Raddin Dr Rabiu Rijiyar Lemo Ga Mulhidan ‘Yan Tijjaniyya
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=593

 
Daga Dr Rabiu Rijiyar Lemo

Raddin Dr Rabiu Rijiyar Lemo Ga Mulhidan ‘Yan Tijjaniyya

Assalaamu Alaikum Warahmatullahi Wabarkaatuh.

Aciga da kawo muku raddodi na malamai da nakeyi kan cin mutuncin da wasu ‘yan tijjaniyya sukayi wa annabi a kano, yau ma ga raddin Dr. Rabiu kano. Allah ya amfanar damu, Allah kuma ya qara shiryar damu baki daya. Domin Saukar wa DANNA NAN wassalamu alaikum

Raddin Abduljabbar dan Taratsi Ga Mulhidan ‘Yan Tijjaniyya

Assalamu Alaikum Barkanku da yau. Kaman yanda kowa ya sani ne cikin kwanakinnan muna cikin bakin ciki game da abubuwan da wasu ‘yan tijjaniyyah suka aikata na cin mutuncin manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam). Wanda hakan ya kai ga samun raddodi daga maluma na sunnah har da ma malaman Bid'ah wanda abin ya wuce tunaninsu. Kaman yanda ya gabata na gabatar muku da raddin malaman sunnah biyu Dr Sani Umar Rijiyar Lemo Da Kuma Sheikh Abdallah Gadon Kaya yau zan kawo muku raddin wani malamin Darika amma ta Qadiriyyah wato Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara.
Shidai Abduljabbar Kaman yadda kowa ya sani ya shahara Da hayaniya Da Taratsi Da kuma kai harin Ta'addanci wa sahabban Manzon Allah(Sallallahu Alaihi wasallam) da kuma magabata na kwarai irinsu bukhari muslim da sauransu. Shidai ba kafar baya bane wurin Ta'addanci acikin addinin musulunci, amma duk da wannan ta'addancin tasa ya ga cewa wa'innan ‘yan Tijjaniyya sunfishi har yaga ya dace Yayi musu raddi mai zafi. Masu sauraro sai kuyi hakuri Sabida acikin raddin tasa zakuga cewa yana kawo ayoyi da kurakurai kuma Ihu da taratsi tayi yawa awurin. Hakan ta samo nasaba ne kan abinda ya gine mabiyansa kan hayaniya da Ihu. Sannan kawo ayoyi da yakeyi da kurakurai ta samo asali ne kan rashin hadda da yake fama da ita kamar yadda shi ya fada da kansa acikin wasu karatuttukansa. Kada na cikaku da bayanai domin sauke wannan raddi DANNA NAN. Ayi sauraro lafiya wassalamu alaikum.

Ya Kamata Shehu A Kafirta inyass

Baidace ace wani Qudubi ko wani Nujubi Ko wani Gausi Koma dai karamin shehi ko babba ya fito ya kafirta wa'innan mutane da suka zagi Annabi(sallallahu alaihi wasallam) a kano da sunan cewa su ‘yan hakika sannan kuma ya kasa kafirta inyass wanda awurinsa su wa'innan mutane suka samo aqeedunsu.Wannan rashin adalci ne. Duk da munsan cewa kafirtasu da akayi ta shafi dukansu har da babansu inyass da suka samo wannan aqeedah awurinsa, amma ya dace afito fili a kafirtashi shima domin kada nan gaba asami wani da zai sake zuwa ya dauko bayanansa na kafirci yana yadawa cikin al'ummah. Sannan cewa ayiwa ‘yan tijjaniyya adalci kada a dangantasu da wa'innan mutane wannan ba daidai bane. Wa'innan mutane bawai sabon abu sukazo dashi daga wurinsu ba, a'a abune wanda tuntuni yana rubuce tun shekarun baya masu yawa cikin littattafansu kuma malamansu suna koyar dashi sai dai ba kowa ake bari ya gane ba sai wanda yayi nisa cikin tafiyar. Wanda wannan abin da kafiran ‘yan hakikan kano suka fada kadanne daga cikin munanan abubuwa da suke kunshe cikin littattafansu. Abin da kawai zamuce ma ‘yan tijjaniyya su tausaya wa kansu su tuba subar wannan tafarki domin wannan tafarki ba ta annabi bace.Batun: Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi