RAYUWAR MUMINI A LOKACIN FITINTUN
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=663

 
Sheikh Isa Ali Pantami

RAYUWAR MUMINI A LOKACIN FITINTUN

RAYUWAR MUMINI A LOKACIN FITINTINU Malaman Sunnah (RH)

sun karantar da mu wasu muhimman darussa a lokacin fitintinu. Duba littafin "al-'Awaasim min al- Fitan." Wadannan abubuwa dole muyi ri'ko da su. Gasu kamar haka:

1) cikakkiyar biyayya zuwa ga Qur'ani da Sunnah bisa ga fahimtar Magabata (RH)
gabannin yin ko wace magana ko aiki ko rubutu ko hukunci.

2) Yin addua gadan- gadan da ikhlasi. Ya tabbata a Sunnah cewa ana addu'ah a lokacin fitintinu da cewa:

"Allahumma Innaa Na'uzu bi Ka minal Fitan maa Zahara min ha, wa maa badan." 3) Nisantar wajen fitintinu. Sunnah ta karantar da cewa "wanda ya Zauna a lokaci fitina yafi wanda ya tsaya, haka kuma wanda ya tsaya yafi wanda ya tafi zuwa gare ta. Don haka ana nisantar wajen fitina.
4) kaucewa Jita-jita a lokacin fitina wajibi ne.

Wajibi ne duk labarin da Musulmi ya ji, ya bincika ya tabbatar gabannin ya isar da shi gaba.

Haka Qur'ani ya mana wasiyya da aikatawa.

5) Tausasawa cikin hukunci da ayyuka bisa ga Manhajin Manzon Allah (SAW). Domin Annabi yace:

"Tausasawa idan ya shiga al'amari yana kyautata shi. Idan kuma aka cire shi a cikin lamari, lalle lamarin yana lalacewa. (sahih Muslim)
6) Kusantar Malaman Sunnah, Shugabanni na kwarai da dukkan Salihan bayi. Domin sune fitilu na al'ummah.

Annabi (SAW) yana cewa: "Lalle a cikin mutane akwai wanda suke masu bude alheri da kulle sharri."(Bukhari).

7) Yin Nasiha ga kowa da kowa kan komawa ga Allah da kuma kiyaye amanar da ke wuyan kowa. Saboda kowa mai kiwo ne, kuma Allah zai tambaye shi kan kiwo da ya dora masa.

Yaa Allah kabawa Nigeria da salihan Musulmai da Sunnar Annabi (SAW) mafita daga wadannan jarrabawa,.... Yaa Allah ka shiryar da Shugabanni zuwa ga abun da ka yadda da shi kuma ka ke 'kaunarsa,.... Isa Ali Pantami, PhD
Batun: Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi