

Nazari kan ayoyin da suka yi magana kan azumin Ramadan

Godiya ta tabbata ga Allah Mai jujjuya ranaku. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga shugaban masu takawa Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, muna yi wa 'yan uwa Musulmi bushara da gabatowar watan azumin Ramadan. Watan Alkur'ani da ke cike da shiriya ga mutane da bayani da rarrabewa a tsakanin karya da gaskiya. Hakika duk da cewa Ramadan ba ya daga cikin watanni masu alfarma (Muharramai) guda hudu da Allah Ya ambata, amma wata ne mai daraja da martaba da girma saboda a cikinsa aka saukar da Cikamakin Littattafan da Allah Ya saukar ga Cikamakin Annabawa da Manzanni (Alaihimus Salam), Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi wa Alihi wa Sallam). 

Hakika a duk lokacin da Musulmi suka iske kansu a cikin watan Ramadan, rayuwa takan sauya, sukan koma ga Allah ta wajen gudanar da ayyukan da'a iri-iri. Wadanda suke jin nauyin yin Sallah sukan motsa su rika yin ta a kan lokaci tare da jama'a. Masu sharholiya sukan rage ko su bari gaba daya. Saboda shaidanu masu ingiza mutane ga sabo sun shiga mari.
Wannan duk albarkacin Alkur'ani ne, domin da azumin watan Ramadan din da sauran ayyukan da'a duk sun biyo bayan saukar Alkur'ani ne. Saukarsa ce ta kawo duk wasu ayyukan alheri da da'a da dan Adam ke gudanarwa, ya alla a cikin watan Ramadan ne ko a wani watan na daban. 

Kuma Alkur'ani Mai girma ya ba mu labarin dalilin wajabta yin azumin cikin fadin Allah Madaukaki: ''Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke a gabaninku, tsammaninku, za ku yi takawa. Kwanuka ne kidayayyu. To wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai ya (biya) adadi daga wasu kwanuka na daban. Kuma a kan wadanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya kara alheri, to shi ne mafi alheri a gare shi. Kuma ku yi azumin (da wahalar) ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance kuna sani.'' (k:2:83-84).

Fa'idojin da za mu samu daga wadannan ayoyi biyu suna da yawa, daga ciki akwai cewa:

1. Wanda ya samu kansa a cikin watan Ramadan yana cikin hankalinsa kuma baligi, to azumtarsa wajibi ne a kansa. (Jami'ul Bayan, Mujalladi na 3 shafi na 454)
2. Azumi yana daga cikin sabubban samu da ginuwar takawa a zukatan mutane.
3. Mai azumi yana tarbiyyantar da kansa ne kan tsoron Allah da kiyaye dokokinSa. Ta barin abin da zuciyarsa ke so ko sha'awa alhali zai iya boyewa ya aikata, amma sai ya ki saboda ya san Allah Yana ganinsa.
4. Azumi yana takaitawa ko toshe magudanar Shaidan. Domin Shaidan yana gudana ne a jikin dan Adam kamar yadda jini yake gudana. To ta hanyar azumi sai a raunana ikon gudanarsa, sabo ya ragu.
5. A galibi mai azumi ayyukansa na da'a na karuwa, ayyukan da'a kuwa suna daga cikin siffar takawa.
6. Idan mawadaci ya dandani wahalar yunwa, hakan zai karfafa masa gwiwar ya taimaka wa fakirai da ba su da komai, wannan ma siffa ce ta takawa.
7. Allah Ya yi wa mara lafiya da matafiyi rangwame su ci abinci. To amma saboda irin maslahar da ke cikin azumi ga kowane Musulmi, sai ya zamo Ya umace su su rama abin da suka sha a wasu kwanuka na daban, lokacin da ciwon ya gushe ko aka dawo daga tafiya aka samu hutu. (Alfawa'id, Mujalladi na 2 shafi na 272)
8. Azumi yana hana jin dadi da sha'awoyin da zuciya ke ji, fiye da yadda sauran ibadoji suke iya hanawa.
9. Azumi sirri ne tsakanin bawa da Ubangijinsa, babu mai riskar hakikaninsa sai Shi (Allah), don haka ne Allah -Ya ce naSa ne Shi zai saka a kansa,- sabanin sauran ibadoji na zahiri. 

Sai aya ta gaba inda Allah Ya fayyace a wane wata ne za a yi azumin, cikin fadinSa Madaukaki:

''Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Alkur'ani a cikinsa, yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa. To wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na daban, Allah Yana nufin sauki a gare ku, kuma ba Ya nufi tsanani gare ku, kuma domin ku cika adadin, kuma ku girmama Allah a kan Ya shiryar da ku, kuma tsammaninku, za ku gode.'' (k:2:185).

Akwai Hadisai da suke da nasaba da wannan aya kamar: ''Daga Abu Huraira (RA) ya ce Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa.'' (Buhari da Muslim suka ruwaito) Sai ''Daga Abu Huraira (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce, ''Wanda ya yi tsayuwar Ramadan yana mai imani da neman lada an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa.'' (Buhari da Muslim suka ruwaito) Daga Jabir Bin Abdullahi (RA) Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Ku rika cin gajiyar saukin da Allah Ya yi muku (ma'ana matafiyi ya sha azumi ya rama ya fi).'' (Muslim ya ruwaito shi). Daga Muhajjinul Aslamiyyu ya ce: ''Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Lallai mafi alherin addininku shi ne mafi saukinsa, lallai mafi alherin addininku shi ne mafi saukinsa.'' (Buhari ya ruwaito shi). Daga Anas Bin Malik (RA) ya ce: ''Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Ku saukaka, kada ku tsananta, ku zaunar kada ku kora.'' (Buhari ya ruwaito shi).

A wannan aya fa'idojin da za mu samu sun hada da:

1. Falalar watan Ramadan saboda saukar Alkur'ani a cikinsa da kuma kebe shi da daren Lailatul kadr. (Jami'ul Bayan, Mujalladi na na 3 shafi na 448)
2. Wajibcin azumtar Ramadan a kan daukacin mukallafai. (Tafsirul kur'anin Azim Mujalladi na 1 shafi na 206)
3. Sauki ga mara lafiya da matafiyi kan su sha a Ramadan, da wajibcin rama abin da aka sha. (Fathul kadir Mujalladi na 1 shafi na 281-282)
4. Saukin shari'ar Musulunci da rashin tsananinta. (Tafsirul kur'anil Azim, Mujalladi na 1 shafi 206).
5. Shar'anta yin kabbarori a daren Idi da ranarsa domin godiya ga ni'imar Allah ta samun shiriya da Musulunci.

Sai kuma aya ta gaba:

''Kuma idan bayiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to lallai Ni Makusanci ne. ina karba kiran mai kira idan ya kira Ni. Saboda haka su nemi karbawaTa, kuma su yi imani da Ni: tsammaninsu, su shiryu.'' (k:2:186).Batun: Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin