MAFITA GA CUTAR EBOLA
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=585

 
Daga Nibras Muhammad

MAFITA GA CUTAR EBOLA

Hasbunallah Wani'imal wakeel.

‘yan'uwa Musulmai muji tsoron Allah mu daina yayata jita jita, abinda bai faru ba mu rinka fadansa. Domin hakan Annabi(sallallahu alaihi wasallam) ya hana. Annabi(sallallahu alaihi wasallam) yace ان الله حرم عليكم قيل وقال..

‘Allah ya haramta muku ance yace'.

Sannan kuma yada irin wa'innan jita jitan yana tsoratar da musulmai, wanda hakan shima haramun ne. Abinda ya dace mutum yayi shine ya kame bakinsa ga barin duk abinda zai tada wa al'ummah hankali. Domin rubutun dazakayi ka tura bakasan har ina zata kai ba.

Mukiyaye ya zamto duk abinda zamu rubuta gaskiyane kuma akwai amfanin rubutashi.
Sannan ita wannan cuta ta ebola annoba ce wadda Bazata shafi mutum ba sai Allah ya kaddara masa. Ya kamata mutane mu hankalta wannan cuta bazata taba shafanka ba sai Allah ya kaddara maka. Allah yace…

ﻗﻞ ﻟﻦ ﻳﺼﻴﺒﻨﺎ ﺇﻻ ﻣﺎ ﻛﺘﺐ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻨﺎ ﻫﻮ ﻣﻮﻻﻧﺎ ﻭﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻠﻴﺘﻮﻛﻞ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻮﻥ.

Ka ce: ''Bãbu abin da yake sãmun mu fãce abin da Allah Ya rubũta sahõda mu. Shĩ ne Majiɓincinmu. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara.''

Sannan kuma koda ta shafeka ka mutu riiba ce gareka. Domin sananne ne a addinin musulunci wanda ya mutu a annoba shahidi ne. To me kake bukata a duniya ya wuce kayi mutuwar shahada? Ya dace mu jaddada imaninmu ga Allah mudogara gareshi mudaina Ruda kanmu. Allah shi yake karemu ba wani ba.

Ina Mafita Ga wannan cuta?.

Mafita Ga wannan cuta shine dogaro Ga Allah sannan Da addu'a. Mu rinka zikirin safe da yamma. Sannan yana daga cikin zikirin da annabi ya koyar mutum yace safe da yamma sau uku.

بسم الله الذي لا يضر مع اسمه شيئ في الارض ولا في السماء وهو السميع العليم.

Bismillahillazi laa yadurru ma'asmihi shai'un fil ardi wala fissama wahuwassami'l aleem.

Annabi yace duk wanda Ya karanta wannan Allah zai kareshi.

Murinka karanta wannan bisa yaQini. Sannan kuma wata addu'a mai mahimmanci itace.

Hadisi yazo.

عن ‏ عمر ﺑﻦ ﺍﻟﺨﻄﺎﺏ ﻭﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﻗﺎﻻ :
ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ – ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ – ‏( ﻣﺎ ﻣﻦ ﺭﺟﻞ ﺭﺃﻯ ﻣﺒﺘﻠﻰ ﻓﻘﺎﻝ : ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﻋﺎﻓﺎﻧﺎ ﻣﻤﺎ ﺍﺑﺘﻼﻙ ﺑﻪ ﻭﻓﻀﻠﻨﻲ ﻋﻠﻰ ﻛﺜﻴﺮ ﻣﻤﻦ ﺧﻠﻖ ﺗﻔﻀﻴﻼ ﺇﻻ ﻟﻢ ﻳﺼﺒﻪ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺒﻼﺀ ﻛﺎﺋﻨﺎ ﻣﺎ ﻛﺎﻥ.

‘Manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam) yace: ‘Babu wani mutum da zai ga wanda aka jarraba sai yace : ‘Alhamdulillahi llazi afana mimmabtalaka bihi wafaddalani ala kasirin mimman khalaka tafdilan. Face wannan musiba bazata sameshi ba komin yaya take.

Wannan addu'a ya dace murinka maimaitawa ba yawan surutai da ruda mutane ba.. Allah kiyayemu wa'inda suka kamu kuma Allah basu lafiya. Sannan in Allah ya jarrabeka da wannan cuta zaka iya amfani da habbatussauda'u.

حبة السوداء.

Domin annabi yace tana maganin komai banda mutuwa. Sai ka gwada bisa karfin imaninka Allah ya iya Tserar dakai. Allah sa mudace. Wassalamu Alaikum.Batun: Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai