Azumi Da Abubuwan Da Yake Koyarwa (1)
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=641

 
Daga Salihu Is'hak Makera

Azumi Da Abubuwan Da Yake Koyarwa (1)

Azumi da takawa:

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. Mai rahama Mai jinkai. Mai nuna mulkin Ranar Sakamako. Kai kadai muke bautawa kuma gare Ka kadai muke neman taimako. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da sauran masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Bayan haka, a makon gobe cikin yardarm Allah za mu shiga watan azumin Ramadan mai albarka, kuma saboda hakan ne muke fara gabatar da dan bayanin da ya samu kan wannan ibada mai girma da fatar Allah Ya sa mu shiga watan lafiya mu azumce shi lafiya mu kuma ga bayansa lafiya.
Allah Madaukaki Ya ce: ''Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke daga gabaninku, tsammaninku, za ku yi takawa.'' (k:2:183).

Takawa a takaice ita ce ''Garkuwa,'' garkuwa daga aikata sabo ko garkuwa daga shiga wuta, wato abin da zai hana mutum aikata sabo ko abin da zai hana shi shiga wuta. Kuma a cikin aya ta 2 sura ta 2, Allah Madaukaki Ya nuna cewa Alkur'ani shiriya ne ga masu takawa. Ke nan duk mutumin da ya rasa takawa, Alkur'ani ba zai zame masa shrirya ba. Don haka rasa takawa ne ya sa ga Alkur'ani a hannunmu, amma ba mu shiryuwa da shiriyarsa, Alkur'ani ba ya zame mana akala, balle ya jagoranci rayuwarmu har ya inganta ta.

Hakika malamai sun sha yi na bayani kan azumi da hukunce-hukuncensa kuma sun sha bayyana cewa azumi yana koyar da takawa, sai dai ya kamata mu rika tambayar kawunanmu ina wannan takawa take shiga bayan kammala azumin? Ko dama takawar ba ta shiga zuciya da jikkunanmu ta ratsa su ne a lokacin azumin, shi ya sa bayan kammala shi ba a ganin gurbinta a ayyuka da dabi'unmu? Ko kuwa kacokan ba mu samun dandanon takawar ne? Yaya duk shekara sai mun yi azumi amma kuma dabi'unmu suna nan jiya ya yau! Me ya sa muka kasa gusawa gaba ta wajen karuwar takawa da ayyukan kirki a tsakaninmu? Ko kuwa hanyar takawar ce ba mu bin ta balle mu kai ga samun takawar?

Bari mu ga abin da malamai suka ce kan takawa da yadda ake kaiwa gare ta da yadda azumi ke haifar da takawa. Fitaccen malamain tafsirin nan Alwahidiy ya ce: ''Lallai azumi tafarki ne na isa ga takawa, domin yana kange mutum daga ayyukan sabo masu yawa da zuciya ke so.'' (Al-Wasid fi Tafsirinl kur'anil Majid na Al-Wahidi, Mujalladi na 1 shafi na 2727).

Shi kuwa Abu Al-Muzaffar As-Sam'aniy ya ce game da fadin Allah Madaukaki: ''Tsammaninku, za ku yi takawa.'' Ma'ana: ''(Za ku samu takawa ce) da azumi: Saboda azumi mai sadarwa ne ga takawa sakamakon abin da ke cikinsa na rinjayar rai da karya sha'awoyi.'' (Tafsirus Sam'ani, Mujalladi na 1 shafi na 179, kuma ana iya duba Zadul Musayyir, Mujalladi na 1 shafi na 167 da Bahrul Muhid, Mujalladi na 2 shafi na 36).

Shi kuma Ibnu Kasir cewa ya yi: ''A cikin azumi akwai tsarkake jiki da kuntata wa hanyoyin da Shaidan ke shiga mutum. (Tafsirul kur'anil Azim, Mujalladi na 1 shafi na 318, kuma ana iya duba Muhasinut Ta'awil, Mujalladi na 1 shafi na 74).

Tushen lamarin dai shi ne azumi a zahirinsa yana kashe jiki ta yadda jiki zai yi laushi ya daina sha'awar aikata munanan ayyuka da sha'awoyi ke haddasa su. Za mu ga haka a cikin Hadisin da Buhari da Muslim suka ruwaito daga Abdullahi dan Mas'ud (RA) inda ya ce: ''Muna tare da Annabi (SAW) sai ya ce: ''Wanda yake da ikon yin aure a cikinku, to ya yi aure, domin ya fi runtse ido da kange farji. Wanda ba zai iya ba, to, na hore shi da yin azumi domin shi makangi ne (daga sha'awa).'' (Buhari, Hadisi na 1905 da Muslim Hadisi na 1400). Ibnu Hajri ya ce: ''Manufa lallai azumi yana kashe sha'awar jima'i.'' (Fathul Bari, Mujalladi na 4 shafi na 142).

Azumi na hana gabbai auka wa haram:

Baya ga haka azumi na hana gabbai fadawa cikin haram wanda hakan ke sa a kara samun takawa. Ibnu kayyim ya ce: ''Wanda ya zauna da mai azumi zai amfana da zamansa tare da shi kuma ya kubuta daga maganar zur da karya da fajirci da zalunci. Idan zai yi magana ba zai yi magana da abin da zai cutar da azuminsa ba. Idan zai yi aiki ba zai aikata abin da zai bata azuminsa ba, sai ya zamo maganganunsa dukkansu masu amfani ne na salihanci.'' (takaitawa daga Al-Wabilus Saibu Min Kalamid dayyib, shafi na 41).

Kuma ya zo a cikin Hadisi daga Abu Huraira (RA) ya ruwaito inda ya ce: ''Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Duk wanda bai bar maganar zur ko aiki da ita ba, to Allah ba Ya bukatar ya bar cin abincinsa da abin shansa (da sunan azumi).'' (Buhari, Hadisi na 1903).

Almuhlab ya ce: ''A cikinsa (Hadisin) akwai dalili na cewa lallai hukuncin azumi shi ne kamewa daga jima'i da maganar zur, kamar yadda ake kamewa daga ci da sha. Idan mutum bai kame daga wadannan abubuwa ba, hakika azuminsa ya samu nakasu, kuma ya bijirar da kansa ga fushin Ubangijinsa da kuma barin karba daga gare shi.'' (Sharhu Sahihul Buhari na Ibnu Baddal, Mujaladi na 4 shafi na 23).

Jabir bin Abdullahi (RA) ya ce: ''Idan kana azumi, to ya zamo jinka da ganinka da harshenka suna azumi (kamewa) daga karya da laifuffuka. Ka guji cutar da mai yi maka hidima, kuma ya zamo kana da sanyin hali da natsuwa a ranar azuminka, kada ka sanya wunin azuminka da wunin da ba ka azumi su zama daidai.'' (Al-Munsif na Ibnu Abu Shaiba, Mujalladi na 2 shafi na 422).

Azumi da koyar da hakikanin ikhlasi:

Bayan ga koyar da takawa haka azumi yana rainon zukata kan hakikanin ikhlasi, wato yin kowane aiki domin Allah kawai. Ibnu kayyim ya ce: ''Azumi domin Allah Ubangijin halittu ne ake yin sa a tsakanin sauran ibadoji. Kuma lallai mai azumi ba ya aikata wani abu, iyaka yana barin sha'awoyinsa da abincinsa da abin shansa domin Abin bautarsa. Wato shi ne barin abubuwan da rai ke so, ko ke jin dadinsu domin fifita son Allah da neman yardarSa. Kuma shi sirri ne a tsakanin bawa da Ubangijinsa, ba wanda ke iya lekawa ya gano hakikaninsa sai Shi (Allah). Bayi suna iya lekawa su ga mutum ya bar abubuwa masu karya azumi na zahiri, amma kasancewarsa ya bar abincinsa da sha'awoyinsa domin neman yardar Abin bautarsa (Allah), wannan wani al'amari ne da dan Adam ba zai iya ganowa ba, wannan shi ne hakikanin azumi.'' (Zadul Mi'ad, Mujalladi na 2 shafi na 29).

Ya zo a cikin wani Hadisi daga Abu Huraira (RA) ya ce: ''Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Allah Ya ce: ''Dukkan aikin dan Adam nasa ne, face azumi, shi Nawa ne, Ni ne zan yi sakayya a kai.'' (Buhari, Hadisi na 1904).

Ibnu Baddalu ya ce: ''Azumi da sauran ayyuka dukka domin Allah ake yin su. Sai dai sauran ayyuka na zahiri Shaidan na tarayya a cikinsu ta hanyar riya da sauransu. Shi kuma azumi ya kasance babu mai iya sanin hakikaninsa, sai Allah. Don haka sai Ya yi sakayya a kansa bisa gwargwadon ikhlasin da aka yi maSa, don haka ya halatta Ya jingina shi ga kanSa.''Batun: Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc