AQEEDAN IBN TAIMIYYAH KAN YIWUWAR ALJANI YA SHIGA JIKIN MUTUM
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=542

 
Daga Sheikhul Islam ibn Taymiyyah

AQEEDAN IBN TAIMIYYAH KAN YIWUWAR ALJANI YA SHIGA JIKIN MUTUM

Sheikhul Islam ibn Taymiyyah (Rahmatullahi alaihi) yace: 

' SAMUWAR ALJANNU TABBATACCE NE DAGA LITTAFIN ALLAH DA SUNNAR MANZON ALLAH(SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM). DA KUMA ITTIFAKIN MAGABATAN AL'UMMAH DA LIMAMANTA. HAKA NAN KUMA SHIGAR ALJANI JIKIN DAN ADAM SHIMA TABBATACCE NE DA ITTIFAKIN LIMAMAN AHLUSSUNNAH WAL'JAMA'AH. ALLAH YACE 'WANDA SUKE CIN RIBA BASU TASHI FACE KAMAR YANDA WADDA SHAIDAN YA DIMAUTAR DAGA SHAFE YAKE TASHI' MA'ANA RANAR TASHIN QIYAMA. DA KUMA HADISIN DA YA INGANTA DAGA MANZON ALLAH(SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM) YACE: 'SHAIDAN YANA TAFIYA ACIKIN JIKIN DAN ADAM KAMAR YADDA JINI KE GUDANA A JIKINSA...

Allah sa mudace.

Mummunan Tasirin Kallon Fina Finan Tarihin Musulunci….
Ina kira ga 'yan'uwa musulmai dasu kaurace wa wannan dabi'ah ta kallon fina finan tarihin musulunci wanda ake nuna sahabban annabi(Sallallahu alaihi wasallam) aciki. Ko kuma wasu Magabata masu daraja. 

Hakan yana da matukar hatsari sosai. Musamman ga yara. Ka kiyaye kada ka rinka barin yaranka suna kallon wa'innan fina finai. Domin yana da matukar tasiri azukatan mutane. 

Wanda inhar mutum ya kalli irin wa'innan film din toh aduk lokacin da yaji sunan wani sahabi toh hoton da zai rinka zuwa zuciyarsa shine hoton da ya kalla a wannan film din. Wanda wa'innan masu shirya fina finai irin shiga da sukeyi ta tsabawa ta sahabban da kuma surarsu baki daya… 

Malamanmu na wannan zamani sun nuna haramcinsa . Sai mu kiyaye. Allah kiyayemu.
Batun: Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc