‘YAN TIJJANIYYAH DA CIN MUTUNCIN ALLAH DA MANZONSA
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=591

 
Daga Nibras Muhammad

‘YAN TIJJANIYYAH DA CIN MUTUNCIN ALLAH DA MANZONSA

Bismillahirrahmanirraheem.

Yau inaso in share din wani sauti ne wanda wasu ‘yan tijjaniyyah suka zagi Allah da manzonsa acikinsa, wannan ya faru ne kaman yanda na sami labari awurin wani mauludin inyass. Inda suke nuna cewa shi inyass ya wuce gabar kowa, da dai kalamai munana na shirka da kafirci da fitsaranci.Kaman yanda kowa ya sani ne maluman Ahlussunnah sunyi kokari kuma suna kai wurin wayar da kan al'ummah akan tafarkin sufaye wanda wannan tafarki gurbatacciyace kuma Tana kaiwa ga halaka. Amma wani lokaci in ana bayanin hakikanin sufanci da abinda ta kunsa sai mutane su rika ganin kaman sharri ake musu, hatta wa'inda suke bin wannan tafarki ta sufancin sai surinka ganin abin karyane tsagoronta sabida su ba'a fada musu ainihin haqiqanin abin ba, su anrudesu ne dason annabi da kuma zikiri da salatin annabi, wanda ahakikanin lamari ba haka abin take ba.
Amma yanzu ansami wanda suka yunkura daga cikin mabiya wannan tafarkin sufanci sukaje suka karanto hakikanin lamarin kuma suka dawo suna bayyana wa mutane gaskiyarta bawai don suka da bayyana aibinta ba, a'a don nuna wa mutane haqiqa subi. Daga cikin wa'innan wa'inda suka karanci haqiqanin lamarin ne aka sami wasu ‘yan darikar tijjaniyya suka fada kadan daga cikin aqeedarsu, hakan yakai ga wasu ‘yan tijjaniyyar sukayi Allah wadai dasu kuma suka nuna su basu tare dasu.

Toh haqiqanin gaskiya ‘yan'uwa wannan irin aqeedunsu kenan dama ga duk wanda ya sani, yana nan rubuce cikin littafansu. Saboda haka in kaji wani dan tijjaniyya yace ba haka bane toh bai karanci tafarkin bane, yana tafiyane a kife. Muna rokon Allah ya shiryar damu ya nuna mana gaskiya ya bamu daman binta, ya nuna mana karya ya bamu daman kauce mata.

DANNA NAN domin saukar da sautin. Wassalam

Mai Rubutu:
Nibras Muhammad Auwal.
Batun: Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi