SHIN RAGOWAR 'YA'YAN NASA BA AHLUL- BAITI BANE N0 1?
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=653

 
SHIN RAGOWAR 'YA'YAN NASA BA AHLUL- BAITI BANE N0 1?

Shubuhuhin shi'a akan hadisin mayafi da warware su a bisa fahimtar malamai na kwarai.

Bissimillahir Rahamanir Rahim.

Daga cikin shubuhar da yan shi'a masu limamai goma sha biyu

suke yadawa akwai hadisin (MAYAFI) wato hadisin da aka karbo daga nana Aisha da umma salama (r.a)
cewa, lokacin da Ayar nan dake cikin suratul Ali- imran ta sauko wato fadin ubangiji (swa) " Duk wanda yayi jayayya da kai dangane da abinda akayi maka wahayi bayan dalilai sun bayyanannu sun zo maka, to kace:- ku zo mukirawo 'ya'yan mu da 'ya'yan ku, da matayenmu,da matayenku, damu kanmu da kanku, sannan muyi addu'a ta la'anta akan masu karya " sai manzon Allah ya kirawo s.
Ali da nana fatima da hasan da husaini (r.a) ya lulluba da mayafi tare da su, sannan yace "ya ubangiji wadannan iyalan gidana ne ka kawar da datti daga gare su,ka kuma tsarkake su iyakar tsarkakewa".

Yan shi'a masu limamai goma sha biyu

sukan kafa hujja da wannan hadisin cewa, s. Ali da nana Fatima da hasan da husaini (r.a) sune kadai ahlul-baiti, kuma ma'asumai ne basa kuskure. Hujjan su nan kamar yanda suke riyawa ita ce. Allah yafi da datti daga barinsu ya kuma tsarkake su.

Don haka sun zama ma'asumai a riyawarsu, jawabi akan wannan hadisi shine, ta fuskoki kamar haka, .

INALLAH YA YARDA ZANKAWO JAWABI AKAN WANNAN HADISIN A DARASI NA GABA.
Batun: Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai