SHIN RAGOWAR ''YA''YAN NASA BA AHLUL-BAITI BANE (003) ?
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=655

 
SHIN RAGOWAR "YA"YAN NASA BA AHLUL-BAITI BANE (003) ?

SHUBUHOHIN SHI'A AKAN HADISIN MAYAFI DA WARWARE SU A BISA FAHIMTAR MALAMAI NA KWARAI.

4) Ga wata tambaya ga "yan shi'a:

menene hukuncin ragowar "ya"yan manzon Allah s.a.w da jikokinsa, shin su ba ahlul-baiti bane? Menene hukuncin ragowar yan uwan s.

Aliyu, ja'afar Akilu r.a ?

Menene hukuncin Nana khadija r.a suma duk ba ahlul-baiti bane?

Idan yan shi'a suka ce suma ahlul-baiti ne. Sai muce to ai suma basa acikin wadanda manzon Allah s.a.w ya lullube da mayafin, ta yaya suka zama ahlul-baiti ? idan yan shi'a suka ce manzon Allah s.a.w baikiraye su bane saboda galibin su basanan.
Sai muce wannan ya zama martani ga "yan shi'a da suke iyakance Hassan da Hussaini da s. Aliyu da nana Fatima r.a amatsayin ahlul-baiti, ya kuma nuna tabbacin abinda muka gabatar cewa manzon Allah s.a.w yakirayi iyaka wadanda ya samu daman yakiraya awannan lokacin, ba wai don sune ahlul- baiti ba. Idan yan shi'a suka dage cewa lallai iyaka wadanda manzon Allah s.a.w ya lullube da wannan mayafin sune kadai ahlul-baiti.

Sai muce meyasa suke kawo sunayen wasu limamai guda tara 9 bayan sa daga cikin wadanda manzon Allah s.a.w ya lullube da wannan mayafin?

Idan yan shi'a sukace su ragowar limamai guda tara 9 anbasu hukuncine irin na iyayen su, saboda jikokin Hussaini r.a ne.

Sai muce, aibasu kenan jikokin Hussaini r.a ba, akwai jikokin sa da yawa wadanda yan shi'a mai limamai guda goma sha biyu 12 ba su yarda da su ba, kamar Zaidu dan Aliyu dan Hussaini da Isma'il dan muhammad dan Aliyu dan hussaini Allah yakara yarda agare su.

Meyasa yan shi'a basa kawo sunayen su amatsayin limamai? Kari akan haka meyasa yan shi'a suka dauki wasu daga cikin jikokin s.

Hussaini r.a sukayi watsida jikokin s. Hassan r.a?

Kuma meyasa yan shi'a suka zabi Hassan da Hussaini r.a kadai daga cikin "ya"yan s. Aliyu r.a?

Sukayi watsi da ragowar, alhali s. Aliyu yana da "ya"ya sama da talatin 30?

IN ALLAH YAYARDA ZAN KAWO CIGABA
Batun: Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai