Zababbun tambayoyi kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (5)
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=548

 
Daga Salihu I. Makera

Zababbun tambayoyi kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (5)

Na Abdullahi bin Muhammad bin Abdul'Aziz bin Humaid
Fassarar Imam Ahmad Adam Kutubi

Tambaya: Shin mace tana da wasu kebabbun kaya ne da za ta yi Harama da su, kuma mene ne hukuncinta idan ta yi Harama da fararen kaya?

Amsa: Mace da namiji matsayinsu daya wajen Harama, bai Halatta ta yanke farce ba, bai halatta ta fitar da gashin kanta ba, bai halatta ta rufe fuskarta ba idan ta yi Harama, sai dai idan ta ji tsoron kada maza su dame ta da kallo. Amma game da launin kayan da za ta yi Harama da su ba a kebe wasu kaya na musamman ba. Za ta iya Harama da kowane irin kayanta kore ko fari ko baki, koma dai wane launi ne, kawai dai ba a so ta yi Harama da kayan ado wadanda za su dauki hankali, domin wajen Allah ta zo kamata ya yi, ta yi shiga takankan da kai.
Tambaya: Shin ya halatta mace ta yi harama alhali tana sanye da kayan ado?

Amsa: Babu laifi mace ta yi Harama tana sanye da zobe ko a hannunta akwai wani abu na Zinare, Haramarta ta yi sai dai ana so ta rufe shi kada ta bayyana adonta.

Tambaya: Shin ya halatta mace ta yi amfani da magani don kada haila ta zo mata da azumi ko a kwanakin Hajji?

Amsa: Babu laifi, ya halatta amma da sharadin kada ya zama zai cutar da mace don ta yi amfani da shi. Malamai suna fada a karshen fasalin haila cewa babu laifi don mace ta yi amfani da maganin da zai tsayar mata da haila matukar dai yin amfani da maganin ba zai haifar mata da wata cuta ba, ko kuma magungunan hana daukar ciki, ko masu hana maniyyi gudana don kada a dauki ciki na wasu kwanaki sanannu, dukkan wadannan babu laifi insha Allahu.

Tambaya: Mace ce ta shiga Makka ba ta yi Harama ba saboda tana haila, mene ne hukuncin haka?

Amsa: Idan ta zo da niyyar yin Umara ne to bai Halatta ta shiga Makka ba tare da ta yi Harama ba, sai dai ta yi Haramar koda tana cikin hailar, domin haila ba ta hana Harama, sai ta yi Harama daga Mikati, ta tsabtace jikinta gwargwadon iko, ta gyara gashinta ta yanke farcenta, ta yi Haramar ta ce: ''Labbaika Umratan'' wato:

''AmsawarKa zan yi Umara.'' Babu ma laifai don ta yi amfani da turare kadan a jikinta don ya kawar da wari mara dadi, idan tai so Makka za ta kasance cikin Haramarta idan ta yi tsarki sai ta yi wanka ta yi tsarki ta je ta yi dawafi da Safa da Marwa, ta yanki gashin kanta shi ke nan Umararta ta cika. Wannan shi ya kamata ta yi, sai dai kai a tambayarka ka ce, ta riga ta shiga Makka ba tare da Harama yanzu ke nan mene ne hukuncinta? Sai muce da kai: Matukar ta shiga ba tare da Harama ba, idan ta yi tsarki, sai ta dawo wajen Mikatin garinsu ta yi Harama daga can babu komai a kanta. Amma idan ta yi Harama daga Makka ko daga Tan'im, to sai ta yi Kaffara, amma Umararta ta yi.

Tambaya: Mace ce ta zo daga Jidda tana jini, wasu suka ce da ita za ta iya yin niyyar Umara duk da ba ta da tsarki, sai ta yi niyya tun kafin ta yi wanka. Da ta iso Makka ta yi wanka ta taje kanta, shin tana da laifi tunda ita ba ta sani ba? Saboda na ji wani malami ya ce sai ta yi kaffara?

Amsa: A'a babu kaffara a kanta, sai dai ba za ta yi dawafi ba, ba za ta je Ka'aba ba sai ta samu tsarki, amma haramarta ta yi. Sai dai bai kamata ta yanki gashin kanta ba, amma abin da ya faru da ita na faduwar wani abu daga gashin kanta wannan babu komai, saboda ta yi ne cikin rashin sani, sai ta ci gaba da zama cikin Haramarta, idan ta samu tsarki ta gyara jikinta ta yi wanka ta je ta yi Umara ta yi dawafi da Safa da Marwa, babu komai a kanta in Allah Ya yarda.

Tambaya: Shin mai haila za ta yi Harama a Mikati bayan tana cikin jini, ta ajiye kayan Hiraminta sai bayan ta samu tsarki sai ta sanya su, ta yi harama daga gidanta sannan ta cika Umararta, ko kuwa dole ne idan ta samu tsarki sai ta koma Mikati ta yi sabuwar Harama? 

Amsa: Lamarin duk bai kai haka ba, ta yi haramarta a Mikati idan tana haila, idan ta samu tsarki sai ta yi Hirami da kayan jikinta, ko ta canja wasu ko ta wanke su idan wata najasa ta taba su, ta yi dawafinta ta yi Sa'ayi.Batun: Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi