Cutar Cin Mutuncin Mutane (2)
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=583

 
Daga Sheikh Abdurrahman Sudais, Babban Limamin Masallacin Ka'aba

Cutar Cin Mutuncin Mutane (2)

Ku sani –Allah Ya kubutar da ni da ku – lallai ukubar cin mutunci tana da muni da gaunin da take girgiza farillai, masu hankali ke tsoro daga gare ta. An karbo daga Anas bin Malik (RA) cewa: ''Lallai Annabi (SAW) ya ce: ''Lokacin da aka yi mi'iraji da ni, na wuce ta wurin wasu mutane suna da farata na bakin karfe, suna yayyage fuskokinsu da kirazansu. Sai na ce: ''Su wane ne wadannan ya Jibrilu?'' Sai ya ce: ''Wadannan su ne masu cin naman mutane, suna cin mutuncinsu.'' Abu Dawuda ya ruwaito a Sunnan dinsa.

Al'ummar Musulmi! Gaskiya hakki ne a kan kowane Musulmi da Musulma idan ya ji ana cin mutuncin wani dan uwansa ya ja hankalinsa (mai cin mutuncin), ya kwabe shi, ya shiryar da shi, ya yi masa nasiha, ya hana shi. Ya kama hannunsa cikin kyautatawa ya shiryar da shi ya gargade shi kan aiki da jita-jita da karya da suke jawowa a fada ga halaka da yaduwar hassada. Cin mutuncin wasu bai haifar da komai sai halaka da barna. Manzon Allah (SAW) yana cewa: ''Wanda ya ci mutuncin dan uwansa za a yi masa suturar wuta (a Lahira).'' Ibn Abu Shaiba ya ruwaito shi a cikin Musnaf dinsa.

Ya jama'ar Musulmi! Domin a kubutar da jama'a daga illar wadannan mutane, babu makawa a kame hannuwansu da rusa manufofinsu da dabbaka hukunce-hukuncen shari'a a kansu, har ya zamo mutuncin mutane bai zama wata iyaka abar halattawa ga kowane jaki da doki ba, bai zamo abin ketawa da takewa ga kowane wawa da gailo ba.
Ta hanyar yin haka ne za mu gina wa kanmu da al'ummarmu tushen zaman lafiya na gaskiya, soyayya da kauna su samu wurin zama a tsakaninmu, kyawawan dabi'u da 'yan uwantaka su ginu, kuma cikin izinin Allah mu kawar da kyamar juna da cutarwa, a samu al'umma mai inganci, mai makoma tagari da zukata masu tsarki da salama da jama'a mai karfin gwiwa da azama. Domin dunkulewar al'umma yana tare ne da dinkewar daidaikun jama'arta, dinkewar daidaikun jama'arta yana damfare ne da haduwar zukatansu da daukakar himmarsu da martabarsu da salamarsu da hadin kansu.

Wannan shi ne abin fata, wannan ake son gani, kuma muna fatar samun taufiki na gaskiya da aiki na ikhlasi daga Allah.

Ina neman tsarin Allah daga Shaidan jefaffe. ''Ya ku wadanda suka yi imani! Ku nisanci abu mai yawa na zato. Lallai sashin zato laifi ne. Kuma kada ku yi rahoto (leken sirri), kuma kada sashinku ya yi gibar sashi. Shin dayanku na son ya ci naman dan uwansa yana matacce? To ku ki shi (cin naman). Kuma ku bi Allah da takawa. Lallai Allah Mai karbar tuba ne, Mai jin kai.'' (k:49:12)

Allah Ya yi mini albarka da ku a cikin bin Alkur'ani da Sunnah. Ya amfanar da mu da abin da ke cikinsu na ayoyi da ambato da hikima. Ina fadin wannan magana tawa, ina neman gafarar Allah Mai girma da daukaka a gare ni da ku da sauran Musulmi daga dukkan kuskure da laifi, ku nemi gafararSa, ku tuba gare Shi, lallai ne Shi Mai yawan gafara ne, Mai jin kai.

Huduba ta Biyu:

Godiya ta tabbata ga Allah majibincin masu takawa. Kuma na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, kuma na shaida lallai Annabinmu Muhammad bawan Allah ne kuma ManzonSa, abin koyin masu neman tsarkaka, tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka ma'abuta rabo da sahabbansa masu da'a masu tsere wajen aikin kwarai da wadanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.

Bayan haka, ya bayin Allah! Ku bi Allah da takawa a boye da fili, ku kiyaye mutuncin Musulmi da mafifitan shiriya da sunnoni sai ku rabauta da mafiya girman albarkoki da rahamomi da kyaututtukan baiwa daga Allah.

'Yan uwa a cikin imani! A cikin shiriyar Ubangiji da manhajar gyara ta Alkur'ani muna da magani mafi dacewa ga gubar nan ta cin mutuncin mutane. Alkur'ani ya dora Musulmi a kan kame harshe da tsarkake shi, wannan yana cikin fadin Allah Madaukaki cewa: ''Don me a lokacin da kuka ji shi (zancen mutuncin wasu), muminai maza da muminai mata ba su yi zaton alheri game da kansu ba, kuma suka ce, ''Wannan kiren karya bayyananne?'' (k:24:12). Ta yin haka sai a kubuta daga shakkun zukata, a tsarakaka daga hassada da kyara, a wayi gari mutunci ya tsaru daga giba da annamimanci da kiren karya da shaidar zur.

Haka ma ya zo a cikin magana mai inganci mai fasaha daga masoyinmu mai cetonmu (SAW): ''Musulmi shi ne wanda Musulmi suka kubuta daga (cutarwar) harshensa da hannunsa.'' Buhari da Musulim suka ruwaito shi. Kuma da haka sai kyawawan dabi'u su cika, karimci ya yadu, a wayi gari 'yan uwantaka da soyayya su bunkasa su yi karfi. Hadin kai ya ginu ya karfafa a tsakanin jama'a. Son Allah ya samu wurin zama a zukatanmu daram. Wannan a wurin Allah ba abu ne mai wahala ba.

Da wannan sai ku yi salati da taslimi a bisa Annabi masoyi mai girma, mai matsayi madaukaki da girma, mai daukakar girma mai karimci kamar yadda Maulanmu Mai jin kai Ya umarce ku a cikin Abin saukarwa Mai hikima, (Alkur'ani), Wanda Ya girma Ya daukaka Ya ce: ''Lallai ne Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.'' (k:33:56). Shi kuma (SAW) ya ce: ''Wanda ya yi min salati sau daya, Allah Zai yi masa salati sau goma a madadinta.''

Allahumma faj'al salatuka wassalamu muda'afan, Linabiyyikal mukhtari khairi mushaffa'i.

Almusdafal hadi ilaika Muhammadin, Wal ali wal as'habi summat tabi'i.

Ya Ubangiji! Ka kara tsira da aminci da albarka a bisa Bashirun Nazirun kuma Sirajun Munir (SAW) da alayensa da sahabbansa.Batun: Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai