SHIN RAGOWAR ''YA YAN NASA BA AHLUL-BAITI BA NE ?(002)
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=654

 
SHIN RAGOWAR "YA YAN NASA BA AHLUL-BAITI BA NE ?(002)

SHUBUHOHIN SHI'A AKAN HADISIN MAYAFI DA WARWARESU ABISA FAHIMTAR MALAMAI NA KWARAI.

1) Tabbas s. Aliyu, nana Fadima, hassan da husaini r.a, suna daga cikin mafiya kusanci da manzon Allah s.a.w.Amma basu kadai Ahlul-baiti ba a haduwar malaman sunnah da shi'a.

2) hakika wannan hadisi ya inganta inbanda wata ruwaya da imamu tirmizi ya fitar da ummu salama r.a tace " lokacin da manzon Allah s.a.w ya lullube s. Aliyu da fatima da hasan da husaini r.a, yakaranta wannan ayar ta cikin suratul Al-ahzab, sai nima (ummu salama) nace ya ma'aikin Allah nima ina cikin Ahlul-baiti ? Sai manzon Allah s.a.w yace " kedai kina cikin alheri".

malaman hadisi sun tabbatar da cewa " wannan ruwaya bata inganta ba". Saboda acikin isinadinsa hadisin akwai gibi kamar yadda lbn kathir yafada. Ruwayan da ta inganta daga ummu salama itace lokacin da tambayi manzon Allah s.a.w cewa nima shin ina cikin Ahlul-baiti? Sai yace!
Tabbas kema kina cikinsu".

3) wannan aya ta cikin suratul Al-imran bacewa tayi manzon Allah s.a.w yakirayi dukkan Ahlul-baiti ba. A'a an umurce shine da yakirawo wadanda suka samu daga danginsa. Sai akace dai dai wannan lokaci s. Aliyu da nana fadima da hasan da husaini r.a sune iyaka wadanda zai kira. Ba wai don sune kadai Ahlul-baiti ba. Dalili kuwa shine sanannen abu ne cewa bayan su akwai wadanda suke da matsayi irin daya dasu ta bangaren nasaba agurin manzon Allah s.a.w ahaduwan malamai.

Amma daidai wannan lokacin basa wannan gurin saboda wasu dalilai misali:- akwai ja'afar dan abi dalib da Akilu r.a yan uwan s. Aliyu r.a wanda matsayin su iri daya ne dana s. Aliyu tabangaren nasaba agurin manzon Allah s.aw.

Ita kuwa nana fadima r.a akwai yan uwanta da suke da nasaba iri daya, amma daidai wannan lokacin dukkan ninsu sun rasu ita kadai tai saura. domin yatabbata cewa "ya "yan manzon Allah s.a.w guda bakwai ne 7 maza uku 3 ;- Alkasin, Abdullahi da Ibrahim r.a.

Sai kuma mata hudu 4 ;- watau zainab da Rukayya da Umma kursum da Fadima yar autansu r.a.

Hasan da husaini r.a kuwa suna da "yan uwa da suke ciki daya, watau zainab umma kursum wacce s.

Ummar r.a ya aura, sai kuma muhsin wanda yarasu yana karami.

Sannan kuma manzon Allah s.a.w yana da wasu jikoki ta bangaren "ya "yansa zainab da Rukayya r.a da suka haifa tare da s.

Usman r.a da ibn abul as r.a. Kari akan haka, akwai Abbas da Abdulmudalib r.a wanda shi yafi kuwa kusanci da manzon Allah s.a.w bayan "ya"yansa amma alokacin bayanan .

Abin dai damuke so agane manzon Allah s.a.w yakira s. Aliyu da nana Fatima da hasan da husaini r.a ne awannan lokacin, don sun kawai wanda zai iya kira ba wai don sune kadai Ahlul-baiti ba. Idan yan shi'a suka to maiyasa manzon Allah bai kirayi matan sa ba a halin yana damar da zai kiraye su. Sai muce jawabi yagabata ahadisin umma salama cewa lallai matarsa suna daga cikin Ahul-baiti.

Amma bai kiraye su bane saboda basu da alaka da shi ta nasaba da jini, sai ta bangaren auratayya kamar yadda bayani zai zo nan gaba. Kari akan haka acikin ayar ba ce manzon Allah s.a.w yakirayi matarsa na aure ba. Kuma manzon Allah s.a.w ba zai iya lulluba tare da matansa ba acikin wannan bargo a halin akwai wanda ba muharramansu nabe aciki.

AKWAI CIGABA A DARASI NAGABA IN ALLAH YA YARDA.
Batun: Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai