KOWA YA SHUKA ALHERI ZAI GA ALHERI
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=586

 
Daga Sheikh Aliyu Said Gamawa

KOWA YA SHUKA ALHERI ZAI GA ALHERI

Alheri danko ne baya faduwa kasa banza, yana da kyau kowa ya natsu tsam yaga shin a rayuwata wani alheri na taba shukawa don kaina da iyalaina da sauran jama'a masu zuwa bayana?
Akwai hanyoyi da yawa da alherin ka zai kai har ga wanin ka tun kana raye da bayan ka koma ga Allah, kai har ma sauran dabbobi, kwari, tsuntsaye da sauran halittun Allah da ke rayuwa a doron kasa.

Ina bamu shawara mu yi tanadin samar da itatuwan dashe don mu dawo da bishiyoyi a gidajen mu, garuruwan mu, da dazuzzukan mu.

Anan kowa nada damar bada gudumawa a nasa matakin ta dayan hanyoyi hudu:
1. Kati tanadi na musamman na dan itace, ka dasa ka reneshi a hankali in ya girma aje a dasa.
2. Ka sayi adadi mai yawa na bishiyoyi ka rabawa al'umma su dasa, ko aje gonaki da cikin daji a dasa cikin damana.

3. A yi amfani da duk wata dama ta shugabanci a samar da irin itatuwan dasawa a rabawa al'umma, kuma a dasa a duk inda ya dace don raya al'ummar mu.

4. Kayi tanadin irin bishiyoyi daban danab kaje ka watsa a cikin daji da fatan a hankali ruwan damana zai fitar dasu har su girma.

Hakika kyautatuwar muhalli na daga cikin hanyoyin samun rayuwa mai dadi cikin ni'imar dausayi da samun albarkatun kasa da kare kwararowar hamada da rage saurin kafewar mashayar dabbobi a daji.

Pls yana da kyau mu dauki matakin bai daya na dasa bishiyoyi a gidaje da gonakin mu, sannan hukumomi su taimaka mana wajen samar da isassun irin bishiyoyi a dasa mana su a dazuzzukan mu da muhallan mu.

Tabbas akwai alheri mai yawa cikin samar da jerin bishiyoyi a kusa da jama'a, da bakin manyan titunan mu, da kusa da manyan rafuka, da gabar koguna da cikin tabkunan mu don su taimaka wajen dadewar ruwan bai kafe ba a daji don amfanin mu da dabbobin mu.

‘Yan uwa munyi sakaci fa, kuma muna yiwa kan mu illa ta hanyar sare bishiyoyi ba dasawa, muna karya dokar hukuma, kuma muna kusanto da hamada zuwa muhallan mu da kan mu, yanzu fa duk dazuzzukan mu sun zama fayau kamar tsakiyar gari, har namun daji da dabbobin mu sun shiga wahalar rayuwa na rashin abinci da abin sha, ‘yan uwan mu mazauna daji da masu sana'ar kiwo, da ‘yan farauta, da masu suu na kifi, da masana masu nemo magani daga itatuwa duk mun durkusar da su sun koma laluben yadda zasu dora targaden da rashin bishiyoyi da bushewar daji yayi mana.

Tarihi ya nuna cewa iyayen mu a can baya sun mana tanadin alheri wajen dasa bishiyoyi a gida da daji don amfanin mu masu zuwa bayan su, sai yau gashi mu kuma mun sare shukan da sukayi mana, dazukan sun bushe karaf tun akan idon mu, to yaya na bayan mu masu zuwa, pls wani tanadi muka yi musu?? Ina fatan mu yiwa kan fada, mu dawo da dabi'ar samarwa kan mu da dazukan mu isassun bishiyoyi.

Mu sani fa duk wanda ya dasa bishiya kuma yayi mata hidimar kulawa da bayin ruwa to tabbas yana da ladan rayuwar ta, da ladan wanda yasha inuwa, ko yaci ‘ya ‘yan ituwan ta, ko aka amfana da iccen wajen magani ko duk abinda ya dace. Dasa bishiya sadakace mai gudana da zaka na samun lada tun kana raye da bayan ka koma ga Allah. Dan uwa da za'a baka zabin aiki na karshe a rayuwar ka yana da kyau ka zabi a baka dama ka dasa bishiya don yawan ladan wannan aiki.

Yana daga hanyoyin raya al'umma ta yau da masu zuwa bayan mu muyiwa kanmu gata da dasa bishiyoyi don dawo da ni'imar dausayin kasar mu, kyautata muhallan mu, habaka tattalin arzikin mu da yiwa na bayan mu tanadin alheri. Allah ya bada iko, aminBatun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen