KUNDIN TARIHIN KWAMANDOJIN SALAFIYYAH KASHI NA 'DAYA (PART 1)
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=669

 
SHEIKH ISA ALI PANTAMI

DAGA BAKIN SHAYKH DR HUSAIN BN ABDUL'AZIZ ALUSH- SHAYKH (HAFIZAHULLAAH)

KUNDIN TARIHIN KWAMANDOJIN SALAFIYYAH KASHI NA 'DAYA (PART 1)

DAGA MIMBARIN SALAFIYYAH NETWORK NIGERIA KUNDIN TARIHIN KWAMANDOJIN SALAFIYYAH KASHI NA 'DAYA (PART 1)
Wannan Shine Ash- Sheikh Abu Abdullahi, Muhammad 'dan Saalih 'dan Muhammadu 'dann Uthaymeen at-Tamimi.

Al-Uthaymeen kamar yadda aka sani mutumin 'kasar Saudiyyah ne wanda ya fito daga cikin 'kabilar Banu Tamim.

An haife shi ne a ranar ashirin ga watan Ramadan hijiriyya ta dubu 'daya da 'dari uku da arba'in da bakwai (1347) a garin Unayzah.
Yayi karatun shi a hannun manya manyan malaman duniya irin su Ash-Sheikh 'Abd ar- Rahman ibn Naasir as- Saa'di, Muhammad Amin ash-Shanqeeti da kuma Ash-Sheikh AbdulAzeez Bin Baz.

Uthaymeen ya kwashe sama da shekaru talatin da biyar yana karantarwa a masallacin Harami dake garin Makka. Kafin rasuwarshi, Malami ne a tsangayar Shari'a dake jami'ar musulunci na Imam Muhammad ibn Saud. Har ila yau memba ne na majalisar malamai na duniya, sannan kuma Shine babban limamin Masallacin Unayza.

Kadan daga cikin ayyukan da yayi ma duniyar musulunci sun kasance kamar haka; .

Rubuta littafin Sifatu Salatin Nabiy, Sharh al- Aqeedat Al- Hamawiyyah, Sharh Usool al-Iman, Sharh Usool al-Thalaathah, Sharh Hadeeth Jibra'eel.

Allahu Akbar Kabiran!

Komai yayi farko zai yi 'karshi. Ash-Sheikh Uthaymeen ya rasu a ranar laraba sha-biyar ga watan Shawwal, hijira na da shekara dubu 'daya da 'dari hudu da ashirin da 'daya (1421 AH). Ya bar duniya yana da shekara saba'in da biyar, sannan anyi jana'izar shi a garin Makka Saudi Arabia.

Duniyar musuluncin Nigeria baza ta taba mantawa da Ash- Sheikh Uthaimin ba domin ya karantar da manya-manyan malaman Sunnan 'kasarnan irin su Ash- Sheikh Abdulwahhab Abdallah Kano da kuma Ash-Sheikh Muhammad Auwal Adam Albaniy zaria (Rahimahullah) a 'karkashin tsarin koyon karatun irin na zaure.

Allah (SWT) muke roko da ya jikan Ash-Sheikh Uthaimin. Allah (SWT)
muke roko da ya kai haske 'kabarinsa.
Batun: Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar