Me Ke Kawo Rauni Ga Musulmi?
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=561

 
Imam Abdulmumini Ahmad Khalid, Masallacin Badar, Kubwa, Abuja

Me Ke Kawo Rauni Ga Musulmi?

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna neman Ya tsare mu daga sharrukan kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya. Ina kuma shaidawa Annabi Muhammadu (SAW) bawan Allah ne, kuma ManzonSa ne. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da 'yan dakinsa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsu, amin.

Bayan haka, ya bayin Allah! Ku ji tsoron Allah. Ku nemi shiryarwarSa, domin wanda Allah Ya shiryar babu mai iya batar da shi. Ku sani cewa Annabi (SAW) ya fadi irin raunin da Musulmi za su samu kansu a ciki a karshen duniya. Da taron dangin da kafirai za su yi musu da zaman da Musulumi za su yi na kara-zube, babu karfi, babu shugabanci.

Sai ga shi duk wanda yake rayuwa a yau babu abin da zai ce, illa ya ce ''Annabi (S.A.W) ya yi gaskiya.''
Da farko makiya sun kyamatar da mu addininmu, suka canja alkiblar tunaninmu, muka daina koyi da Annabi, (SAW) bayan Allah (SWT) Ya ce: ''Kuna da kyakkywan abin koyi daga rayuwar Manzon Allah.'' (Al-Ahzab:21). Sai suka fuskantar damu ga rayuwa irin ta Yahudu da Nasara. Maganganunmu, tsarin gidajenmu, sallamarmu, bikin aurenmu, kasuwancinmu da duk mu'amalarmu irin tasu ce. Sun kyamatar da mu harshen addininmu. Yau mai jin Larabci ba ya burgewa, wanda ba ya jin Ingilishi shi ne bagidaje, komai Larabcinsa da sanin addininsa. Sun raba mu da Alkur'ani. Mafi yawan masu ilimin zamani a yau ba su iya karanta komai daga Alkur'ani, kuma ba su jin cewa suna cikin hasara, tunda dai suna jin Ingilishi. Ba su mutunta makaranci da makaranta Alkur'ani, amma suna mutunta Bature da harshen Ingilishi ko Turanci. An sanya musu girman kai da kin yarda da gyara a addini.

Misali an taba yin kokarin gyara wa wani yadda ake tsayuwar Sallah, sai ya ce: ''Kai ni fa Darakta ne a ma'aikatarmu, kuma ni ne shugaban kwamitin masallacinmu.'' Wato, yana shugabantar masallaci amma bai san yadda ake tsayuwa a masallaci ba, kuma ba zai yarda a gyara masa ba.

Abu Sa'id Al-Khuduriy (RA) ya ce: Annabi (SAW) ya ce: ''Lallai ne za ku bi tafrkin wadanda suka gabace taku da taku, har idan da za su shiga ramin damo sai kuma kun shiga.'' Sai suka ce: ''Kana nufin Yahudu da Nasara?'' Ya ce: ''To su wane ne in ba su ba?'' (Buhari da Muslim suka ruwaito).

Wannan Hadisi yana nuna irin tsananin koyi da kafirai da Musulmi za su yi. Kuma duk wanda ya lura da yadda Musulmi suke a yau zai tabbatar da haka.

Haka idan mutum ya karanta Hadisin Sauban wanda Abu Dawud ya ruwaito, inda Annabi (SAW) ke cewa: ''Al'ummomi (kafirai) sun yi kusa su yi muku taron-dangi kamar yadda karti majiya yunwa suke taruwa kan kwanon abinci.'' Sai suka ce: ''Shin a lokacin saboda ba mu da yawa ne?'' Ya ce: ''Kuna da yawa amma yawanku kamar yawan kumfar ruwa ne (wato ba ku da karfi), saboda Allah Zai cire wa abokan gabanku tsoro ko haibarku a cikin zukatansu, kuma Ya sanya muku rauni a zukatanku…. Saboda sonku ga duniya da kinku ga mutuwa.'' Annabi (SAW) ya yi gaskiya.

Ku dubi halin da Musulmi suke ciki a yau. Babu shugabanci na addini, babu hadin kai a tsakaninsu. Duk duniya haka muke sai muka rungumi sarakunan gargajiya muka ce su ne shugabannin Musulmi. Wani da ya ji ina fadin haka sai ya ce domin mene ne na ce haka? Ai sarakunan Musulunci ne. Sai na tambaye shi na ce, su wane ne sarakunan Musulunci? Ya ce su ne. Na ce su wane ne sarakunan gargajiya? Ya ce dai sun ne. Na ce da wace irin gaisuwa ake gaishe su a fadojinsu? Ya ce, na gargajiya. Na ce idan ka je fadar sarki ka yi masa gaisuwar Musulunci zai karba? Ya ce, ai sai fadawa su ladabtar da mutum idan ya yi haka! Na ce mene ne mastsayinsu a wurin hukuma ? Ya ce a mastsayin sarakunan gargajiya suke. Na ce bayan sanar da ganin wata wane aiki suke yi ga Musulunci? Ya ce babu. Na ce to, ka yi wa kanka adalci, ka daina yaudarar kanka. Kada ka musanta karantarwar wannan Hadisi.

Allah (SWT) Ya ce : ''Wadanda suka kafirta sashinsu masoya sashi ne. Idan ku (Musulmi) ba ku yi haka ba (ba ku nuna soyayya a tsakaninku ba), fitina da fasadi za su yawaita a bayan kasa.'' (Anfal:73).

Lokacin da Annabi (SAW) ya bar duniya ba a yi jana'izarsa ba, sai da aka zabi shugaban da zai jagoranci al'amurar Musulmi. Kuma duk wani shugaba na Musulunci idan aka shugabantar da shi sai an yi masa mubaya'a. Kuma Annabi (SAW) ya nuna Musulmi koda mutum biyu ne za su yi tafiya su shugabantar da daya daga cikinsu.

Amma ku duba halin da Musulmi suka shiga a garin Jos da Jihar Filato, babu wanda ya yi magana a mastsayinsa na shugaban Musulmi, saboda babu. Ga abin da ke faruwa a Gaza kasar Falasdinu duk duniya babu wanda ya yi magana a matsayinsa na shugaban Musulmi, sai sauraron shugabannin kasashen Larabawa ake yi ko za su yi magana da sarakunan gargajiya na kasashen Larabawa. Kuma babu wanda ya ce wani abu.

Mu yi tunanin hanyoyin samun shugabannin Musulunci domin shi ne kawai mafita. Kuma mu nemi ilimin sanin addini, kuma mu yi kishin addinin shi ne hanyoyin samun shugabanni Musulmi.

Allah Ya daukaka Musulunci da Musulmi, Ya kaskantar da kafirci da kafirai. Allah Ya ba Musulmin Gaza nasara a kan Yahudawa, Allah Ya tabbatar da duga-dugansu. Kuma Allah Ya shiryar da mu, amin.Batun: Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar