Wani Abu Kan Tuba Da Komawa Ga Allah
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=646

 
Daga Salihu Is'haq Maqera

Wani Abu Kan Tuba Da Komawa Ga Allah

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificn halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, a daidai lokacin da muke tunkarar watan azumin Ramadan, watan tuba da komawa ga Allah yana da kyau, mu fara shirin komawa ga Allah tun kafin isowar wannan wata mai girma da albarka. Ba wai muna cewa sai Ramadan ake tuba a koma ga Allah ba, amma sananne cewa galibin mutane sun fi tuba da yin istigfari da komawa zuwa ga Allah a wannan wata da muke fuskanta. Tabbas tuba da komawa zuwa ga Allah abu ne da ya zamo wajibi musamman a wannan lokaci da muke fuskantar jarrabawa iri-iri.

Tuba a koma ga Allah abu ne mai sauki wato shi ne a nemi gafarar Allah da harshe da zuciya kamar yadda Allah Madaukaki Ya nuna: ''Kuma wanda ya aikata cuta ko kuwa ya zalunci kansa, sannan ya nemi Allah gafara, zai samu Allah Mai gafara ne, Mai jin kai.'' (k:4:110).
Sannan Abu Huraira ya ce: ''Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Na rantse da Wanda raina yake hannunSa, da za a ce ba ku yin kuskure da Allah Ya shafe ku duka, Ya kawo wadansu mutanen da za su yi kuskure su roki Allah gafara don Ya gafarta musu.'' Muslim ya ruwaito.

Don haka bari mu sake yin dubi a takaice kan wasu ayoyi da suke magana kan istigfari da komawa ga Allah da tuba gare Shi, domin mu ga irin irin yadda magabata suke daukar zunubi da ka'idojin karbar tuba da yadda ya kamata a yi addu'a.

1. Istigfari dabi'a ce ta mutanen da Allah zai ba su nasara ko babban rabo:

Allah Madaukaki Ya ce: ''(Sai 'yan wuta suka ce), Ya Ubangijinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sannan idan mun koma (ga aikata barna), to, lallai ne, mu ne masu zalunci. Ya ce, ''Ku tafi (da wulakanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana. Lallai wadansu kungiyoyi daga bayiNa sun kasance suna cewa, ''Ya Ubangijinmu! Mun yi imani, sai Ka gafarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alherin masu tausayi. Sai kuka rike su leburori (wulakantattu).'' (k:23;107-110).

Shi ke nan magana ta kare? A'a sai Allah Ya ce: ''Lallai ne, Ni Ina saka musu a yau, saboda abin da suka yi wa hakuri. Domin lallai ne, su, su ne masu samun babban rabo.'' (k:23:111).

2. Istigfari yana bude dukkan kofofin alheri a nan duniya da Lahira.

A lokacin Halifancin Amirul Mumina Umar bin Khaddabi (RA) an samu kamfan ruwa a Madina, bayan an yi shelar sallar rokon ruwa, sai Umar (RA) ya hau mumbari a lokacin hudubarsa ya fi karanto ayoyin da suka yi magana ne kan istigfari. A wancan rana ya karanto kalmomin Allah game da abin da Annabi Nuhu (AS) ya fada ga mutanensa: ''Na ce, ''Ku nemi gafara daga Ubangijinku, lallai ne Shi Ya kasance Mai gafara ne. Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai bubbuga. Kuma Ya yalwata muku game da dukiya da 'ya'ya, Ya sanya muku (albarka) ga gonaki, kuma Ya sanya muku koguna.'' (k: 71:10-12).

3. Istigfari yana nuna mutanen da suka fi soyuwa a wurin Allah:

Abu Huraira (RA) ya ce: ''Ya ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: ''Na rantse da Allah, Ni ina rokon Allah gafara da tuba a gare Shi a wuni daya fiye da sau saba'in.'' Sannan labarin Annabi Ayyuba (AS) na cewa: ''(Muka ce), Kuma ka riki wani kulli da hannunka, ka yi duka da shi, kuma kada ka karya rantsuwarka. Lallai Mu, Mun same shi mai hakuri. Madalla da bawa, shi. Lallai shi mai mayar da al'amari (tuba) ga Allah ne.'' (k:38:44).

4. Ganin girma da munin zunubi:

Hadisin Ma'iz yana nuna yadda ake istigfari da yadda gaskiyar tuba ga Allah take. Abin da ya faru Ma'iz shi ne ya yi zina, kuma ya zo ga Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Ya Manzon Allah! Na yi zina!'' Sai Manzon Allah ya kawar da kai daga gare shi, ta yadda Ma'iz zai hakura ya tserar da kansa daga haddi, amma sai Ma'iz ya ci gaba da komawa ta gaban fuskar Annabi (SAW) yana maimaita ''Na yi zina! Na yi zina!!'' 
Da Ma'iz ya yi ta nanata fadin haka sai Manzon Allah (SAW) ya tambaye shi: ''Shin kai mahaukaci ne?'' Ya ce: ''A'a.'' ''Shin ka sha giya ne (ya nemi wani ya sunsuna bakinsa)?'' Ya ce, ''A'a.'' Ya ce: ''Kuma ka shige ta?'' Ya ce: ''Eh!''
Sai Manzon Allah (SAW) ya tambaye shi a hankali, ''To wai me kake so da kake bayyana wannan abu?'' Sai Ma'iz ya ce: ''Ina so ne ka tsarkake ni!''
Irin wannan karfin imani da ya sa Ma'iz irin wannan tuba ga Allah da za a raba shi da ya ishi dukkan mutane Madina, kamar yadda karshen Hadisin ya nuna.

Sannan Hilal bin Sa'ad ya ce: ''Kada ka dubi kankantar zunubinka, ka dubi girman Wanda kake saba maSa (Allah)!'' 
5. ka'idojin tuba ta gaskiya:

Anas (RA) ya ruwaito Manzon Allah (SAW) yana cewa: ''Dukkan 'yan Adam masu kuskure ne. Amma mafi alherin masu kuskure su ne masu tuba.'' Tirmizi ya ruwaito. Imam Nawawi (RH) ya rubuta cewa ana neman gafara kan kowane zunubi. Idan wannan zunubi tsakanin bawa da Ubangiji ne, bai shafi hakkin wani ba, to akwai ka'ida uku na karbar wannan tuba:

1. Daina aikata wannan zunubi.

2. Yin nadama kan abin da ya gabata.

3. Da niyyar ba za a koma ga aikata wannan zunubi ba. Idan aka rasa daya daga cikin wadannan ka'idoji to akwai nakasu ga wannan tuba.

Idan kuma akwai hakkin wani to sharadi na hudu zai shigo. Wato mutum ya mayar wa mai hakki, hakkinsa. Misali idan ya saci kayansa ne ya mayar masa. Idan ya mare shi ya ba shi dama ya rama, ko ya nemi ya yafe masa. Idan ya zage shi ne ya nemi ya yafe masa.

A karshe ga wata kissa nan don nazari: Wata rana bayan an tafka ruwan sama Hisham bin Hasan yana tafiya a bayan Al'ala bin Ziyad a wata hanya mai tabo a kauyensu. Sai ya lura Ziyad yana kauce wa ruwan da ke gudu a gefen hanya tare da tabo, sai wani ya tunkude shi har takalminsa ya zame ya ja shi cikin ruwan. karfin igiyar ruwan ya tilasta Ibnu Ziyad ya koma daya gefen.

Bayan sun isa gida sai Ibnu Ziyad ya juyo ga Hisham ya ce: ''Yadda muke kauce wa tabo da igiyar ruwa a kan hanyarmu ta zuwa gida, haka ya kamata Musulmi ya kauce wa saba wa Allah a daukacin tafiyar da yake yi zuwa Lahira. Kuma kamar yadda ka ga igiyar ruwa ta ja ni, haka igiyar zunubi take jan mutum lokacin da ya fada cikinta, za ta yi ta jansa tana dulmiyar da shi yana dada nutsewa.''Batun: Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi