Ko Kafiran Zamanin Jahiliyya Ba Su Dauki Karya Hanyar Rayuwa Ba
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=627

 
Sheikh Muhammad Ibn Salihu Al-Usaimin

Ko Kafiran Zamanin Jahiliyya Ba Su Dauki Karya Hanyar Rayuwa Ba

Babi na Hudu:

Musulmi ba ya zaluntar Musulmi kuma kada ya mika Musulmi ga azzalumi:

162. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: ''Laisu ya ba mu labari daga Ukail daga dan Shihab cewa: ''Lallai Salim ya ba shi labari cewa, lallai Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya ba shi labari cewa: ''Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, ''Musulmi dan uwan Musulmi ne ba ya zaluntarsa kuma ba ya mika shi zuwa ga azzalumi. Wanda ya kasance a cikin kula da bukatar dan uwansa, Allah Zai kasance cikin kula da bukatarsa. Wanda ya kwaranye (shafe) wa wani Musulmi bakin cikin (duniya) Allah Zai shafe masa wani bakin ciki daga bakin cikin Ranar kiyama. Wanda ya boye asirin wani Musulmi Allah zai boye masa asirinsa Ranar kiyama.''

Babi na Biyar:

Bisa fadar (Annabi SAW) cewa: ''Ka taimaki dan uwanka azzalumi ko wanda aka zalunta:

163. An karbo daga Usman dan Abu Shaiba ya ce: ''Hushaim ya ba mu labari ya ce, Ubaidullahi dan Abubakar dan Anas da Humaid ya ji Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: ''Annabi (SAW) ya ce: ''Ka taimaki dan uwanka azzalumi ko wanda aka zalunta.''
164. An karbo daga Musaddad ya ce: ''Mu'atamir ya ba mu labari daga Humaid daga Anas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: ''Manzon Allah (SAW) ya ce, ''Ka taimaki dan uwanka azzalumi ko dan uwanka wanda aka zalunta. Sai (sahabbai) suka ce, ''Ya Manzon Allah! Mun san yadda za mu taimaki wanda aka zalunta, amma kamar yaya za mu taimaki azzalumi? Ya ce, ''Ka rike hannunsa ka hana shi aikata zalunci.''

Babi na Shida:

Taimakon wanda aka zalunta:

165. An karbo daga Sa'id dan Rabi'u ya ce: ''Shu'abah ya ba mu labari daga Ash'as dan Sulaim ya ce, ''Na ji Mu'awiyya dan Suwaid ya ce, ''Na ji Barra'u dan Azib (Allah Ya yarda da su), ya ce: ''Annabi (SAW) ya umarce mu da abubuwa bakwai, ya hane mu game da abubuwa bakwai, sai ya ambaci: (1) Gaisar da mara lafiya; (2) Bin jana'iza (Sallar Gawa); (3) Gaisar da mai attishawa; (4) Amsa sallama; (5) Taimakon wanda aka zalunta; (6) Amsa kiran gayyata; (7) Taimako wajen isar (barrantar) da rantsuwa (don samar da wani hakki).

166. An karbo daga Muhammad dan Ala'u ya ce: ''Abu Usama ya ba mu labari daga Buraid daga Abu Burda daga Abu Musa (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: ''Mumini da dan uwansa mumini kamar ginin bene ne, sashinsa na karfafa sashi, sai (Annabi) ya hada tsakanin yatsunsa (ya ce, kamar haka).''

Babi na Bakwai:

Neman taimakon Allah a kan azzalumi. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: ''Allah ba Ya son bayyana mummunar magana face wanda aka azalunta, Allah Ya kasance Mai ji Masani (k:4:148).'' Da fadarSa cewa: ''Kuma su ne wadanda idan zalunci ya shafe su sai su rika neman taimako (su rama).'' (k: 42:39).'' Ibrahim ya ce, ''Sun kasance ba su son ramuwar gayya kansu amma lokacin da suke da karfi sai su rika yafewa (ga wadanda suka zalunce su).''Batun: Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar