WA'AZIN SHEIKH JAFAR MAHMOUD ADAM (RAHIMAHULLAH) NA KARSHE A DUNIYA KUMA GA
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=662

 
WA'AZIN SHEIKH JAFAR MAHMOUD ADAM (RAHIMAHULLAH) NA KARSHE A DUNIYA KUMA GA MATASA DA 'YAN SIYASA

Wannan Nasihar Marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam Rahimahullah ya gabatar da ita ne a ranar Alhamis 25 ga Rabi'ul Auwal, 1428. wato dai- dai da 12th April, 2007.

Ya gabatar da wannan Nasihar a daren Juma'ar da aka kashe shi, a wajen muhadarar da aka shirya a masallacin Juma'a na Usman Bin Affan dake kofar Gadon kaya . Bayan dawowar sa daga garin Bauchi.

Ita wannan muhadarar malamai uku ne suka gabatar da ita daga cikin su akwai sheikh Dr Muhammad Sani Umar R/lemu da Malam Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa da sheikh Muhammad Nazeefi Inuwa.

Wadannan sune malaman da suka gabatar da wannan muhadar, amma kasan cewar sheikh Jafar ya dawo daga tafiya ne sai aka bashi minti goma yayi ta'aliki. Ga kuma yadda ta'alikin nasa ya kasance :
Bayan Mallam ya yi godiya ga Allah, tare da yin salati ga manzon Allah salallahu alaihi wasallam, sannan ya yace ''ya yan uwa musulmi abin da zan fada a nasiha ta ta karshe '' Allahu akbar wato wannan jumla ita Mallam ya fara bude maganarsa da ita, kamar yasan cewa washe gari juma'a zai riga mu gidan gaskiya, sai yaci gaba da cewa ''Muji tsoran Allah, mu duka, muda zamuyi zabe'' wato ya yi wannan Nasihar ne ana jajiberin tsamiya na zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi, Sannan ya ci gaba da cewa '' muda zamuyi zabe da kuma wadan da za'a zaba.

Asalin zaben nan malamai sunyi bayanin sa. Dukkan mutumin da zaka zaba, to ya zama cewa zaka zabe shi ne ba don maslahar ka ba kai kadai, sai don maslahar al'umma gaba daya. Akwai mutanen da suke fama da kuncin tunani, wadan da su tunanin su me zasu samu a karkashin dan takara, sannan su ce a zabe shi; ko kuma me suka rasa suce kada a zabe shi. Inda dan takara zai zo yabani naira miliyan goma ni kadai a matsayi na na Ja'afar amma ya ha'inci alummar da yake wa mulki ta hanyar sauran bukatunsu, wadan da a asusun gwamnati akwai kudaden da za'a iya wadan nan bukatu amma yaki yi, Ni kuma in kalli miliyan goman nan ince ku zabe shi. To hakika na ci amanar kaina, kuma na ci amanar ku talakawa bayin Allah, shi kuma shugaba na haince shi.

Inda shugaba zai hana ni ko kwabo, amma ya zanto kudaden daya karba daga asusun gwamnatin tarayya ya aiwatar da su ta hanyar da ta dace. To wajibi na ne, in kiraye ku cewa ku zabe shi. Ba a dauki ma'aunin na ni me na samu ko me na rasa ba, masu irin wannan sune wadan da suka jahilci Addini kuma suka jahilci rayuwa. Domin wannan shi ne yakai Nigeria cikin halin ka-ka-ni-ka-yi.

Ganin in amfana ni kadai ko kuma a bude mana wata kafa mu yan tsiraru shi ke nan sai muyi shiru alhali mun san abin da shugaba yake yi ha'inci ne,amma sai mu daure masa gindi,hasali ma mu dinga kuruta jama'a cewa dole ne su zabe shi, ba don komai ba sai don abin da bai taka kara ya karya ba.

To wannan kuntataccen tunani ne, kuma rashin hangen nesa ne rashin sanin ya kamata ne. Kullum zaka kalli me muka samu na ci gaba, ba me ni kadai na samu ba '' Allahu akbar sai malam ya kara da cewa '' ina kira ga ku matasa ku lura da yadda ake amfani da ku ''malam ya buga wani misalin abin da ya gani yayin da yake dawowa daga tafiya sai yace '' Da zu na shigo kano dab da lokacin sallar maghriba kafin zuwana nan sai naga wadan da suke kanfen (campaign)
wato da alamu anyi yawo da su cikin garine za su koma gida. Naga yara matasa an ciko su akan akorukura su kusan hamsin acikin motar nan kai da ganin su babu wanda ya yi sallar azahar ballan tana la'asa kuma galibin su da alamun sun bugu mota tana ta layi dasu suna ihu suna dauke da hotuna suna sai wane sai wane kuma su wadan da suke bada kudi ayi hakan ciki babu 'ya 'yan su, nasu suna can, sun kai 'ya 'yan su mayan makarantu na cikin gida ko na waje.

Wannan shi ne hakikanin cin amanar al-umma, kai wannan shi ne kakikanin rashin mutunci, ka haukata ya yan talakawa bayan ka yinwatar da su ka kuma ka jahiltar da su babu ilmin addini babu na rayuwa su kashe lokaci mai tsaho suna dauke da hotunan ka kan kana son ka tsaya zabe a wani mataki na zabe.

Akan abin da za'a basu wanda bai gaza Naira dari uku ko da hamsin ba.

Sannan mallam ya cigaba da nanata maganar sa ta farko inda yace ''Hakika wannan ya kamata ayi hattara, duk wanda zamu zaba, kada mu kalli me ya bamu, mu kalli dacewar sa da cancantar sa. Duk wanda zamu zaba ya kasance ya cancanta ko yabamu kudi ko bai bamu ba. Duk wanda bai cancanta ba to ko yabamu fan taba sama to mu kadashi wannan shi ne gaskiyar lamari, amma idan ku ka tsaya da jahilci da kuntatacciyar kwakwalwa ta ni an bani kaza ni naci kaza.

To wannan tunani na ci bayane ba tunani ne na wanda yasan abin daya kamata ba''.

Sai malam ya kara da cewa ''Abin haushi da takaici hatta wadan su masu Magana da yawun Addini akwai masu irin wannan kuntataccen tunani ubangiji ta'ala ya yi mana gamdakatar''.

Allahu akbar wannan it ace Nasihar da malam ya yi ta karshe ga matasa kai dama dukkan wani mutum mai hankali. Bayan an kammala wannan muhadarar da niyyar washe gari juma'a malam zai yi khudba akan zabe. Ranar juma'a da asubahi malam yana cikin sallah, ya karanta suratul Ma'arij aka samu wasu mutane miyagu azzalumai makiya Allah makiya san cigaban Addini, suka yi masa harbi da bindiga ba sau daya ba, ba sau biyu ba, kisan gilla inda suka harbe shi a kirjinsa na gefen hagu.

Anan muna rokon Allah ta'ala ya sa malam ya yi mutuwar shahada kuma ya karbi shahadar sa, Allah ya kyautata bayansa, ya sanya Albarka a cikin iyalansa da zurriyarsa. wadanda suka aikata wannan aiki na ta'addanci a'ansa, su sani wannan tafarki da Mallam Jafar ya mutu akansa, kamar wata bishiya ce da bata tsiro bata tofo har sai mun shayar da ita da jinin jikinmu, wannan abu ko kadan bazai sanyamu mu yi rauni ba akan wannan tafarki. Allah ya daukaka Musulunci da Musulmai, ya Allah kada ka baiwa azzalumai dama domin su cutar da al'umma.

By Yasir Ramadan Gwale
Batun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen