Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al'umma 11
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=531

 
Daga Salihu Is'hak Makera
 
 Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al'umma 11
 
 'Yan uwa Musulmi in za a tuna mun jingine tattaunawa a kan wannan batu kan hakkoki biyar da ke kan gwamnati ko hukuma ta tsare su ga jama'ar da take mulki, saboda karatowar azumin Ramadan da muka kammala a makon jiya. Alhamdulillah, yau za mu dora daga inda muka tsaya, burinmu mu ankarar da Musulmin da ke cikin wannan gwamnati kan nauyin da ke kansu domin mu samu hujja a kansu gobe kiyama domin kada su kasanec hujja a kanmu.
 
 Na hudu: Kyautata tsare nasaba da mutunci:
 
 1. Kwadaiarwa kan yawaita nasaba (haihuwa):
 
 An karbo daga Mu'akkil (RA) ya ce: ''Wani mutum ya zo wurin Annabi (SAW) sai ya ce: ''Lallai ne na samu wata mace ma'abuciyar nasaba da kyau, sai dai ba ta haihuwa, zan iya aurenta?'' Sai (Annabi SAW) ya ce: ''A'a.'' Sannan ya sake zuwa masa karo na biyu, ya hana shi. Sannan ya zo masa karo na uku, sai (Annabi SAW) ya ce: ''Ku auri masu sonku masu yawan haihuwa, domin ni zan yi alfahari da yawanku kan sauran al'ummomi.'' (Abu Dawud ya ruwaito shi a cikin Nikahi, Hadisi na 2050, sai Nisa'i a Nikahi, Hadisi na 3227. Kuma Albani ya inganta shi a cikin Irwa'il Galil, Hadisi na 1784).
 
 Ad-dayyibi ya ce: ''A cikinsa (Hadisin) akwai falalar yawan haihuwar 'ya'ya domin ta haka ne Annabi (SAW) zai cimma burinsa na alfahari da yawan mabiyansa.'' (Sharhin Ad-dayyibi a kan Mushkat, mujalladi na 6 shafi na 226).
Masu kin haihuwa ko masu sukar Musulmin da suke haihuwar 'ya'ya da yawa, ku sani kuna fada ne da addini da kuma wanda ya kawo addinin? Idan kuna tunanin dukiyar daukar nauyinsu ne, sai mu tambaye ku wane ne ke bayar da dukiyar? Wayo ko dabarar mutum ko kuwa Wanda Ya halicci mutum din? Turawa suna yaudararku da talauci don su hana ku haihuwa ne saboda su ga Annabinku (SAW) bai cimma wannan buri ba. Shin idan ba a haihuwa ma yaushe rayuwa za ta ci gaba da gudana? Ko so muke daga kanmu duniya ta kare?
 
 Almannawi ya ce: ''Al'amarin rayuwa ba zai tafi daidai bisa tsari ba, sai jikin dan Adam ya kasance lafiyayye, nasabarsa ta dauwama, kuma su biyu bas u cika sai da wasu abubuwan tsare samuwarsu, wannan kuwa shi ne tabbatuwa da dauwamar nasba (ci gaba da haihuwa). An halicci abinci a matsayin sila na rayuwa aka halicci mata a matsayin muhalli na adana nasaba. Sai dai abin da ake cid a abin da ake aura ba su kebanta da wasu abubuwan da ake ci ko ake haura ta hukuncin fidira. Kuma da an bar abu sakaka ba tare da sanin dokokin kebance komai ba da al'amura sun shiga rudu an yi ta kashe-kashe, kuma hakan ya shagaltar da su daga bin hanya, su fada ga halaka. Amma sai Allah Ya bayyana dokokin da suka shafi dukiya a ayoyin mubaya'o'i da na ginin dauloli da nag ado da sauransu. Kuma daga cikin abubuwan da suka shafi mata akwai ayoyin aure da makamantansu.'' (Faidul kadir, mujalladi na 3 shafi na 242).
 
 2. Kwadaitarwa kan aure:
 
 Imam Buhari ya ce: ''Babin Kwadaitarwa kan aure, saboda fadinSa Madaukaki: ''Ku auri abin da ya yi muku dadi na daga mata…'' (Nisa'i: 3). (Sahihul Buhari Kiabu Nikahi, mujalladi na 9 shafi na 5 tare da Fathul Bari).
 
 Hafiz Ibnu Hajar ya ce: ''Fuskar kafa hujja da ayar ita ce ta zo ne da sigar umarni da ke nuna nema, kuma mafi karancin darajarsa shi ne mustahabbanci, sai kwadaitarwa ta tabbata.'' (Fahul Bari, mujalladi na 9 shafi na 6).
 
 An karbo daga Abdullahi dan Mas'ud (RA) ya ce: ''Annabi (SAW) ya ce mana: ''Ya ku taron samari! Wanda zai iya aure daga cikinku, to ya yi, amma wanda ba zai iya ba, na umarce shi da yi azumi, domin shi garkuwa ne gare shi.'' (Buhari a Kitabun Nikahi, babin fadin Annabi (SAW): ''Wanda yake da ikon aure a cikinku to ya yi aure.'' Hadisi na 5065).
 
 Annawawi ya ce: ''A cikin wannan Hadisi akwai umarni da yin aure ga wanda yake da iko yinsa kuma zuciyarsa ta yi sha'awarsa, kuma wannan ijma'i ne.'' (Sharhin Sahihul Muslim, mujalladi na 9, shafi na 172).
 
 Algazali ya ce game da fa'idojin aure: ''Fa'ida ta farko wadda ita ce asali, shi ne dora aure kuma makasudin a tabbatar da dorewar nasaba, kada duniyya ta wofinta daga jinsin mutum.'' (Ihya'u Ulumid Din, mujalladi na 2 shafi na 75).
 
 3. Gargadi kan dandaka da kwadaitarwa kan aure:
 
 An karbo daga Sa'ad bin Abu Wakkas (RA) ya ce: ''Manzon Allah (SAW) ya ki yarda wa Usman bin Mad'un ya yi dandaka (zama dake mara haihuwa), da ya yi masa izini da mun zama dakakku.'' (Buhari a Kitabun Nikahi, babin abin da aka ki na dandaka da dakewa, Hadisi na 5073).
 
 Alhafiz ya ce: ''Hikimar hana su dandake ita ce don yawaita nasaba (haihuwa) domin a ci gaba da yakar kafirai, ba don haka ba da an yi izini da haka, akwai tsoron karewarsu da yankewar nasaba sai Musulmi su yi karanci ta haka, kafirai su yi yawa wanna kuwa sabanin makasudin aiko Annabi Muhammad (SAW) ne.'' (Fahul Bari, mujalladi na 9 shafi na 21).
 
 Ke nan masu da'awar kayyade iyali suna karfafa wa kafirci ne a kokarin kafirai na ganin sun fi al'ummar Annabi (SAW) yawa. Manufar aiko Annabi (SAW) ita ce al'ummarsa su yaiwata a bayan kasa, addinsa ya shafe kowane addini ya rinjaya a kansa, to idan Musulmi suka rungumi akidar kayade iyali ta yaya za su cika wannan burin a Manzon Allah (SAW)? A yanzu da muke wannan rubutu Musulmi su ne marasa rinjaye a tsakaninsu da kafirai, na daga Ma'abuta Littafi da mushirikai da majusawa da sauran kafirai, wadanda dukkansu Millah (akida) guda ne, duk da bambance-bambancensu.
 
 An karbo daga Anas bin Malik (RA) ya ce: ''Wasu mutum uku sun zo gidajen matan Annabi (SAW) lokacin da aka ba su labari sai suka rika muhawara a tsakaninsu. Suka ce ina mu ina Annabi (SAW) wanda hakika an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa da abin da ya jinkintar? dayansu ya ce: Amma ni zan yi ta yin Sallar dare har abada. dayan ya ce: ''Ni kuma zan yi ta yin azumi har abada ba zan sha ruwa ba. dayan kuma ya ce: ''Ni kuma zan nisanci mata ba zan yi aure ba har abada.'' Sai Manzon Allah (SAW) ya zo ya ce: ''Ku ne kuka je kaza da kaza? To wallahi na fi ku tsoron Allah da yi masa takawa, amma ni ina azumi ina cin abinci, ina Sallah ina barci, kuma ina auren mata. Don haka duk wanda ya kawar da kai daga (kyamaci) sunnata ba ya tare da ni.'' (Buhari a Kitabun Nikahi, babin kwadaitarwa kan aure, Hadisi na 5063).
 
 Alhafiz ya ce: ''Fadinsa ''Ba ya tare da ni,'' idan kawar da kan ya shafi tawili ne da za a yi uzuri ga ma'abucinsa, to ma'anar ''Ba ya tare da ni'' ita ce ba ya kan hanyata, bai lizimtar fita daga Musulunci, amma idan ya kasance bijirewa da ke nufin I'itikadi da fifita aikinsa, to ''Ba ya tare da ni'' na nufin ba ya kan addinina ne, domin I'itikadi da haka nau'i ne na kafirci. Kuma a cikin Hadisin akwai dalilai na falalar aure da klwadaitarwa a kan yin sa.'' (Fathul Bari, mujalladi na 9 shafi na 8).Batun: Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc