IDAN MAYE YA MANTA TO UWAR 'DA BATA MANTA BA
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=667

 
IDAN MAYE YA MANTA TO UWAR 'DA BATA MANTA BA

Allahu Akbar! 'kai'kayi koma kan mashe'kiya kenan. Nan Mallam Sani Yakubu Zaria da ma'karrabanshi suka kai 'karar Ash-Sheikh Albaniy Zaria 'kara a masarautar zazzau kan raya sunnar sallar jumma'a kafin rana tayi zawali da 'dalibanshi suka yi.

A 'daya 'bangaren kuma dagangar Mallam Sani Yakubu da ma'karrabanshi suka shafa ma fuskarsu toka suka'ki kai 'karar Zakzaky wurin sarkin zazzau saboda 'kaninsu ne duk da irin zagin sahabban da yake yi.

A sakamakon haka, 'karara sarkin zazzau yace zai yi amfani da jami'an tsaro akan marigayi Albaniy Zaria kan matsala ta furu'a.
Allahu Akbar! Allah ya kare Ash-Sheikh Albaniy Zaria daga jami'an tsaron da sarki yace zai yi amfani dasu akanshi.

Tsarki ya tabbata ga Allah! Sai gashi yau bayan gushewar Ash- Sheikh Albaniy Zaria Allah ya saukar da ikonshi ta yadda da kanshi yayi amfani da jami'an tsaron akan 'dan lelen da aka 'ki kai shi 'kara a masarautar zazzau saboda yana da iyaye a gaban murhun masarautar zazzau.

Allahu Akbar! Sai gashi Allah da kanshi yayi amfani da jami'an tsaron akan 'dan lelen da masarauta bata ta'ba cewa za tayi amfani da jami'an tsaro akanshi ba duk irin zindiqancin da yake yi.

Allahu Akbar! Wa yamkuruna Wa yamkurullah, Wallahu Khairul makirin.

Allah (T) muke roko da yasa wannan lamarin ya zamanto sanadiiyar mutuwar shi'a a 'kasar zazzau. Allah (T) muke roko da yayi mana maganin duk wani mai yun'kurin hana mu 'dabbaka addininmu a bisa hasken manhajin SalafiyyahBatun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen