Zararren Takobin Sunnah Akan 'Yan Shiah!!!
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=661

 
Sheikh (Dr.) Mansur Sokoto

Zararren Takobin Sunnah Akan 'Yan Shiah!!!

Idan akwai wani Malamin Sunnah wanda kai tsaye zaka ce 'yan Shiah suna kwana da tararrabin bankado irin abinda miyagun litattafansu suka kunsa dan ankarar da al'ummar Musulmi illa da mugunya da ke tattare da wannan ADDINI na Shiah to kai tsaye zaka iya cewa shi ne Dr.

Mansur Sokoto.

Hakika, Malam Mansur Sokoto ya yiwa Addinin Allah hidima wajen bankado irin miyagun aqidun 'yan Shiah dan Ilmantar da al'umma da nuna musu irin mugun hadarin da yake tattare da 'yan Shiah da kuma shi'anci, Malam ya kutsa cikin tafka- tafkan litattafan 'yan Shiah da suke dauke da guba mai karya garkuwa da lalata tsiga da lakar jikin Imani na hakika, Imani na kadaita ALLAH da Bauta da cikakken Tauhidi.
Manya manyan litattafan Shiah, musamman littafinsu mafi tsarki da girma, wato AL-KAFI wanda daya daga cikin miyagun Malamansu wanda akayi a tsakanin karni na 3 zuwa na 4 wato KULAINI, wannan littafi shi ne mafi girman littafi a wajen 'yan Shia na da da na yanzu, sababbinsu da tsofaffinsu; kuma Shi ne mafi girman wani littafi da ya kunshi sharri da kararirayi da makirci da kutunguila da tufka da warwar akan Sahabban Manzon Allah tsarki ya tabbata a garesu, Malam Mansur ya kutsa cikinsa, inda ya tsiraita kusan kafatanin hujjojin da suke rakitowa daga cikin wannan littafi suke takama da dagawa da su.

Malam Mansur Sokoto ya shahara wajen bayyanawa al'ummar Manzon ALLAH SAW cewa duk inda kaga 'yan Shiah a duniya sun siffanta da wasu suffofi guda uku, wadannan suffofi sune JAHILCI, MAKARYATA NE sannan kuma MASU CANZA GASKIYA NE, wadannan su ne manyan siffofin da zaka iya gane duk inda dan Shiah yake. Dan Shiah duk girman rawaninsa da girman Alkyabbarsa sai ka same shi da irin wadannan siffofi manyansu da kananansu, na farkonsu da na karshensu.

Alhamdulillah, da daman al'umma sun fahimci 'yan Shiah yanzu, domin kullumwadannan siffofi kara bayyana suke yi a garesu.

Tarihi bai gushe ba yana tabbatar da duk wasu maganganu da aka fadaakan 'yan Shiah, domin tarihi ya shaide su da yin karya, da batar da sawun gaskiya, da canza hakikanin gaskiyar lamura zuwa wasu abubuwan daban, kuma su din mutane ne masu kambama wani abu da bai kai ya kawo ba, dan rudar daal'ummar Musulmi,Kuma tarihiya shaidesu wajen dakushe gaskiya, da nuna rashin kimarta da rashin bata muhimmanci. Duk wannan abubuwa ne da suke a zahiri wanda tarihi ya shaidi 'yan Shiah da su.

Malam Mansur Sokoto hakika, mutum ne mai saukin kai da taqawa da kamun kai, ga kula da zumunci, duk wanda ya san Malam Mansur Sokoto ya sanshi da zumunci da kaunar 'yan uwa Ahlussunnah.

MalamMansur Sokoto ya yi hidima ainun wajen bayyanamiyagun Aqidun Shiah ya kuma rubutu kasidu da litattafai dadama akan haka, Kasidun da ya rubutu a cikin turancin Ingilishi da Hausa ba za su lissafu ba. Haka kuma, ya rubuta litattafai da dama dan bayyanawa al'umma su waye 'yan Shiah, kadan daga cikin muhimman ayyukan da Dr.

Mansur ya yi akwai fassara katafaren littafin nan na Ibn Taymiyya na Min- Hajis-Sunnah zuwa HarshenHausa wanda ya zuwa yanzu babu wani Littafin Hausa da aka taba bugawa da yakai girmansa duk fadin kasarnan, akwai da dama daga cikin litattafan Malam da suka dade a hannun al'umma suna karantawa kamar KUBUTACCEN KARBALA, KADDARATA RIGA FATA, SU WAYE MASOYAN AHLULBAITI da sauransu da dama, wadan da ba'a kai ga bugawa ba.

Hakika a wannan zaminin da muke ciki musamman a Najeriya ta Arewa idan akwai wani Zararren Takobi da yakeyawon a saman kan 'yan Shiah suka firgita suka dimauce suka rasa ina gabas take to la-shakka shi ne Malam Mansur Sokoto.

Allah ya taimaki Malam, ya sanyawa rayuwarsa Albarka, ya tsawaita rayuwarsa dan amfanar Addinin Musulunci. Allah ya sanya masa Albarka a cikin zurriyarsa da dukkan lamuransa baki daya. Na tabbata wannan ban fadi komai akan Malam Mansur Sokoto ba, da dama idan sun samu dama zasu yiwa al'umma cikakken bayani sama da wanda na rubuta akan irin hidimar da wannan Bawan Allah ya yiwa Sunnah.

YASIR RAMADAN GWALE
Batun: Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar