Tukuici Ga Mai Azumi
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=644

 
Tukuici Ga Mai Azumi

Hikimar wajabta azumin Ramadan:

Ramadan suna ne na watan tara daga watannin Musulunci, shi ne kuma watan da Allah Ya ambace shi karara. Hikimar da tasa aka wajabta mana azumi don tsarkake rai ne da kuma sanya mata tsoron Allah don ta cancanci dacewa gobe Lahira.

Ladubba wajibabu ga mai azumi:

1. Wajibi ne ga mai azumi ya tashi da niyyar cewa azumi ibada ce cikin maganganunsa da ayyukansa.

2. Ya nisanci abubuwan da aka haramta a cikin maganganunsa da ayyukansa kuma ya tsare ganinsa da jinsa da tafiyarsa daga haramtattun abubuwa. Wadannan wajibi ne ga mai azumi ya kiyaye su in yana so azuminsa ya karbu a wajen Allah.
Abubuwan da ake so ga mai azumi:

1. Jinkirta yin sahur.

2. Gaggauta yin bude-baki.

3. Yawan karatun Alkur'ani Mai girma.

4. Yawaita addu'o'i na alheri.

5. Yawaita sadaka.

6. Yawan ambaton Allah da tsarkake Shi da sauran ayyukan alheri.

Falalar watan Ramadan
1. A cikinsa aka saukar da AIkur'ani: Allah Yace: ''Watan Ramadan ne wanda aka saukar da AIkur'ani a cikinsa.''

2. Ana gafarta zunubai a cikinsa: Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace: ''Wanda ya yi azumin watan Ramadan yana mai imani yana mai kyautatawa, to an gafarta masa abin da ya gabata na laifufukansa.'' Buhari ya ruwaito Hadisin.

3. Ana amsar addu'ar mai Azumi: Annabi (SAW) yace: ''Ana karbar addu'ar mutum uku: mai azumi lokacin bude-baki da shugaba mai adalci da wanda akazalunta.''

4. Daren Lailatul kadari: Allah Yace ''Daren Lailatul kadari ya fi wata dubu wajen alheri.

5. Ana daure shaidanu: Domin Annabi (SAW) yace: ''In Ramadan ya zo ana daure shaidanu kuma a bude kofofin Aljanna.''

6. Yin Umara a Ramadan yana daidai da aikin Hajji.

Imam DSP Ahmad Adam Kutubi 08036095723Batun: Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin