Jan Damara Domin Samar Da Kyakkyawan Shugabanci Mai Adalci a Najeriya
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=566

 
Daga Hudubar Injiniya Isma'il M. Chindo Gotomo - Masallacin Juma'a na Gwadangaji Intermediate kuarters, Birnin Kebbi

Jan Damara Domin Samar Da Kyakkyawan Shugabanci Mai Adalci a Najeriya

Godiya ta tabbatar ga Allah, Wanda Ya yi baiwa ga bayinSa masu imani ta hanyar tayar da Manzo daga cikinsu, wanda yake karanta musu ayoyinSa (ayoyin Allah), kuma yana tsarkake su, kuma yana sanar da su Alkur'ani da hikimarsa (Sunnah), alhali kafin haka, suna cikin bata bayananniya. Ya Allah! Ka yi salati da sallama ga wannan Annabi da jama'ar gidansa da sahabbansa baki daya.

Bayan haka, yayin da shekarar Miladiyya ta 2015 take ta kusantowa, wato shekarar da aka shata don a gudanar da babban zaben kasa a kasar nan insha Allah, jama'a daban-daban, kama daga 'yan jarida zuwa sauran jama'a (masu fatar alheri), ba su gushe ba suna bayyana babbar fatarsu ta ganin cewa al'amurra sun gyaru; wato sun canja daga munin da suke ciki a halin yanzu zuwa kyautatuwa insha Allahu.

Ko ba komai, kasar nan ta Najeriya Allah Ya yi mata baiwa masu yawa fiye da kasashe masu yawa a duniyar nan! Allah Ya ni'imta mu da makekiyar kasa mai albarka. Ga korammu, ga itatuwa, ga tsirrai, ga yanayi mai albarka (kusan komai ana iya nomawa a cikinta) ga kuma ma'adinai (masu dauke da sinadaran) da ake bukata domin masana'antu da kere-kere iri – iri. Bayan wannan kuma ga albarkar yawan jama'a - masu basira, masu hazaka! Kai! ''Ko kun kidaya ni'imomin Allah ba za ku iya lissafe su ba!'' (Suratun-Nahl:18).
Amma kuma kash! Duk da wadannan ni'imomi, wata babbar matsala (da ke damun kasar) ita ce (ta) rashin kyakkyawan shugabanci. Wannan matasalar ta hana a ci amfanin duk wadannan ni'imomi yadda ya kamata; ta ma hana a ga hasken wasu ni'imomin. Mun rasa shugabanci nagari, wanda ke gudun cutar da bayin Allah, talakawa – saboda tsoron gamuwa da Allah. Mun rasa shugabanci mai hukunci da gaskiya da adalci. Haka kuma ba maganar janyo wa talakawa alheri da kuma kare su daga sharri (babu tsaro). Ana yin abubuwa ne a kan ganin dama da ra'ayi kawai…To, fatar 'yan kasar nan ita ce a samu canji daga wannan mummunan yanayi!

Muna cikin yanayin da yake kowane irin zalunci ke gudana; ga shisshigi da ketare iyaka; ga fasadi (lalacewar al'amurra, cin hanci da rashawa) ya shiga kusan ko'ina! Sa'an nan, wal'iyazu billahi, ga kashe-kashe a Najeriya sun munana! Kai, ina tunawa har wani dan jarida mai suna Gbenga Omotoso ya fada a jaridar ''The Nation'' ta ranar Alhamis 9 ga Janairu, 2014 a shafin karshe, cewa (da Turanci):

''Since the Cibil War, this is the first time Nigerians habe witnessed so much bloodshed in the land''.

Ma'ana: ''Tun bayan Yakin Basasa, 'yan Najeriya ba su taba ganin matsanancin zubar da jini irin wannan da ke gudana a halin yanzu ba a kasar nan.''

Don haka, ya ku 'yan uwa! Wajibinmu ne mu yi kokarin ganin cewa al'amura sun canja, sun gyaru! Lallai ne Allah ba Ya canja yanayin da mutane suke ciki sai sun canja abin da yake ga zukatansu (Suratur Ra'ad:11). Kuma kada mu taba tunanin cewa wai wata Amurka, ko wata Tarayyar Turai, ko wata Majalisar da ake cewa ta dinkin Duniya su za su zo su yi muna magani! Ko kusa! In gaskiya ne, to, yaya aka yi da 'yan matan Chibok? Don haka, gyaran kasar nan aikinmu ne. Dole ne, mu za mu tsaya mu yi shi da kawunanmu! Allah Ya taimake mu.

Hanyoyin gyara:

Ga shawarwari gare mu, a matsayinmu na daidaiku da kuma jama'a, domin samun gyara, musamman a kan siyasar (zaben) da aka fuskanta in Allah Ya so. Wadannan shawarwarin sun shafi mazanmu da matanmu, yaranmu da manyanmu, malamai da masu wa'azi, shugabannin kungiyoyin addini da gwamnoni da sauran masu mukaman shugabanci, sarakuna da sauran shugabannin jama'a, da sauran masu fada a ji; su fadi gaskiya, kuma su tsayu a kanta. Su nisanci kwadayi da sauran munanan halaye ababen zargi, masu janyo kaskanci. Su tuna da gyaruwarsu ne al'umma suke gyaruwa!

'Yan siyasa baki daya da 'yan boko gaba daya da sauran masu ji da wayewa. Wannan kuma ya hada da dukkan nau'o'in ma'aikatan Hukumar Zabe da jami'an tsaro dukkansu da duk masu aiki irin nasu su ji tsoron Allah; kada su kai jama'arsu ga mahalaka saboda abin duniya mai karewa! Kuma a rika sara ana duban bakin gatari. Misali, komawar da kaikayi ya yi ga mashekiya a Jihar Adamawa bayan tsige Gwamna Nyako, ba-ji-ba-gani, abin wa'aztuwa ne.

'Yan jarida, su yi amfani da hikima da baiwar da Allah Ya ba su ta iya motsar da mutane da karkatar da tunaninsu, zuwa ga samun gyara da kuma kyautatuwar al'amurra. Su tuna sakamakon aikinsu yana ga Allah.

Samari maza da mata; su tuna idan abubuwa ba su gyaru ba, to, za su fi kowa dandana kudarsu (gane kuskurensu) a nan gaba. Don haka su yi aiki domin kawo gyara.

Mabiya malamai da mambobin kungiyoyi (dukkansu) talakawa da sauran jama'a baki daya; a tuna cewa fa, a Musulunci babu biyayya ga duk wani mutum wajen saba wa Mahalicci. Kuma mun sha ji game da Imam Malik (R.H) yana cewa ''Zancen kowa, akwai abin dauka, akwai abin ajewa in ban da na Manzon Allah (SAW).'' Kuma, kamar yadda Shehu Usmanu (Rahimahullahu) ya ce, ''…Addini an gina shi ne a kan basira ga mutane masu basira.'' (Usuluddini). Don haka, a Musulunci, ba ido-rufe ake bin shugaba ba. A'a, ana bin shugaba ne ga abin da ya dace da Shari'a, ba abin da zai kai jama'a ga mahalaka ba. Allah Ta'ala Ya sa mu fahimci haka, kuma Ya agaje mu, amin.

Ya Allah! Ka ba mu abu mai kyau a duniya, kuma Ka ba mu abu mai kyau a Lahira, kuma Ka kare mu daga azabar Wuta. Ya Allah! Ka kyautata sha'anoninmu dukkansu, kuma kada Ka dogarar da mu a kan kawunanmu koda da kiftawar ido ne.

Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Za a iya samun Injiniya Isma'il M. Chindo Gotomo ta:

Email: ismailgotomo@yahoo.comBatun: Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai